← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 306

Sashe 134

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

dana taso yaron yana jin hakan ya mike tsaye ya fito daga dakin daidai lokacin mahaifinsu ya shigo gidan shima cikin murna da ganinta yana fadin wai baya batada kada ? Yanzun nan na fita fa ashe har kun iso mun iso malam mun mun sameku lafiya yaya gida da al,amura kuma ? Yana washe baki ya samu waje ya zauna a gefenta yana fadin kunsha zaria dai kam daga tafiyan kwana ukku gaku sai yau din nan muka ganku ? Tafiyane ya kama haka mun tsaya saida akai komai a gaban mu na samu na taso Aliyu dake tsaye dan nisa kadan da bayan mahaifinsu yana mata alama da ido sau daya ta kalloshi ta dukar da kai ta cigaba da magana da mahaifin nasu. Ganin bata kula dashi ba yasa ya fice daga gidan kofan gida ya koma ya zauna yana dakon fitowan mahaifin nasa . Saidai mahaifin nasa yakubu kamar yasan da hakan a lokacin yaki fitowa daga gidan suna can matarsa baraka na mashi hiran yadda zama nasu ya kaya a lokacin. Ya gyada kai yana fadin mena fada maki a baya malamin da naje wajen kafin ki wuce aiya fada muna zai bayar da kudin ba tare da yayi gardama ba. Yanzu dai aikin gane gaskiyan da nake fada maki cewa kune mata aka tauye su suna amfana da kudin ku sun gina kansu sun bunkasa sun barku a cikin wahala. Idan ba yasan ya samu ba wanan kudin za ace an tarawa wanan uban riban haka mai yawa ya dade yana moriyan abinsa shi kadai ba tare da kowan ku ba. Hakane ai kafin naje na samu saratu ta zuga mama sosai har mama ta yarda da zancenta cewa da dukiyan mu yake wanan abubuwan tunda ba binkcike akeyi kansu ba. Shima kawu daya zo haka yace da mama din shiya bada karfin gwiwan da har aka samu aka zauna komai kudin kowa ya fito a cikin mu. Yanzu kuma ai sai ya samu wanda zaiyi facaka dashi da yake dauka yafi kowa yaron nan baida kirki ina fada maki baki yarda yanzu ai gashi kin gani dama kyautan rufe baki yake maku don kada a tambayeshi kudin nan. Jafaru fa kafansa ya dafa kasa malam har kyautan gidaje naji yayiwa Habu da Yazid a wajen kufa ya tambaya da sauri tace mu ai matane ba zai bamu gida haka bakatan ba. A,a lalai dole ya kawo maku kudi haka masu yawa ya toshewa kowa baki amma ki rubuta ki aje zai dawo daga baya yana maku dadin baki ku hada kai a bashi yacigaba da juyawa . Cabdi yana da wuya hakan don yadda akayi din nan banjin zai karbi kudi a hannun wani kuma nasa kason ma jiya muke ji da dare wai yace a buge massalacim kofan gidan mu din nan a tayar da wani Allah ya kai ladan hakan ga baba. Kaji dan duniya ya fada yana mikewa yau kuma ina mota saratu ta kirani take fada min cewa wai yayiwa matansa akwatuna da mama dasu har iya na tausan gaba din nan da maza keyi. To shi sana,an me yake hakane wai indai ba smogal ko safara yajefa kansa a ciki ba yake wandaka da kudi haka ya kamata a buncikeshi dai gaskiya. Ance sana,an mai sukeyi yanzu kuma naji yana fadawa iya cewa yana kai kayan ma,adaine kasan waje akwai samu sosai ga hakan . Ni yamace yana son ganina kafin na wuce ban tsaya jiranshi ba na taho abina to me zai min yanzu tunda hakkina ya fito a hannusa ba abinda ya rage kuma ai ? Mena fada maki dama kudin nan yake son ya biyoki ya karbe yace ki bashi tunda yaga kamar kece mai taushi a cikin ku. Kofa ya nufa yana fadin ni zan fita me za a zo maki dashi a daidai lokacin wayanta ke haske bata dauka ba take bashi amsa da ba komai saidai dan abu mai maiko haka dai ? Tana duba wayan take fadin ikon Allah jafar dinne fa ke kirana yace aina fada maki zai saka rai ga taki dukiyan ta dauka da sallama tana fadin bari muji me zaice ai. Jafar ta ambaci sunanshi yake fadi a bangarenshi Anty baraka kin tafine ban sani ba ashe saida nazo ake fada min ai kin wuce naso muyi wata magana dake wallahi. Cabdi nikan gani Gusau ai jafaru da yake tunda safe na taso kasan malam bai son inyi tafiyan dare yace hakane to an isa lafiya yaya su malam iliya din suke ? Ta amsa da lafiya yanzu yaya akayi jafaru yace leter on zamuyi magana ai dama zancen Aliyu naso muyi jin hakan mijin nata yayi murmushi yasa kai ya fice Aliyu dake kofa ya fado dakin yana fadin uncle Jafar ne mama abani shi don Allah ? Ya mika hannu ya karbi wayan yana fadin Uncle ina wuni fita yayi da wayan a hannunsa sukai magana ya gamsu da maganan kawun nasa a lokaci. Ya dawo da wayan ya mikawa maman nasa yana fadin yace zakuyi magana dashi ya samu waje ya zauna a gefenta yana fadin. Mama ina ta maki kwantance da kada ki yarda da duk wani dadin bakin da baba zai maki kada ki yarda da baba don Allah . Yana fadin hakan tace babangida banson rainin wayau banson rashin kunya kaine zaka fada min zancen mahaifinka dana zauna dashi. Dana zauna dashi da farko har na haifeku kaine kake zuwa ka koya min dabarun zama dashi din ? Babangida ka fita min a ido tun ban saba maka rai a wajen nan ba wallahi ina ruwanka da sha,anina da mahaifinka ? Kallon mamaki ya bita dashi kafin ya mike baki a laikum ya fice daga dakin har ya nufi wajen fridge dinsu sai kuma ya fasa ya fice daga gidan baki daya Alkawari ya daukarwa kanshi ba zai karawa uwar tasa maganan komai ba dangene da abinda ya hango yana tunkarota kan mahaifin nasu. Yasan tabbas mahaifinsu dabara irin ta miji da mata yake sonyiwa mahaifiyarsu gashi kuma maman nasu ta kasa saurareb shi . Idan ya mata hankaline zai tashi a banza don ba fahinta zatayi ba lokacin saboda dadin bakon mahaifin nasu daya inma bakinshi wajen tsara mutum don haka yin shiru da bakinsa yana kallon irin bidirin da suke zubawa a gidan Tun dawowan mahaifiyan nasu aka tsiro cin dadi a gidan nasu inda baraka sai barin kudi takeyi shiko malam yana manne da ita yana mata dadin baki. Alkawari iri iri da labarai sai fitowa sukeyi a bakin mahaifinsu donshi yanzu Aliyu ya zama kamar makiyinsune a gidan don tun ranan da mahaifinsu yai mashi tas yana fadin ya facin Aliyu din yana bakin ciki da lamarinsa a gidan don haka zai dauki mataki mai karfi akansa yaja bakinsa yai shiru tare da saka masu ido ga duk abinda sukeyi. Babu zancen za a bashi kudin jari ko wanda akai mai alkawarin in an samu za a sai mashi offer wajen aiki da mata garin ma,aikantan gwaunati ke sayarwa. Hakan yasa ya nemi laban kawunsa Jafar ya kirashi yace yazo Zaria ya samu habu sun riga da sunyi magana a kanshi don haka daya taso daga gidan bai fadawa kowa ba sai kanwarsu da yace da ita zai tafi ya nemo kudi ya bar garin. Zarian ya nufo amma kuma ya samu ance Habu don yayi tafiya dole ya juya ya dawo gida ba tare da bukata ya biya ba. Inda Habu yana sane yaki bari ya gana da yaron a lokacin cewan Habu idan anyiwa yaron ai kamar ita Baraka akaiwa don haka taje taci barnan ta a yanzu tunda tace su diya mazan dakin su basu da taimako ko amfani a garesu. Don har matayesu sun fisu dara don akan matansu suke mutuwa ya dawo ya samu mahaifiyar nasu baraka ta dauki kudin daya rage taba mijin nata don ya juya matasu .
Chapter 134 · 0% Book details