← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 215 OF 306

Sashe 215

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yadda naga dare haka naga safiya a ranan don ko ban runtsa ba har safe tunda na idar da sallah asuba na dauko wayata ina kiran maria. Duk da banso hakan ba nasan tana fama da kanta a wanan lokacin saidai haka ba zaisa ta shareni da yawa ba nayi magana tace mijintane yace ta natsu a waje daya saboda laluran cikin jikinta da take fama dashi. Tana dauka na hau kuka ina fada mata cewa ni zan tafi abujane nagaji nagaji ba zan iya ba hakkurina yana gab da karewa a gidan nan yanzu. Subbahanallahi meya faru Ramaah ta fada cikin rikicewa ta dora da fadin kun sake wani rigimane kuma yau din dasu ? Bamuyi ba zamu daiyi nan gaba kiris don har mama wanan karon zata san halina tunda bata kaunan mu to wai meya hadakune haka Ramaah ? Saidai kinzo zakiji na fasa ina kashe wayata a cikin takaici hankalintane ya tashi dan jin mena fada a lokacin don tasanni da karfin hali tasan halina idan na rikice kuma. Hakan yasa ta kira mijinta Habu take fada mai akwai abinda ke faruwa a can gida don na kirata hankali tashe har ina mata ikirarin cewa zan tafi abujane ko wajen ummah kaduna. Cikin tashin hankali yake fadin ohh lord mekuma ya faru matan nan basu bari a zauna lafiya baga Yazid a gida ba na kuma fada mai yasa ido a kansu. Bari na kira yazid din naji abindake faruwa zan kiraki daga baya da hakan suka rabu ya kashe wayan yana dannawa yazid don kira saidai bai dauka sai wajen kira na ukku ya daga suka gaisa. Suka gaisa sama sama ya soma fadin yazid meke faruwa a gidanne baka fada min ba ko dazun munyi waya da kai ai ? Wani gida ke nan yace nan mana yarinyar nan Rahama amaryan J ta kira hankali tashe tana kuka yace gaskiya ban sani ba dan uwa . Amma zan shiga in bincika yanzu habu yace dole akwai abinda ke faruwa gidan don dai ta kira a cikin kuka dazun nan har sun kare wayan zai kashe yace wait dan uwa. Kodai akan cikin jikintane suke magana dama nasan za ai hakan saboda jahilcin su irin na mata amma bari na shiga inji dai ? Ciki habu ya fada cikin mamaki yace eeh ciki gareta mana kuma na bincika na J din ne so me zasu tsaya sunyiwa rigima kuma ? Matarsa ce ba zina sukayi ba don me hakan zai zama abin tashin hankali kuma har su sakata kuka akan hakan su barta taji da abinda ke damunta mana ? Ciki fa kace habu a hakan har ta samu ciki dariya Yazid din ya kwashe dashi yace miji da matane fa meye kakewa mamaki kuma sai habu din yayi murmushi mai sauti yana fadin no banyi mamaki ba ai amma nayi kabar guy din nan inda kaganshi gaskiya J yakai dan iska haka ashe kana kwance haka ka dirkawa diyar mutane ciki ka barta a cikin tashin hankali da surutun mutane. Bari dai in shiga din inji kome ke faruwa ya daga daga kwancen yana zura jallabiyarsa a jikinsa zuwa cikin gida. Duk da bai saba ganinsu hakan a part din da safe ba yasan dole akwai wani abinda ke faruwa ke nan da gaske saidai ana ganinshi kowa yayi shiru sun gaisa dasu mama ya nufi cikin dakin inda dan uwansa yake kai tsaye. Ya jima a dakin suna tare dashi kafin ya fito ya fice daga part din don yayi nazarinsa baiga wani abin daga hankali daga gareshi ba don haka ya kyaleshi bai fito mai da zancen ba. Mama tudu ta sameni a daki ina kwance take fadin wai ba zaki tashi ki fito bane kina daki tun dazun kin dunkule ai sai hakan yasa baki gane jikin kiba ? Tsayuwan da tayi a kaina yasa dole na tashi na fito zuwa dakin kwanan mu inda na samu yaya J din shidaya a dakin yana kwance. Haka kawai naji ina ganin bakinsa tare da takaicinsa lokaci guda naji gaba daya ban kaunar ganinsa a rayuwata Saboda yadda zuciyana yake raya min duk wani kunci da tsana da nake fuskanta a rayuwa kusan nace saboda shine nake ganin hakan a yanzu. Banda ganin kutse da katsaladan din shigo masu rayuwa da matansa suke ganin nayi haka kuma a yanzu suke ganin na yaudaresu ko ina ha,intansa nakwaso ciki a waje nace shine dashi. Abu dai da yawa suka taru sukai min yawa a lokaci guda bake ganin gusawa daga nan din shine kawai mafita a gareni da zaisa in samu sallama. Ina jin muryanshi yana badaniyan magana dani dana shigo hakan baisa na juyo na kalleshi ba lokacin na dauki abinda zan dauka zuwa ban daki na shiga. Nayi kuka sosai a ciki kamar yadda na kwana ina sharban kukan a lokacin gab da in gama wankan naji zuciyana tana tambayana akan yata din da yanzu shi meye nasa a cikin zancen nan ? Da har na hada dashi nake fushi mutumin da ko a kwancen da yake yana nuna ina da muhinmanci a zuciyarshi aiko bai cancanci nayi mashi hakan a yanzu ba wata kilama wani abu yake so na shareshi baki kulashi anya kuwa Allah ba zai tambayeni dalilin hakan da nayi ba ? Ga mama nasihanta a gareni kullum idan mun kebe shine kada in yarda a ji kaina da mijina inyi hakkuri dashi dako wani irin hali na daure kada in taba bari a san tsakanin mu. Yau kuma sai taji akan abinda ba laifisa ba suji cewa ina fushi dashi har mun samu sabani a tsakanin mu nasan ranta ba zai taba dadi dani ba. Kodana fito abin mamaki yana kokarin dagawa daga saman gadon da kanshi da sauri na isa gurinshi nace kai kuma meye haka idan ka fadifa kaji ciwo. Maganan kamar an kwatoshi daga bakinsa yake fadin me akai maki meya faru naga kinyi kuka binshi nayi da kallo nace ina turu baki gaba ni banyi kuka ba. Ya koma ya zauna yana nishi na juya zan nufi wajen kayana haka kawai aka banko kofan dakin kamar a cikin fushi duk muka bi kofan da kallo cikin mamakin ko waye ? Saiba ce tana wani huci a fuskanta tana ganina taja tsuki tana fadin ai duk abinda mutum keyi a boye Allah naganinsa kuma ba azzalumin kowa bane. Inma wani kato yaba yarinya ciki take kokarin dafawa mutane sai Allah ya baiyana maishi ta nufi wajensa ta aje kayan abincin data dauko na karyawa. Ban kulata ba yi nayi kamar bansan ta shigo dakin bama a lokacin don ko gaisawan dole da mukeyi da aka tillasta munayi a tsakanin mu bamuyi ba a lokacin. Kokari nayi na taushi kaina ban kula mata ba na juya na fita bayan na saka tufafi a jikina nakai kofa take fadin iskancin banza sai asirin yarinya ya tono a gidan nan. Azo ana daga muna kai ashe ba class ba aji nakowa clininc cema kowa ya hau ya wuce hakan data fada yasa na tsaya na juyo ina fadin komai zaman mutum nakowa ubanki yayi kadan ya shiga wanan clinic din. Ke dawa kike wakike zagi nace da wanda ya amsa min da ita nakeyi kamar su mama suna jirace sai gasu sun fado dakin ita da iya. Kai kai lafiya wai meke faruwa hakane kuma daga shigowan ki nifa irin fadan nan na cacan baki na kauyanci na fada maku ba a nan ba don bashine a gaban mu ba yanzu. Har ita ta isa ta zagi ubana ita din me abin banza ke inkina da kunya har kina da bakin magana banda abin kunyar da kikaiwa kanki din nan ? Miji yana kwance haka sharkaf kije ki dauko mai cikin shege ki kawo mai zaki mana mashi don an kiraki da yar iska zagi akayi ko halinki aka fada ? Ai shine nace da ubanki mukayi iskancin ko don sune manyan gidan yan iskan da muke zuwa,,,,,,,, Muryan yaya jafar dake badaniya a saman gado ya dakatar damu duk daidai shigowan mama da tawaganta yake fadi da karfi ba cikin shege tayi ba nine da kaina nayi abina. Yana fada yana kokarin nuna kanshi da hannunsa don a gane me yake fadi to kinji abinda ya fada dai yace cikinsane abinda yake fada ke nan yayu wani kada kai alaman ehh kamar wani tsohon kadangare dashi lokacin. Yana kokarin cigaba da maganan da yake son fada kowa a dakin yai shiru yana kallonsa yace saiba kiyi hankali idan kika kuskura kika sheganta min cikin nan zan sakeki ya fada kamar maganar tana kwato mashi a bakinsa. Haba dai wai meye hakane kin gani idan kika jawo muna wani matsala a cikin zancen nan wallahi ranki zai baci sosai yaron nan tun farkon maganan nan ya nuna cikinsane yasan da hakan ba shike nan ba ke meye naki a cikin zancen wai ? Ciki dai Allah yayi lokacin zuwansa duniya yayi a haka ba wani mahalukin da ya isa yace kar yazo yau ninaji karfin halin maye da hauka. Akadara ma bash yayi cikin nan ba ke meye naki a ciki zancen nan yanzu tunda aurene kawai ya hadaki damu yarinyar nan kina da karfin hali sosai wallahi. Maman tudu take fadan hakan a cikin hasala iya dake salati tana fadin yanzu yarinyar nan sheganta masu cikin nan kike kokarin yi ko me ta cabe zancen mama da fadin. Yarinyar nan wai hankalinta daya meye a cikin zancen nan ke kishiya tunda dubu ta nuna kinfi kowa a wajenta har yakai zaki wuce gona da iri ? Ke Nusaiba ku fita daga nan, na fada maki ai inma ba cikinsa bane ganewa za ayi tunda ba a bace jinin gidan nan suke ba. Ni dai nafice tare da nazarin lafazin kowa a wajen nayi koka sosai a ranan daga baya naba kaina shawara akan zancen sai zuwa karfe ukku ya Habu da yanda suka shigo gidan. Ina jin muryansa suna gaisawa dasu mama suna tambayan yaushe ya dawo yace da ranan nan ya wuce ya shiga wajen dan uwansa. Ya jima a ciki ya fito yana fadin amma mama abinda yarinyar nan takeyi a gidan nan yai yawa
Chapter 215 · 0% Book details