← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 306

Sashe 46

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan muka bar mama da ummah muka dawo gida saboda abincin da part din yaya suka kawo mama tace ba sai munyi wani abinci ba a ranan mu barshi kada ya zama barna. Hakan yasa koda ya Habu ya sauke mu gida barci sosai mukayi sai wajajen la,asar muka tashi mukai sallah Salima tace zan rakata kasuwa . Banyi mamakin hakan ba don nasan tana kudi ranan kudin da dan uwanta ya bamu da zai tafi ni banko tsaya duba kudin ba tunda na saka a kasan jakkata a lokacin. Kayan gyaran jiki ta kwaso su man shafi sabulai turare har ina mamakin hakan yadda ta iya fidda kudi ta biya kudin ba tare da jin komai a ranta ba. Saita tuna min da anty Salman Abuja a lokacin har nake mata hiran tana min shige da ita don haka halaiyanta yake itama. Bayan mun dawo gidane tace na kwashe wanda take amfani dasu da farko don ita bai mata ba a cikin murna na kwashe zuwa inda nake aje kayana na jera kamar yadda suka jera nasu gefe daya don kowa nada inda yake aje kayansa a dakin. Tun a hanya ta gargadeni da cewa kada in yarda in fadawa anty saare ko nawa aka ban in mace kawai dubu biyar ne ko goma. Nayi mamakin hakan data fada amma na share muka dawo gida a falo muka sameta zaune tare da iya muka zube kayan a nan falon. Duban kayan tayi tana fadin kasuwa kukaje Salima baki fada min ba aida na baku sako kun sayo min tana duban kayan take magana . Kudin ba zasu azu min ba hakana zan iya kashesu ban mora ba ko kuma in rasa me nayi dasu amsan data bata ke nan lokacin. Ga mamakina sai naji Saare din na fadin ke Ramaah nawa ya baki halan nace dubu gomane sai tayi shiru bata sake magana ba sai can take fadin baki sayo komai bane ke nace a,a ban saya ba anty Saare. Mikewa Salima tayi zuwa daki da ledan kayanta a hannu na dan kai kwance a inda ta tashi ina kallon tv dake aiki iya ke fadin ki lalubo muna Jafar muji koya sauka lafiya. Ta dauki wayanta tana neman layinsa din yashiga take gaidashi tare da fadin iya tace ka sauka lafiya ko yace Alhamdullahi ina kaduna sai yamma zamu shiga jirgin Rivers din . Muryan Salimace ke kirana daga daki na amsa na tafi ba tare dana san yadda sukayi ba kayane saman gado ta zuba dana shigo take fadin ki kwashi kayan nan Ramaah kiyi amfani dasu tun wanda yaya ya sayo muna ne da yaje tafiya da wasu na sallah ba amfani nake dasu ba don ban faye son dogon riga ba idan zan fitani. Godiya nayi mata na kwashe kayan zuwa wajena na aje ta mike zuwa gaban mirrow ta kwashe kayanta kaf ta miko min tana fadin zaki iya amfani da su zai maki kyau sosai ya gyara maki jikin ki don ni bai kara min wani haske ba. Na fararen mutanene na kwaso sai daga baya nagane hakan kinga idan ya karbeki kya dinga sayensa daga baya kina amfani dashi. Kwasa nayi na kai wajena tunda yanzu a nan dole zan rika amfani tunda yaya Habu yana nan sai gashima washegari shima ya koma wajen aikinsa . Duk daya tafi ban koma ba a nan muke kwana saida mama tayi wajen kwana uku asibiti tare dasu ummah ta fahintar da ita komai game da antyna ta dawo gida ta dan huta. A ranan ne kuma muka wayi gari da an shiga part din nasu saidai bamu san me aka dauka ba tunda masu wajen basa nan. Wanan dalilin yasa ya J daukan maigadi a gidan dama yana da niyar hakan ga iyalinsa din ya kasance a yanzu muna da maigadi sai kuma mama tace nida salima mu koma kwana a can har ya Habu ya dawo wanan dalilin yasa muka koma kwana din a part dinsu mu biyu. Acikin yan kwanaki na kara fahintar waye salima don gaskiya muna zaman mu na lafiya sosai tsakanina da ita duk da ba wani girma na sosai tayi min ba amma haka bai hana in bata girmanta ba. Itama din na fahinci tana daukana tankar yar yar,uwartace ta jini don yadda take zama ta fada min komai nata ta dai sake jikinta sosai dani tunda tasan ba wanda zan fadawa . Wani saurayi take so sunansa yazid amma iyayyenta da yayyu sunce yayi yaro kwarai a gareta ita kuma ta nace akan shi take so . Duk da yazid din zai girme mata da shekara biyar ko fiya da hakan amma sun nuna basu son alakanta dashi gashi kuma sun shaku sosai dashi din. Da muka dawo da kwana part din antyna sai hakan yai mata dadi sosai sai sukai wani lokaci dashi a waya nikan ina kwance ina sharan barci na. Idan ko idonshi biyune zata ban waya mu gaisa dashi ya dan jani da fira har in gaji in mika mata waya don bai gajiya da rokona in kafa masa gwaunatinsa gasu yaya. Shi baisan banda power hakan ba garesu nima cin arzikin yar uwatane ya hadani dasu idan bashi ba ina rugga tare da dabbobin mu da baffa ya kwace muna. Rai da kwade irin na dan adam a zaman mu wajen Baffa saida muka gano shanayen maihaifin mu kuma muke basu kulawa sosai a lokacin. Don sai ince yawancin shanayen da baffa ke alfahari dasu na mahaifinmune don sunfi yawa sune masu dabbara dabaran baki da fari a jikinsi kinsan shanun mu na can suna da babbanci da shanayen ku na nan mu namu gudale sinfi yawa sunci sun koshi sosai suna bunkasa don hakkin da suke samu. Yayin da yar,uwata take har lokacin karkashin kulawan likita kuma tayi kyau sosai su mama dabu da mahaifiyan mu suna kwantat mata da hankalinta. Hakan yasa jikinta yayi kyau ta murje ba kamar yadda aka kaita asibitin ba ga kuma rubutun da a kullum sai an wanko mata tasha. Yauma shiri muke don mama tayo waya da muje gidan malamin bayan kwatancen da tayowa salima tace tagane gidan zamu karbo mu sameta dashi asibiti. Zafin ranane a lokacin amma haka muka daure muka fita bayan la,asar dakyat kuma muka sami abin hawa da zai kaimu unguwar mu karba mukai asibitin. Gidane mai fadin baranda daga waje sai ciki inda tulin kayan da muka gani ya nuna na almajiran gidan ne muka karasa ciki kuma zaure biyu ne a gidan nan muka sami malamin muka karba ya tambaye mu mai jiki ? Salima tace da sauki idon da bawan Allah ya kura min yasa na shiga tsarguwa da irin kallon da yake min har dai muka samu ya mika muna mukai mai sallama. Karfe biyar a asibiti yayi muna mun samu su mama a waje suna shan iska muka gaidasu tare da mika mata sakon tana ta saka muna albarka. Nan take fada muna cewa almajirin dake kawo masu kullum yau baida lafiya ita kuma ba dadin jiki ta tashi dashi ba don saida tasha magani. Tausayi ta ban don akan ciwon yar uwata ta hade nata ta zauna a asibitin duk akan neman saukiwa danta take wanan abin mun dan jima a wajensu din. Nan mahaifiyar mu take min yare da inzo in mata kitso kanta yayi mata nauyi da yawa na bata shawara akan tazo gida zaifi . Don ta samu ta wanke kan saboda kitson ya jima akanta idan anyi sabo duk a cikin harshen fulatanci muke magana da ita don haka basa jin mu. Inda ummah ke fadin ya zatayi tazo gidan da sunan kitso gara dai inzo nan in lalaba mata kan nata duk da maman mu yar daji ce amma gaskiya tana da tsabta sosai kafata da kanta basu rabuwa da gyara kullum. Mamace ta mike take fadin bari ta duba ko ta falka ta bata maganin ta shiga nan nake fadawa Salima takaddaman da mukeyi da ummah din wai kada a zageta yarta na asibiti kwance ace tana batun kitso ita. Lah ummah kizo gida ki wanke idan ba zaki zo ba kuma sai a kaiki sallon a wanke maki a can tunda shi kitso dole sai anyishi. Murmushi tayi tana fadin boni jam saloon kuma yar nan meya kaini zuwa saloon a wanan shekarun nawa kuma yanzu ai garama inje gidan baku aimin a can din. Itama salima din tayi dariya tana fadin kukan filani Allah yayiku da kunya ummah meye a cikon kunyan haka kuma tunda ba tsufa kikayi ba ai nifa har yanzu zuciyata ta kasa yarda cewa kece kika haifi su Ramaah wallahi. Don kinfi kama da ace kece yayarsu dai ba mahaifiya ba ummah don sam baki tsufan haihuwansu ba haka tayi murmushi tana dukar da kai. Wai meyasa mutane da dama suke fadan hakane garemu bakece kika fara fada ba kowa haka yake fadi a kanmu idan ya ganmu da ummah din. Mama ta fito da kayan abincin da anty Yanda taci hakan yasa na tashi da sauri na karbo a hannunta tana fadin tagode kayan da zamu dawo gida dasu ta fara tattara muna waje daya harda wa yanda zan wanke masu. Karfe shidda a gida yai muna ban kuma zauna ba saida na wankewa ummah mu kayan nata dana anty yanda da ake kawowa gida in wanke ko yaushe. Abinda ke ban mamaki yadda na kula da matan gidan basu damu da zama yar uwata asibiti ba irin yadda na sani idan dan uwanka yana kwance ka dan rika lekasa din sam basa sunayin hakan gareta ba su ? Hakan yasa na kara nisantar lamarinsu iyakata dasu gaisuwame tun bayan da naje neman magani in hade saboda ciwon kan daya kamani ta dalilinsu suka hana min magani saida mijinsu ya sawo min har yanzu kuma ina amfani da sauransu wajena. Iya taje asibitin ta zauna da matan kawu dauda a ranan don su karbawa su mama zaman su dan dawo gida su dan sarara hakan yasa na samu daman banyewa ummah kai nayi mata kitso irin wanda na saba yi mata a gida. Sai wanan ranan yan gidan suka san dana iya kitso sosai har salima na fadin zan mata
Chapter 46 · 0% Book details