← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 306

Sashe 16

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

tashi ba har yanzu. Kuna da kokarin yaran nan saidai kai Jafar matsalan matan da Allah ya bakane sai addu,a mata ba sanin ciwon kai ace har yakai don rashin hankalin kishi irin nasu yar nan ta watsawa uwarku abinci a jikinta abinci mai yawa don wullankaci su wullakantashi haka wuein bakin kishin su na tsiya ? Abinci kuma suka watsamawa Iya kardai zancen da Nusaiba ta kirani ke nan shekaran jiya take son min ban saurara ba don dama shiya kawoni garin nan jiya tunda naji ta ambaci sunan mama a cikin zancen ta hankalina bai kwanta ba na taso. Kaiko dai akan wanan zaka taso haka zuwa nan iya shegen yaran nan ne kawai don batama san da ina tafe ba ai kodata jefowa yar uwa abincin sai saman jikina ya dira ya zube banso iya ki fada mashi ba ai tunda anyi ya wuce ko tun a wanan ranan indai zasu gyara su gyara don ba,a wasa da abinci. Mama indan iya bata fada min ba waye zai fada min bayan don haka take zaune damu gidan idan suna abu ba a tsawata masu watarana ai za a samu sun illanta kawunansu a dawo ana ganin laifin ku daga baya. Zasu aika tundai wanan mai zubin yan ruwa da take daukan kanta wata tsiya banda karyan banza da ci mutunci babu abindata koya a duniya na kwarai Iya ke fadan wanan magana a cikin hasala. Sallaman Abubakar falon yasa suka sake zancen ya shigo suka shiga gaisawa da juna kafin ya sanu wuri ya zauna mama dubu ta jefo mai tambaya tana fadin kayan can dakazo dasu fa Habu ? Juyawa tayi ya kalli wajen da mama din ke kallo kafin ya dan bata fuska yace daga can nazo dasu meye a ciki Jafar ya tambaya ? Mikewa mama tayi ta isa wajen jarkan da akaiwa nadi cikin buhun irin na da da ake amfani dashi sai wasu kwanduna da aka rufe da ganye zakice gorone a cikinsa aka rufe ta shiga budewa . Yayin da iya da su Habu din suke hiran yanayin kasan Cameron da irin mutanen dake rayuwa a cikinsa muyan mama dubu sukaji tana cewa Habu wanan ai ba karamin kaya bane ka dauko ? Meye a ciki mama Jafar ya tambaya yana mikewa mama ta juyo tana fadin wallahi nono ne da danyan madara wanan kuma kindarmo wanan wara da ake kirada (wagashi ) warar fulanice ta ainihi da aka sani da ainihin nonon kindarmo za,aita dafashi har ya cure a waje daya kana a dauko buhu ko abin tsama a matseshi yadda akeson girmansa saidai nasan akwai sauran fasahan wanan abin da ban fada ba a bayani amma dai nonoce zalla ta kindarmo sabon tatsowa ake wanan wari din dashi wanda akecinsa danyensa ko kuma a yanyankashi kamar nama a sayo da mangyada ko manja. Shi wanan abin yanzu soyashi za ayi Jafar ya tambaya mama Dubu tace kwarai kuwa sai kace a karo maka idan an soya din ai ana amfani dashine kamar nama zaka iya zubawa a cikin miya a dafa miyar dashi ko kuma ka watsa saman shimkafa kamar nama. Ban taba ganinsa ba Jafar din ya fada nima dai gaskiya bansanshi ba Yaya J , kawai dai naga ana sayane nace nima aban na sayo wasu mama mashi nazo dashi. Mama Dubu dince ta katse su da fadin wanan kuma chikwi nefa Habu sai ta mike tsaye tana fadin amma kasha kudi a wajen nan bari nazo na dibawa yan gida akai masushi a mutuncinsa tun bai tabu ba don in suka kai kwanakin da zanyi a nan suna iya lalacewa. Kallon juna diyan nata sukayi wanda ta fahinci nufinsu tace meye duniya Malam idan kaba wani ya kare idan baka bayar bama karewa zaiyi gara ka bayar din kaci moriyansa can inda bakai tsamani. Ai bamuce komai ba mama zuwa anji zan shiga na gaidasu da yamma sai a zuba na fita masu dashi don naga shi Habu kamar da sauran gajiya a tare dashi. Duk wanan nono shanune a cikinsa ya nuna sauran jarkan dake rufe mama din tace ina gani tana kallon danta habu ko zai masu bayani maimako ya bada amsa sai ya juya ya koma saman kujera a daidai lokacin mama ke fadin ikon Allah man,shanune haka cike har jarka. Kai habu wanan lissafin dariruwan kudi akeyi fa ina kasamo wanan kaya haka kamar na gara Iya ta fada tana mikewa zuwa wajen taga man shanun da aka fada din. Sai fadi take saidai wani lokacin suyan manshanun fulani kamae harace don basu irin suyan mu na mutane gari a saka albasa da gishiri don yayi kamshi haka suke soya abinsu ba komai a cikinsa. Kada kisha idan bai hadu ba Habu kai kaji iya tun bataci ba fara kushe abin murmushi yayi kafin can yace ba manshanu ba ai har mai man shanun zan dauko maki gidan idan ta girka ta baki kada kici tunda basu iya suya ba. Au to kinji abinda ya fada shidai ke nan bafulatanan kasan can da sukaje zai auro sai ki shirya Iya kishi da balatana kuma yanzu. Barni a Iyata da nake yayan hauawan ma gasu gaban mu na kasa gane kansu yara kamar kansu aka fara kishi yara kanana da bakin kishin tsiya irin ta hauka. Ai ba dukansu bane basu da hali iya habu ya fada don gara Asmau ita tasan darajan kowa batawa mutane rashin mutunci ita. Babu gara kana ina suka watsawa uwarku abinci saman jiki ga hijjabin can ta jika yaki fita har yau don iya shige irin nasu . Abinci kuma suka watsawa mama a jikin garin ya haka ya faru mama kai ya jafar wani mataki ka dauka akai yanzu ? Shine nan ka ganni zaune ina son iya tayi min bayanin abindake faruwane sai gaka ka shigo aka kawar da zancen da muka soma. Ai bada sani hakan ya faru ba nan dai mama ta kwashe yadda abin ya faru wanda ta sani ta mayar masu ran yayan nata ya baci sosai da hakan tunda Abubakar yafi daukan zafi akan zancen. Ya dago kai yace mama shine kuma kike cewa a kyalesu har su iya wanan abin kuma a saka masu ido gobe su kara wanda yafi wanan ke nan ko idan an kyalesu. Kaiya ita wanan mai shigar cikin bafa laifinta bane na fada maku yadda zancen yake ya juya wajen dan uwan nasa yace kai kaji bros ya lumshe idanunsa don baida abinda zaice kuma tunda mama ta hanashi daukan mataki akai tace rashin sanine ya jawo hakan yayi hakkuri da matanshi ya dai tsawata masu kan hakan. Gaba daya falon yai shiru saiga Asmau tashigo da sallamanta ganisu haka a zaune yasata dan tsarguwa tana kuma mamakin ganin har Habu da bai faye zama dasu ba yau duk suna tare hat dashi. Sun dai amsa mata gaisuwan saidai ta tsargu duk da wancan kaifin ita bata sashi a zuciyarta ya tsaya mata tunda ba itace tayi laifin take gani. Sai bayan ta gama gaidsune ta dubi mijin nasu tana fadin yaya J an gama breakfast don haka ta taso ana ce masa a cikin unguwa kaf manya suce dashi malam din gidan Sanda .
Chapter 16 · 0% Book details