← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 258 OF 306

Sashe 258

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

karara ga yar nata dake wanan magana. A,a iya rashin hankali yake son ya tafkawa mutane waishi ga salamame zaije gun yarinyar nan Rahama ya tare don rashin hankali ya daukarwa kansa zunubi. Zunubi a wajenwa Dubu wajen ki ko wajen wa zai dauki zunubin da kike fadi dubu ? Dubu dubu kanki daya kuwa da yaron nan yayi wata da watanni a gidan nan meyasa bakice a kwashshi a kaishi can ba lolacin kada ya kwashi zunubi sai yanzu ? Iya wanan ai lalurane itama din ai tana tare dashi a nan kuma, zaman nan din aida ita akayishi da yanzu zatace a maimaita mata hakan da akayi ? Ta fada maki cewa sai an mata maimaicin hakan a gidanta wai dubu meke damunkine haka wai ? Kai Yazidu koma dakinka ka kwanta don ba inda zaku a cikim daren nan da wanan rashin hankali na uwarku don kina mara hankali zaki gidan surukarki da wanan zance na hauka idan kinje kice masu me yanzu ? A,a iya ki bari nayi maganinsa tunda yana ganin ya isa ne yanzu har zai kwashi kafa ya koma can ya tare bai fadawa kowa ba ? Kamar yaya Dubu don ni ban fahinci wanan rashin hankalin naki ba har yanzu waiko dubu akwai hankali akanki kuwa ? A fahintana Dubu kamar kishi kike da yaran nan fa don abin nan da kikeyi bana kai sake bane dubu ban taba gani ko jin irin wanan rashin hankali naki ba gaskiya. Iya yanzu sai a kyaleshi yaeinya karama tana juyashi ana kallo ba a dauki mataki ba jinyar da tazo nan tayi nasa ai yan uwanta dashi ta cuta ga hakan ? A,a ba juyashi tayi Dubu mulkeshi tayi iyakar juyawa dai ko aiki ya sameki babba idan kikace kishi zakiyi da matan yayan ki ? Duniya da mutanen cikinta suna shirin maki dariya jeki dan mutuncin dake gareki a idanun yarinyar nan ya zube aikin banza aikin wofo kawai da rashi kamun kai ? Kai yazidu koma wajenka ka kwanta ba inda zaku ni naga rashin hankali yau a filin Allah ashe ke ba zancen yaron nan daya batane ya dameki ba shirmenki kike a zuciyarki ? Yau ni naga hauka na rubutawa a jarida Dubu baki tsoron bakin duniya ko wanan halin da kikewa yayan mutane ya tambayeki nan gaba ? A,a iya don Allah abar zancen nan baikai har kiyiwa yaran nan baki ba a gareni yaje ya zauna tunda ya zama sallamame a wajenta. Karamar yarinya kamar wanan yau zata juyawa Jafaru hankali yana wanan abin a gaban kowa iya dole inyi magana abin yayi yawa dama an fadi matan fulani haka suke idan sun shigo waje. Kai Yazidu dawo ka kaita ta dauki matakin da zata dauka iya ta katse mama din dake magana ta juya tabar wajen yazid kuma bai ko juyo ba ya shige part dinshi. Washegari da safe kodana tashi kamar kullum na hada mai abinda zai rike mai ciki kafin mu gama breakfast ya dan kwanta. Hakan da nake mashi ba karamin kara mai lafiya yake masa ba ga sunan Allah da zaibi jikinsa da ruwan zamzam ga kuma kuzarin da jikinsa zai dauka yana daga cikin abinda Yazid ya hango na annuri a garesa yake fadin yaga ya canza mashi lokaci guda. A gurguje nake aikina ba don wani abu don kawai nasawa raina cewa suna iya zo min gida a ranan don Aminu dake nan wajen mu. Mun gama na jera mai a kasa don na fahinci a yanzu yafi son ci a kasan don kamar baijin dadin zama saman kujera yaci abu a yanzu da baida lafiya din nan. Na gama na shirya kaina na umurci biba data jetayi wanka har tace ta dauki abincin Aminu takai mai ne da sauri na juyo nace a,a ki barshi nan kitchen har ya shigo. Ba son komai nace haka ba saboda ban manta wani case din daya faru akan wata uwa dake tura yarta kaiwa saurayin gidan abinci ba. Amma haka mutumin yayi amfani da wanan daman ya batawa wanan matar yarta akaita case din karshe dai an cuci yar da uwar don har yakai ga dirkawa yarinyar ciki dole aka haifi dan hakana kuma yarinyar karamace sosai a lokacin. Wanan ya tsaya min a rai yasa nake kafa kafa da yar mutane ban yarda ko maigadi tayi wani dogon mu,amula dashi iyaka gaisuwa a tsakaninsu. Gareku mata wanan abin ya faru da gaske wallahi mutum koke kika haifeshi yanzu ya zama dole a gareki ki saka ido ga mu,amulansa na yau da kullum Allah ya tsare ya kare amin. Wasu dogon riga na saka a jikina _onion_ colour da adon zaiba har kasa anyi rigan mai dagware a sama kamar alkyaba yana daga cikin dinkin da anty salma tayi min na aure a Abuja. Zaune na samu yaya a dakin na shigo ina fadin ka tashi ashe yake fadin yazid ya tayar dani da waya wai yaron nan sun dauka ya batane ashe basu san yana nan ba ? Aminu na fada cikin mamaki yace shifa kiji ba yace muna ya tafi can ba ashe karya yakeyi ke nan nan yayo direct wajen mu. Ikon Allah amma cewa yayi ai yaje ya samu baka nan ace kana nan yace karya yakeyi yanzun ka fada masu yana nan dai ko ?/ Na fada masu ya fada a sanyayye nasan zasu shigo yanzu ai tunda sunji yana nan amma Aminu bai kyauta ba daya dagawa mutane hankali haka ? Bar dan iska kilama abinda ya fada karyane barshi kawai bari suzo din muji ai nasan za a fada masu abinda yayi ya gudu nan yau din nan zai bar min gidana. A,a yaya na fada da sauri ya katseni cikin tsawa da fadin ke karki tsoma min baki cikin maganan su ki barni kawai dasu. Nayi shiru kafin nace wanka zakayi ke nan yace haka naso na mike zuwa bandaki na hada mai ruwan wanka ya mike ya shiga saida ya gama na cude mai jiki da ruwan addua ya saka kaya muka fito falo. Mun zauna ke nan na zuba mashi ya fara ci biba tana gefe daya tana cin nata don sosai muke sakewa da yarinyar harshi sukan dan taba hira wani lokaci da ita. Muka ji sallaman Salima shigowa gidan ashema dukkansune tafe sai Asmau ce sai matar Yazid suka bari a gida lokacin. Ban daina mika mashi fruit din dana gyara ya zama juice ba da nakeyi na amsa sallaman nata ba tare dana juyo ba suka karasa shigowa gidan gaba dayansu. Nagama na dago ina fadin sannuku da zuwa ina kwanan ku a cikin jam,i bansan waya amsa ba ko wanda bai amsa ba a lokacin don na basu bayane ina zaune amma naji muryan yazid. A,a a a mutumina inafa zaka koma gida wanan riritakan da yar nan keyi shine ka gudu ka barni ba azo cin dadin amarcin dani ba ? Iya ba gaki kinzo ba yanzu saiki zauna muci dadin yanzu kada in kwareki kaidai tunda ina da rabo a cikin na yanzu sai in zauna inci amma zan barwa amaryaka aronka kwana biyu ai don tasan ina da kara amma fa a tuna damu muma kada a shagala suka kwashe da dariya. Ai fakaice baiyi iya gara ki fito mashi fili tasan yabar wasu a gida ba nan bane kawai gida a gareshi don shi naga hanyar konewa ya zaba yanzu. Bani ganin hakan cikin zuria,ata insha Allahu daidai lokacin namike a kusa dashi zuwa gaban mama na durkusa har kasa ina gaida ita. Kamar dole ta amsa min ba kin dawo lafiya na juya wajen kawu na gaidashi sai iya dake fada na rike hannunta sai lokacin ta dakatar da zancenta take fadin. Ke dai yar nan kin dawo lafiya yaya kika bar yan gidanku duk suna lafiya dai ko naso nazo banda wanda zai kawoni in maki sannu da zuwa. Iya ba komai na fada ina mikewa tsaye na nufi hanyar dakina muryan ya J naji yana fadin ina kuma zaki ? Daki zan tafi har ku gama na bashi amsa sai yace abincin fa wazai ban kizo ki zauna muci kema baki karya ba ai bari dai ku gama na fada. Kizo ki zauna nace me zamu fada wanda ba za aso kiji ba iya na fadin zo ki zauna abinki ai ba komai zamuyi ba ballema ina zata iya ? Yadda yake magana hakan yasa na dawo na zauna a inda na tashi duk suka zuba muna ido gashi sai magana yake min a cikin rashin damuwa da suna wajen a lokacin.
Chapter 258 · 0% Book details