← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 306

Sashe 70

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

lafiya lau ba tare da aiki ba ranan munyi murna sosai da haihuwan . Ya habu bakinsa yaki rufuwa duk daurin fuskan nan nasa a ranan babu wanan halin a wajensa sai washe baki yake kallo daya zakiyi mai ki gane yana cikin farin ciki. Matan yaya Jafar kusan sune sukazo a karshe daga gidan duban maijego da jariri sun samemu a dakin zaune tare da ita muna hira su mama suna waje da ummah mu zaune don an dauke wuta. Sun shigo sunyi barka basu zauna ba duk da dagawan da mukayi muka basu wajen zama sukace sauri suke zasu koma gida iyace da mai aiki suka bari a gidan. Bayan fitansu mama ta aiko Nafisa tazo sai gata ta dawo tana fadin zata bisu su sauketa gida ta karbo sako a wajen innansu. Don haka suka tafi tare dasu a hanya suka fara zagin yar uwata harni basu barni ba da uwarmu duk sun hada sun zagemu tas a lokacin kishin (saure) ke nan wasu suce dashi (Facal) matar wa da kani ko dan uba. Yafi zafin kishi wani lokacin ga mata har gara kishiyar da kuke mijin ku daya da matar dan uwan miji koda ko ba a gida daya kuke rayuwa da juna ba ana samun wanan matsalan sosai a ko wani kabila a duniyan nan. Mukan bamu san sunayi ba abinda dai na sani shine basu kaunan mu wanan yasa gaba daya bani shiga tsabgansu yanzu ko part dinsu tunda mijinsu ya samu lafiya rabona da wajensu ke nan sai inyi kwana gamu gida daya amma bamu hadu ba. Ina dakin nasan dai ya dawo garin tunda naga motar dayake amfani dashi haka kuma anshigo da tsaraba akace shine ya dawo. Sai asibiti muka hadu daya shigo ganin jaririnsu jikinshi a lokacin ya dan dawo sosai zakice bashine yayi wanan ciwon bala,in ba a watannin da suka shige. Gashi a yanzu yadda nake ji a wajensu arzikinsa sai habbaka yakeyi don har su mama da iya na kiran dan yar uwata da arzuka wai yaya J yace ana sanar mashi da zancen haihuwan kuma aka kirasa kudadenshi sun fito masu yawa daya saka hannun jari a wani harkan mai a can kudu. Don haka komai baja baja akeyinsa a gidan alherinsa ga mutane kuma bai daina ba kamar ma kada yai ciwom nan abin ya nunku masa. Ya shigo da mutane a bayansa yuuuu da suka taka masa naji Nafisa tana gaidasu nidai sau daya na gaidasu na mike tsaye na koma can wajen gado na tsaya. A cikin yare anty Yanda take min magana da na dauku dan nabasu don haka nake fadin nikan ina nasan haka akeyi. Yar fillo anyi da sintirin zuwa asibiti ya kare sai karatu yanzu ko abinda yaya j ya fada min ke nan a lokacin na danyi murmushi ina mika mashi dan cikin ladabi. Amsan shi yayi yana kallo ya jima dashi a hannu sai daga baya na fahinci addua yakewa yaron ashe naga yana mashi ikima da bin sassan jikinsa yana tofewa har dai ga al,auran yaron ya mikawa na kusa dashi yana fadin Allah ya raya muna Alh mu bisa kan sunna sunan baba na saka mashi dama alwashina ke nan idan na samu da in saka mai sunan baba sai ga habu ya rigani hakan. Ai duk nakane wani mai banbadanci ya fada basu jima ba suka mike don tafiya akwaisu da son kanninsu don haka ya yafito Nafisa da hannu ta biyoshi kome ya tuna naji yana fadin yar fillo zo muje mana. Dole na biyo bayanshi sam ba zan iya yadda suke da yan uwansa ba sosai suke sakewa dashi fiye da Habu donshi Habu ko yaushe fuskansa babu fara a cikinsa. Shiko yana da dama sosai yakan zauna dasu yayi hira su fada mashi korafinsu kuma yayi masu maganin hakan a take matane kawai za ace bai dace dasu ba. Amma yana iya kokarinsa ba zaki gansu da tufafi da bai dace ba saidai yanayin gyaran ne da basu tsayawa suyi kawai gara Saiba yar kadunace iya kwaliya a wajensu yake sai dai ita kamar bata amsa sunan yar kadunan ba. Mun fito yake fadin to yaya Nafisat party zamuyi ko walima ta kwashe da dariya tana fadin party kuma yaya kamar wata yarinya karama au to ke in bakiyi yar fillo zatayi ai ? Ko sai ki hada muna taron fulanin ku ayi sharo ayi rawan sanda nayi murmushi ina fadin yaya ai sai za aje neman aure ake sharo ba a haihuwa ba. Au ashe akwai kallo kuwa ranan da zaki kawo muna miji don sai munyi masa shadin nan dubu kafin mu bashi mata. Abokansa suka kwashe da dariya wani ke fadin ka ganta kuwa sai jarumi zai iya zuwa don wanan za a kashe nagge a kanta kana ganinta nan. Au Allah dai kace mu shirya kwasan nagge ke nan nidai sai murmushi kawai nakeyi don ban iya cewa komai idan yana min irin ba an nan. Yanzu ke Nafisa sai mun hadu a gida ke nan ko yar fillo dai wasan Nagge zatayi muna da kiwo ke kuma kince bakyayin party sai walima ? Tana dariya take fadin sai mun dawo yaya Allah yasa kana gari ba tafiyan zakayi ba mukai masu sallama har bakin mota bayan ya gama da su mama suka tafi. Da muka dawo dakin Nafisa ke muna hiransu irin rayuwanshi da yadda suka taso har wani labarin danake tsakwaro maki nasu da akayi bani wajensu. A gurin ta na kan danji tarihin rayuwan mama dubu da iyalinta don takan fada min komai salima ma takan fada sai da komai har haka ba. Hidama sosai yayiwa sha,anin sunan zakice matarshice tayi haihuwan farko haka kudi ya raba muna har anty Salima dake kara a birnin minna don ita bata samu zuwa ba ya tura mata da kudinta Saare kuma da ita akayi sha ,anin bukin. Babban yarsu tazo daga zamfara don da yayi ciwo a lokacin kuma mijinta yayi accident ya kare a hannu sai wanan zuwan muka santa dai zance amma muna gaisawa a waya da ita. Ummah mu ana gama hidimar suna ta nuna tana son komawa gida a lokacin saidai mama ta hana hakan sai anyi arba,in tace yan uwan mu sunzo mutum biyu da namiji guda . Sunzo da nasu abin arzikin daidai iyawarsu an kuma yaba mukan bamu da abinda zamucewa hardo daya rungumemu hannu biybiyu a yanzu . Sai a bakin iya nake ji wai ai ummah mu ta samu manemi a kaduna zatayi aure wani abu naji ya daki zuciyana nace iya ummah tamuce zatayi aure kuma ? Muna ga rasulu yar nan me zai hanata aure wanan da bata wuci haihuwa ba kar kiyi jahilci mana damuwan ku zai iya hanata samun lada . Da zaran kun nuna baku yarda ba zaku sare mata gwiwa da hakan taji auren ya fita ranta take fadin wanan matar da suke asibiti tare itace ta yaba da hankalin uwarku ta nemawa dan uwanta aurenta. Wai matarshi ta rasu shekara ukku ke nan yanzu ya kasa samun matar da zai aura ko wace aka kawo mai yace batayi ba amma yana ganin umnan ku ya yarda. Kinga ai hakan alherine ko har yazo suna asibiti ya ganeta a nan kaduna yake da zama dan jahanan ne shi kinga ai ta dawo kusa daku ke nan idan Allah yayi abin. Jinta kawai nakeyi ina tuna mahaifin mu daya rasu ta yaya ummah zatayi auren wani kuma yanzu ?
Chapter 70 · 0% Book details