← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 306

Sashe 28

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

wanan yau alheri da kyautatawa abokin zama kuma laifine Nusaiba ? Shi dan arziki a duk inda yake yakan nuna halinsane da irin tarbiyan da akai masa ai alheri kuma a cikin jinin bawa yake. Nayi mamakin yadda yaran nan har zasi iya saka muna abinci bama mu kadai ba harku a gidan amma ku din nan kuna bakin ciki ace yau abinku ya shigo a hannun ko tsohuwar nan balle ni ? Har yaushe yarinyar nan tashigo gidan nan da wani zance can zai biyu baya binsu mukayi da kallo mijin da dayan matanne suka shigo part din zama sukayi nan mijin nasu shima ya dora da fadin yazo dasu gaban tsofin ne ya kafa hujja akan abinda yake son fada game da matan nasa. Ga kaninsa nan ya soma fadin tare da iyalinsa ina son kuji ku sani kada ku dauka ban san plan din ku bane saboda kun daukeni bansan me nakeyi ba. To ina son ku sani duk ranan da wata daga cikinku naji kona gani tayi fada ko tsangwama akan yarinyar nan da aka kawo gidan nan zan ba mace mamaki sosai ga matakin da zan dauka. Babu macen da zata hadani fada da dan uwana ko wani nawa a gidan nan mama ki duba matan nan basuji kunya ba don Allah idan zanyi magana mama kice na barsu zasu canza. Yau ace matar Habu ce datazo jiya jiyan don nan tasan tayi girki ta sako maku abinci har nima a saka min don girmamawa da halarci wai kuma don suna dolaye sun kasa fahintar ma,anan hakan da yarinyar nan tayi. Aiko ita bayin kanta bane mijinta ko wani ya bata dabaran ta dinga hakan Saiba ta fada daga gefen mama wajen da take zaune din. Ban fada maki idan kina zancen ki kibar sakani a ciki ba habu ya fada a harzuke yana mikewa tsaye zai dosheta don abinda ta fada. Kai Habu koma ka zauna kada ka tako wajen nan mama ta fada mama ki bari in koya mata wayau don Allah wanan yarinyar bata da kunya wallahi. Kinfa ji abinda ta fada waini na koyawa Maria wanan hikimar idan kuma bani bane wani ya saka tayi hakan tana nufin ke kenan ko iya ? Ballema nice ta tambaya jiya da zata zuba ta kirani tace mutum nawane manyan yaya Habu a gidan nan na fada mata amma wallahi ba wanda yasa tayi hakan a gidan nan . Na fada mata basai ta saka ba tunda muna girki a nan muma tace a,a idan tayi hakan rashin kunyane tayi girki iya bakinsu bata ba manyan shi ba da wani ido zata kallesu . Don ya habu yana mijinta ai bashi kadai zata bawa abinci ba su a wajensu hakan rashin tarbiyane kuma bayan hakan ina zata da alhakin kamshin da mutane sukaji a kanta. Sare ce dake rike da labule tana kallon draman da yaninta keyi da matan nasu take fadan hakan amma wallahi ba wanda ya saka anty maria zuba abincin nan. Ita tasan darajan mutane tarbiyan data taso a gidansu cikine ta fara nuna muna nan koyin da gidansu sukai matane take wanzarwa yanzu a nan. Ai dama ko wani tsuntsu kukan gidansu yakeyi a duk inda yaje haka kuma Allah ke nan ya nuna maku bakin cikin da kuke shukawa sarakuwarku gata zaune. Yau ubangijo ya kawo mata yar da zata share mata hawayenta kuna kallo ban taba gani ko ji inba gareku ba yau ace matar data haifi mijinka baka san darajanta a idanunka ba. Uwar mijinka tazo ko ruwa baka iya daukowa ka bata balle abincin alhalin kuma dantane ya ya sayi wanan abincin kika zauna kikaci har kina bawa yan uwanki amma ba zaki iya ba yan uwan mijin ki ba ? A,a iya mu munga cewa abincin nan duk abinda ya kawo sai an kawoshi nan wajen ki shiyasa aka daina zuba maku komai idan mun dafa. Fau ya dauketa mari yana harzuka yace idan duk na kawowa iya ina ruwanku sai in zauna ku kashe muna tsohuwa da yunwa kome ? Jafarne ya dauke Asmau dake kusa dashi zaune mari ya mike yana fadin wallahi iya ban taba sanin cewa basu dafa abinci da kuba a gidan nan sai yau din nan amma babu komai ke kuma zaki dawo ki sameni ai bari ganin kin boye a bayan mama ya fada a hasale ya juya zai fice daga falon. Kada ka daki yarinyar nan bai tsaya sauraro ba ya fice fada sosai iya da mama sukai masu Abubakar ya mike yana fadin indai abincin part din kune na soke dama bansan ta saka maku ba da ban bari takai maku ba don ku ba mutanen arziki bane kowa kuma ya sani. Matan dake bakin ciki da yan uwan mijinsu kada wani yazo gidan nan ya ci wani abu daga jikin J basu kaunar ganin J yaiwa wani alheri a rayuwansa . Ina son ku sani ba J kadai yake da ikon gidan nan ba gaba dayan mune muke da iko a cikin gidan nan har Ahmed da yake yaro yana da hakki a cikin gidan don naji abinda kuka fada ranan game da zaman mu a cikin gidan nan. Mama gata nan itace mukewa biyayya dagamu har mijinku din don ra,ayin mamane tagan mu a waje daya haka zaune. Ra,ayin uwarkune hadin kanku dana matan ku amma wa yan nan shedanun da Jafaru ya tara da alaman zasu durkusar da wanan mafalkin na Dubu nason taga kun samu hadin kai tsintsiya daya madaurinta ku daya. Iya ta fadi hakan ga shi Habu da ya saura a falon yace basu isa ba iya kuma sunyi kadan mu zuba da mace a gidan nan a yanzu zasu gane waye Habu ? Duk abinda akayi ina zaune a gaban idona akayi shi har fitan matan yayan nasa da sukaji fitan mijinsu suka koma part dinsu bayan sun gama koke kokensu don ranan mama ta nuna masu bacin ranta sosai a gabansu. Tunawa nayi da yar uwata da naji ana fadan wai bata da lafiya hakan yasa na mike na nufi part dinta da sauri na sameta zaune a falo saidai yanayin ta kawai zai sanarwa mutum bata da lafiya. Sam ban fada mata tashin hankalin da akayi ba balle in kara mata damuwan da na ganta a cikinsa abinci na dora muna bayan tayi min bayanin abinda zan dafa saidai har lokacin zuciyata tana min sake,sake. Na wani irin rayuwa akeyi a gidan nan haka kuma yaya yar uwar tawa zata kasance cikin matan nan dana hango rashin da,a a tare dasu dolene nima in zage a yanzu in kare yar uwata tako wani hanya . Can wajensu kuma sai waya kowa keyi nan aka fara fadin mena fada maki saiba tunda kikace bafulatana kanin mijinku ya dauko ? Fulani da kika gansu mutane da akewa kallon basu san komai ba amma sunfi mutum sanin duniya kar suke kallon mutum sun iya sace zuciyar duk wanda suke so su kuma nunawa wanda basu kauna boni a cikin ruwan sanyi kin fara gani ke nan wanan ma ai kadan kuka gani indai bafalatanin mutum ne. Wallahi mama saina nuna mata ba kowa take ba a gidan nan ba zan yarda da sherin daduk zatazo muna dashi ba yar daji da ita kawai. A dakin Asmau kuma yar ta ke fadi a cikin waya bance kada ki yarda da hadin kan Nusaiba ba Asmau nusaiba munafukace yar iskace ta karshe irin na bugawa a jarida din nan amma kinki ki gane me nake nufi ? Ki zauna tayi amfani dake ta cika burinta a kanki ta fitar dake gidan kila lokacin zaki gane me nake nufi da kalmana inba kina shasha ba. Ta yaya zaki zauna yarinyar data hanaki farin ciki a rayuwanki kin sani wai ki dinga bin kaidin ta kuna musgunawa uwar mijinku da kakanshi ?
Chapter 28 · 0% Book details