← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 306

Sashe 30

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanan case don da akayi shine mafarin komai a gidan har zuwa wani lokaci muna rayuwa dasune kawai da sunan muna gida daya. Amma hassada da kyashin duniya sun dauka sun dorawa anty Yanda dani kanwarta a gidan bamu da da matsala da surukan anty Yanda ko kadan . Don mutanene su masu mutunci daba zan iya fadan irin halarcinsu ba a garemu don sun rikemu kamar mu din jininsune . Haka muma bamu yarda wani rashin hankali ko sabani muyi kuskure a garesu idan mama ta koma can tudun wada nice zanta hidima da Iya . Wanda ban daukeshi wani hidima a wajena kafin na wuce makaranta zan tashi kiran sallah farko in gyara part din tsohowar ko ince part din mu in dora ruwan zafi na wanka dana flask idan akwai dumame in gyara muna don tafi son dumame ita. Sai infito in share haraban gidan nan kaf ba zakiga wani datti ba a wajen gidan ko kadan saidai kafin in dawo zaki matan part din yaya J sun jefo abubuwa sun bata wajen hakan bai damuna. Don wanan kadanne daga aikin da muka baro a gidan baffa ba yabon kai ba nafi anty na kuzari nakan gama nawa na hada da nata sai mun gyara garken shanu munyi ma matansa tatsin nono da surfe da acan muka koya wata rana harda fura mu wuce kiwo. Sai yamma lis zamu dawo gida mu sakawa shanaye hayaki muna kula dasu wanan yasa ban dauki aikin gidan nan wani aiki ba a wajena. Idan na gama inyi shirin school in wuce kuma ban makara tunda karfe hudu nake tashi zuwa makarantar idan na dawo nayiwa iya dan miya ko abincin da take so taci a ranan kullum cikin saka min albarka take. Duk da haka kuma zan shiga wajen anty na na gyara part dinta don shigan cikin data samu mai bata wahala hakan yasa yanzu da mijinta shima dan uwansa ya kadashi cikin business dinsa bai zama sosai a gari idan bai gari abincin da nayi wajen iya mekeci tare da ita. Duk ciwon da anty maria takeyi bai sa matan yaya J tausaya mata ba ba ruwansu da ita wai bata da lafiya balle su tausaya mata. Haka itama lamarinsu bai dameta ba idan bani gida ina school zata shigo wajen iya su zauna tare har lokacin dana dawo. Wani lokaci a nan zamu zauna sai dare zata koma wajenta wanan ya jawo tsegumi saidai ba suyi a gabanta don ba ruwanta dasu ko abinda sukeyi bata kallon hakan don ita bata da yawan magana kamata. Don ni a cikin dan lokaci nasan mutanensu sosai har iya kan aikeni irin gidan Kawu dauda ko can tundun wanda wajen mama . Ko acan wajen mama da mukanje mata wuni wani lokacin nayi sabo sai da mutanen gidan don akwai yan mata sa,anina da wa yanda suka girmemin a gidan. Hakan ya jawo sabo sosai a tsakanin mu cikin dan kankanen lokaci wata rana na dawo daga school da rana ina zaune muna hira da iya da antyna. Anty Asmau ta shigo part din kallo guda zakai mata kasan bata da lafiya gaida ita mukayi na cigaba da kankare kumbana da nakeyi . Naji tana fadin iya don Allah nazo aron budurwan nan nakine taje ta taimaka min tun shekaran jiya banda lafiya . Girki nakeso dan Allah ta taimaka min har yanzu saiba taki dora girki kuma tasan banda lafiya amma bata do,,,,,,,, Jeki ki girka mata din saidai ki sani ba zan yarda da hakan kullum ba haba iya iya yau din nan ne ko zuwa gobe dai haka har Allah ya ban lafiya. Koma dai meye banson abinda zai jawo kace nace akan hakan son Allah iya ta fada tana kara kallona tace min jekiki ki taimaka mata din kinji yar albarka. Kallon yayata nayi tayi min alama da intafi mana tunda iya tace inje din tare muka shiga part din nasu ga dai gida kan amma babu mata a cikinsa saboda kazanta. Wani plate don yakai kwana bakwai a wajen wani cup har yayi huhuna da abinda akaci cikinsa aka barshi nan kaya saman lafiyayyen kujeran dake falon kayan yayansu da nasu abin ba tsarin fada wallahi. A kitchen din naga tashin hankali don tukwane abincin ne a girke da ruwa da ruwa duk sun yi babu kyau gani a wajen hakan na tsaya saidana wanke tukunyan da zanyi amfani dashi lokacin na dora girkin . Ban iya sakewa kitchen da kazanta haka dole na shiga wanke kayan dake tare a kitchen din ina mamakin yadda mace zata samu daula haka kazanta ya hanata gyaranshi. Lafiyayyen shimkafa da miyar kaza na hada masu fridgen din nan nasu dankare yake da nama haka store dinsu kayan abinci a dankare kamar sun lalace a wajen gyara sosai na tsaya nayi masu tsakani da Allah ga yarta dake ta kuka na dauketa na goya ta a bayana yarinyar tayi barci haka kuma nake wanan uban aikin da ita a goye a bayana. Banji kyashi ko kiuya yi masu aiki tsakani da Allah ba inayi ina gyaran falon ina duba girkin daya gauraye gidan ba wani abu bane girki kamar mace ta tsaya ta soya kayan miya yadda ya dace . Haka tayi amfani da sanadarin girki na zamani ko na gargajiya da muka sani wanda nagani a kitchen din shi nayi masu amfani dashi a lokacin. Na bude miyar naga ko ya isa daukewa saiga dayan matar ta shigo kitchen din ksllon mamaki take min kafin ta karaso gabana tana fadin . Banyi mamakin ganinki a nan ba tunda har ga yar gida a bayanki yau nagani nidai ki gama ki fito muna dashi in diba na amsa da fadin. Ba aiki ya kawo ni nan ba zuwa nayi in taimaka mata idan wace ta sani na girka ta fito sai ta baki daga haka ban kara tankawa ba kuma. Huumm,ummm kama kanki yarinya bakin rijiya ba wurin wasan yaro bane nan ba wurin raininki bane ko yarki bata isa ta kawo min rashin mutunci ba balle ke ? Muryan Asmaun mukaji a bayan mu tana fadin sannu da aiki Ramaah yauwa sannu anty na kammala na fada ina kokarin fita daga kitchen din. Ai da kice min munyi sabuwar yar aiki a gidan nan Saiba ta fada sai naji Asmau na fadin . Yar aiki kuma ina take kafin ta gano me take nufi sai tace haba dai kanwar tamuce kuma yar aiki daga taimako ? Ninaje gun yar uwarta na rokota tazo ta kama min kaina yana damuna da ciwo ga zazzabi kada mu zauna da yunwa. Ki duba irin aikin da yarinyar nan tayi muna kamar ba mutum yayisa ba cikin dan kankanin lokaci haka ga kuma gitki . Yarinyar tayi kokari gaskiya wanan matsalankice Asmau banga abinda zaisa na ja wa yanda sabodasu akaci min mutunci a gidan nan. Kitchen din na dawo ina fadin karbeta zanje nayi sallah ta mika hannu ta karbi yarta daga bayana zan fice take fadin zoki dibi abincin mana ? A,a akwai abinci wajen ,,,,, Dakata don Allah Asmau nifa ban son kaskanci ki bari in diba inyaso idan na diba sai ta diba din wani kallo nayi mata na wuce zuwa part din iya din. Koda na koma suna zaune da anty da Yanda a falon suna hira na shigo na fada saman kujera sai iya ke fadin har kin hada nace nagama iya. Ai yanzu dai sunga ranan dan mutum ke nan yaro dama ba a haifeshi don mutum daya ba yau da babu zaman mutunci ai ba zata zo neman alfarma haka ba. Ina jin tsohuwar saidai na kasa magana saboda maganganun da Saiba din ta fada min duk da ban kyaleta ba nima amma sai nake ganin ta shammaceni ai a lokacin data fada min magana irin wanan . Asmau ta shigo da abincin a cikin kula tana fadin ga abincin Ramaah kinki tsayawa ki dauko a,a ba zanci ba na fada ina gyara zama . Tace saboda me ko akan maganan da saiba tayi zakiki karban abincin aiba ita ta sakaki ba nuce na roka kiyi min kuma nagode da abinda kakai min. Ita haka halinta yake bata da tunane sai ta dauka kowa bai isa ba ita kadaice ta isa a gidan nan shiyasa ko yaushe kuke jin fadan mu da ita a gidan nan ai. Ba ita ta sakani ba ai balle ta dameni na fada ta dan juyo tana kallona sai kuma tayi murmushi a fuskanta tace. Yadda kikayi ai naji dadin hakan Ramaah tayine don kada gobe ki kara taimaka min kiyi fushin zuciya akaina haka take min wallahi. Duk wanda taga ina abin arziki dashi duniyan nan Saiba na bakin ciki da maishi ko gaisuwa batayi da kai indai ina hurdan arziki ki da mutum. Aiko zata wahala wallahi indai Ramaah ce dama bata nuna hakan ba da dukkanku kunji dadinta antyna ta fada tana dariya. Daga wanan ranan da haka ya faru muka dan fara shiri da Asmau a gidan har antyna suna dan biye juna sama sama . A cikin wasa Asmau zata jani zuwa wajenta muyi gyaran daki haka yarta a yanzu yarinyar tayi mugun sabo dani sosai idan ta ganni ta fara washe baki ke nan tana miko min hannu tana son in dauketa. Idan na bushi iska zan shiga wajen anty Asmau din mu dan taba hira sama sama da ita wanda hakan tun yana ba Saiba haushi har tazo takan dan saka muna baki a cikin maganan mu din wani lokaci. Wani lokaci kuma kamar bata san da Allah ya ajeni ba takeyi ranan da yan iskan nata suke kai saidai tayi ta jan tsoki tana jin haushi ta nuna cewa bata son zaman mu a lokacin. Wanan yasa ban faye damuwa da ita ba ban kuma fasa shiga ba idan na bushi iska ranan da ba karatu sai hakan yasa shakuwa sosai yashiga tsakanin mu. Saidai matsalan ta shine kazanta da kuma rowa tana iya hanawa mutane abu koda ba zatayi amfani dashi ba zata bar abin ya lalace saidai ta zubar dashi a karshe. Amma yana da wuya tace maka gashi a cikin dadin rai saidai in rabon mutum ne ya
Chapter 30 · 0% Book details