← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 306

Sashe 21

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanda wace akafi sani da maria kamar yadda aka rada mata zanen sunnanta tun haihuwanta inda sunan nata ya samo asaline ga sunan kakarsu kasancewar hakan da uwar bata iya kira saboda sunan sarakuwartace sai ta juya sunan a cikin harshen yarensu da yan mata. Dama sunan da mahaifiya ke kiran da dashi shine mafi karbuwa a bakin mutanen dake kewaye dasu don suma da wanan sunan zasu dinga kiran yaro saboda agane. Yanda yariyace natsatsiya ga ilimi da Allah ya bata na addini dana boko wanda sanadin samun hakan zaman da mahaifisu yayi a Abujan Nageria ne dasu. Inda yake sana,anshi na sayar da kayan masarufi wanda daga baya ya dan samu kariyan arziki saiya koma gadin gidan wani dan majalisan taraiya mutumin maiduguri. Zamane na amna a tsakaninsu don matarshi mutumiyar arzikice dama ance silan gyaran gida yada a wajen mata don ko hjy itace tasa Yaro ya dauko iyalinsa ya dawo dasu gidansu a inda suke wani unguwa a cikin masaka. Zuwan yairo birni da kuma kariyan arzikinshi kuwa ya samo asaline daga kiyayya irin na yan uwa daya taso a cikinsa kusan bafulatani da riko haka kuma duk bafalatin asali suna da wani hanya irin ta kaucewa da suka rike dimun dimun a zuciyarsu wanda ba kowane zaisan wanan ba sai su yasu yasun su yan wajen. Zaki gansu adaji suna rayuwa kiyi ta tunanen ko basujin tsorone wai idan kika zauna kikai nazarin fulani da kyau koda a birni suke kuwa zaki fahinci asalin fulani yana da wani boyayyen siri nai kama da surkin jinnu a cikin halaiyansu. Wanan zancen ba karya bane haka zancen yake duk da fulanin yanzu ba damuwa da irin abubuwan haka sukayi ba suma don wayenwa kai a yanzu. Zakiga tsofin fulani ba kasafai zasu iya barin daji ba saboda anan Allah ya halicci rayuwansu tare da dabbobinsu da tsuntsaye da sauran namun daji dake kewaye dasu da kuma sauran abin boye. Kiyiwa kanki tambaya ke mai karatu su basu tsoron dajine wai ko basu tsoron dare da abinda ke cikin darenne wai wanan amsan yana ga balafulatanin asali daya san kansa wanda bai iya ruwa ko a cikin mutane sai gefen daji zai zauna shi kadai. Irin hakane da Allah ya tsamo Yairo daga ruga don yawan tsagwaman yan uwa ya dawo birnin ya fara sana,a sai suke ganin ai yaro ya lalace a yanzu ya zama dan duniya. Abu ga Allah haka sukai ta jefo masa asiri tun bayan da sukaga da gaske yaro keyi da zaman birni tunda har yazo ya dauki matanshi da tsohon ciki zuwa birno to tabbas zaman Yairo birni ya tabbata tunda har ya iya daukan matarshi dele suka koma birni da zama. To tanbada ya hau kan yairo ke nan a yanzu ka,ida wanda suke ciki daya zai tattara dan sauran abinda ya bari ya hade da nasa na tsawon wasu shekaru idan bai dawo ba sun zamo nasa ke nan ladan kiyo. Haka baffa sa,idu ya tattara sauran dabbobin mahaifisu ya hade da nasa ga bakar asirin dayai ta jefawa Yairo din wanda gida ya fita ransa baki daya har yakai yayi haihu hudu duk bai tako gida ba. Allah ya rufa mashi asiri rikon amanansa yaja mashi farin jini sosai ga Alh da iyalinsa da suka rikesu amana a tare dasu da farko zuwa yake shi kadai sai bayan wata yace zai tafi dubo iyalansa. Ranan Alh da hjy ya samu a tsaye yazo sallamansu akan yana son ya dan leka iyalinshi don bashi dayane maigadi ba sukan shirya a tsakaninsu sai mutum daya ya tsaya ya fake gida har dayan ya dawo irin hakane yazowa Yairo din . Kudin mota Alh ya bashi yana godiya har ya dan daga hjy Falmata ke fadin wai kai Yairo har ina iyalinka suke zaune kai din mutumin wani garine wai ? Ya dawo ya gurfana ya soma fadin hjy ni mutumin nan Gembo ne nan wajajen tasanwa kasan Camero saidai yan uwana da kowa nawa sun ketara yanzu suna kasam ccamero din da zama. Iyalina kuma suna nan masakane zaune inda na kama haya a nan na barsu suke zaune nan masaka na Abuja ko ince nan Nasarawa yace kwarai hjy nan na kama masu haya suke zaune don yafi min kusa da zuwa can gida. Matarka dayace yara nawa yace dayace hjy da yarinya daya da take goyo kallon mijinta tayi don a gaskiya suna jin dadin zama sosai da yaro mutum ne mai mutunci da kamun kai sosai mutumin. Ai ina ganin Alh basai na dako wata yar aiki ba indai matarsa zata iya min komai ai gara ya daukota nan tunda ga wuri zaifi sauki. Yafi muyi tafiya mu bar yaran nan a cikin zullumi ko yaushe ina ganin haka yafi ai ko meka gani kai yaro ? Hjy nikan in anyi min haka ai banda bakin godiya a hakan Allah ya kara daukaka da nisan kwana nagode kwarai Allah kara rufa asiri amin hjy din ta fada. Ta dora da fadin yanzu kaje duk shawaran da kuka yanke sai muji ko mu ganku tare ya kara mata godiya donshi mijin yana ta faman amsa waya a lokacin. Wanan ne sanadiyan zuwansu zama gidan Alh inda hjy taji dadin zama da Ashatu mata mai kirki bata da kiuya ga tsabta da mutunta kowa har yara . Jin dadin zaman nasu yasa hjy batayi kyashin sakasu boko ba tasa aka hada Yanda da yaranta suna zuwa makaranta haka kuma ta islamiya da suke zuwa a tare da ita. Wanan yasa yaran suka taso cikin jin dadi da natsuwa ba zaki taba sanin su din yayan tugga bane don basu taba sanin wani abu rayuwan ruga ba. Sun dauka Alh dan uwan mahaifisune don su kadai suka sani a danginsu lokacin kwatsan ranan mahaifisu ya samu labarin rasuwan tsohonsu hakan yasa ya roka da zasuje gida har yaran. Ba jin komai hjy tasa aka kaisu har garinsu cikin motan gida wanan zuwan shine yayi silan komai garesu. Don kuwa mahaifisu bai dawo gida ba saida dafi da aka jefashi dashi inda ya dawo yayi ta jinya daya zamo ajalinsa akarshe. Anan babban asibitin Abuja Allah ya dauki rayuwansa ganin halin da iyalin yaro suka shiga yasa Alh da hjy suka kaisu gida da kansa da niyar suje suyiwa yan uwansa ta,aziya su dawo dasu daga baya. Saidai tun zuwansu budan bakin baffa fara tambaya yayi ina dukiyan dan uwansa daya tara abuja din ? Mamakine ya kama Alh yace shidai a saninsa baisan Yairo yana da wani dukiya ba yasan dai duk wata yana bashi hakkinsa kuma yaransa kaf sun dauke masu laluran karatunsu suke biya shida matarshi. Karshe dai ba a rabu da dadi ba tsakaninsu da Alh saima sukace zasu bar iyalansa a nan don za a dinga zuwa gaisuwa ana tambayansu daga baya in komai ya lafa zasu nemesu. Sukan tunda suka roko ko yanda dake shirin zana jerabawa a bari suje da ita sukaki suka fahinci ba su son yaran su koma hannunsu ne. Haka suka tafi suka barsu a wajen yan uwan mahaifinsu karshe da suka gano ashe dukiyan da suke zaton na yairone ba nasa bane ashe sai haushin hakan ya koma wajen yaransa. Nan wanan baffan nasu ya rufe ido yana fada yana fadin indai hakane dole su biyasu hakkin kiyon da Yairo ya gudu bai karasa ba ya koma birni da zama don iyalinshi suji dadi . Wanan dalilin yasa suke zaune a hannunsu cikin ukuba da tsagwama ga yunwa da wahala daya juye masu kamaninsu a lokaci guda. Dan wayan dataje dashima garin baffan ya karbe ya sayaryan suturunsu duk sun koda a karshe dole suka koma amfani da irin wanda mutanen wajen suke amfani dashi suka saje dasu baka gane sun taba rayuwan Abuja a baya. Irin wanan labarin da Yanda takan ba Abubakar a cikin waya shine suke tsuma zuciyarshi yana jin yana son ya taimaka masu duk da yasan karfin sa baikai ba amma zai gwada sa,anshi ya gani ko Allah zaisa a dace. Da haka kuma ta kara shiga ransa sosai yake matukar jin ko ta halin kaka saiya taimaki rayuwan Yanda din inma da son samu gaba dayansu zaiyi sanadin dasai sun dawo cikin gari da zama amma kuma ya kan tambayi kansa da taya haka zai faru ? ( IKKO Ikon Allah ) Tafiyan jirgine yayi don haka bai huta ba washegari ya fita wajen business dinsa yabar zancen da sai Meimbe ta nemasa da kansa don har yanzu bai kai ga yanke hukunci ba duk da malam na kusfa ya gaya masu akwai alheri tattare da wanan abin saidai zai dan fuskanci baraza amma kuma ya bashi addu,a tare da ruwan rubutu dayasha tun a wajensa. Haka kuma baiyi sanyi a gwiwaba tun dawowan nasa yana duk abubuwan da kawunan nasa suka bashi shawaran yayi don rigakafi a rayuwansa. Har wani annashuwa yakeji don abubuwa yanzu sai budewa sukeyi tun dawowanshi daga gida kofofin samunsa kamar an bude mai yake gani duk abinda ya taba cikin yardan Allah zaiga nasara akan abin. Haka saida ya tabbatar da matansa sun horu sosai kafin ya fara daukan wayansu koshi saida iya ta kirashi tana sheda mai zuwansu Asibiti da Saiba da aka tabbatar da tana da matashin ciki a jikinta na wata biyu da kwanaki. Kamar yadda iya ke fadamai tun bayan barinshi gida bata da lafiya wanan yasa ya kira Asmau ya fara jin lafiyanta kafin ya kira saiba din a gurguje suka gaisa yayi mata ya jiki ? Zata fara kawo mashi kissa yace aiki yakeyi zai kirata idan ya gama shine farkon da har yake saurarensu idan sun kira wayanshi din koshi ya kira yaji lafiyan jikinsu. Tunda ya tara guzame a gidansa don ko,wacesu tana dauke da cikinsa a yanzu ya zama dole ya kulasu haka kuma duk sati yana turowa ko wacensu kudi a account dinta don bukatun yau da kullum irin haka na mata. Yau ya kasance saura kwana biyu ya cika sati biyu da dawowa gidane suka hade miss meimbe a wani shago itace ta fara hangoshi ta nufi wajenshi cikin sakin fuska tana fadin kai kayi wuyan gani fa ? Shima murmushi yayi cikin dan basarwa yana fadin mun
Chapter 21 · 0% Book details