Sashe 166
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mummy ko ranan sunna gani zaune tana raba abu data kawo kaina ta tsalakeni taba ta kusa dani ko ruwa saida dare mummy salima data ban abinci nasha ruwa a gidan nan ranan. Kinji ko ai kinji tsiyar basu da hankali ke meye naki a ciki ina mijinsu ya kawoki nan zama ko wajensu kuma yana iya kaiki ai inga halin arziki ai. Sun kasa gane hakan da sukeyi suna bata kansune a wajen yan uwa duk da yan uwan suka nuna masu sunfisu daraja bakomai bane kuma hakan sai kwadayin duniya. Ai kinga uwarki da yar uwarta da suka kama kansu inba wani dalili mai karfi ba basu zuwa gidan balle su shiga shirginsu din bakiga suna mutuntasu ba dole tundai Rukkaiya da bata daukan raini. Shigowansa ya katse masu zancen yashigo yana fadin iya kedawa ke fada haka tunda safe tun ina falo nake jin muryan ki ? Nida sarakunan kishin nan mana matanka su nake zankada tunda safe matarka tace damu yau tare zamu karya dakai shine abin yaban sha,awa nake fada dasu. Murmushi yayi yana kallona yace haka tace ta hanani barci wai in taso kada mu barki da yunwa kiga laifinta ? Ina laifi yar nan kin maisheni kamar basaraka ko sarakuwar uwarku ban samu rabin gatan nan a wajenta ba gashi na samu ga jikokina. Iya ai dole muyi maki kece fa gatan mu ga baki daya in ba ai maki abinda zakiji dadi ba aiwa,washi iya na fada na mike ina jin tana fadin cikin raha ashe gaskiyane akwai mata masu tsoron kishiya gashi ko nagani a yau. Falon muka fito gaba dayan mu nan aka zauna saman babban shimfidan da nayi maimakon danning din saboda tsohuwar na fara zuba abincin sai kamshi ke tashi . Yayin da iya ke faman zuba cikin washe baki da jin dadi muna tsaka da cin abincin sai sallaman mama mukaji da kawu sun shigo. Kawu yana fadin a,a lalai iya kan ba zata koma gida ba ana haka duk wanan didiman haka iya ? Kayi bakin ciki da hakan ne tunda ka kasa danka ya dauka yanayi ko iyan ta fada na yunkura na mike ina mai barin abincin tare dayi masu sannu da zuwa. Na gaidasu suka amsa kawu yana fadin nina isa in bakin ciki iya tunda jafaru ya kama muna ni dama nace da wuya iya kiyi zancen gida a yanzu tunda mukajiki shiru haka ashe dadi jafaru ke narka maki a nan haka ? Ta sake fadan kayi bakin ciki ke nan nace aka kwashe da dariya mama idonta yana kan plate din abincin kowa take fadin. Ai dole ta koma gida tunda a can take gamu sai zaraya ta barmu munayi zuwa nan dubanta sai iyan tace na hutar daku ku zauna gidan ku nan kan banda ranam bari inma daukana kukazo yi to ba zani ba. Kitchen na nufa na barsu suna drama da tsohuwar tasu har na dawo na aje plate din a gabansu ina kokarin zuba masu abincinne mamatace nikan a koshe nake ban fito da yunwa ba. Ai badon yunwa zata zuba maki ba dubu tunda tasan mijinta bai kaza dake ba kamar yadda ya bayar nan ya baku a can ai. Amma karrama bako yana cikin koyi da sunnan ma,aikin Allah ai ko kin isa kija da hakan kuma yanzu baki zuwa gidan nan kice wai a koshe kike baki fito gidanki da yunwa ba ke ? Iya idan ban koshi ba ai zanci koda yaya yazo daukata ya samu ina cin abinci gashi nan ki tambayeshi ? Amma ba irin wanan bako nidai na zuba nakai plate din a gabansu ina daukan nawa na mike inacewa biba ta taso muje daki muci. Shidai yana zaune yana jinsu sai abincinshi yakeci kawu ya fara jawo nasa plate din ya kawo gabanshi ya soma ci ya fara fadin dubu kici abincin nan kada mu kwareki don Allah. Ina iya zata yarda ta koma can tana hada wanan a rana haka kafin yakai karshe tsohuwar tace ance kaci mai dadi idan ka samu daman hakan. Can babu mai dadin ne iya wanan ai sai a dauka can bamu da irin cimar nan a can din sai dai ace kawai gyaran ba daya bane kawai. Ina gyara zaizo daya dubu tunda ilimin abin ba daya ba kefa dubu duk abinda zaki fada iya ba jinki zatayi ba a yanzu don haka kiyi shiru kawai da zancen nan . Iya munzo akan maganan yaron nan Yazid ne da Jafar ya sanar damu dawowanshi wai kuma har da iyalinsa yanzu iya ga Jafar fisabilillah abinda yaron nan ya aikata muna yayi daidai ke nan ? Ace wai yazid daga zuwa karatu yaje kasan mutane yayi aure a can bada sanin kowa ba a cikin mu ina shi ina zuwa auren wani kasa iya don Allah ? Zakija da ikon Allah ke nan ko duk abinda bawa yayi mukkadarine garesa dama dalilin hakan yaje kasan da sunan karatu don ya hadu da matar nasa hausawa sunce matar mutum kabarinsa ai . Koda rarafe sai yaje tunda Allah yayi a can matar nasa take kuma dan uwansa ya fada maki dalilin hakan to meye na damuwan zuciyarki ke a yanzu ? Iya ba hakana bane naga kayi aure a gida ka auri matar da akasan dabi,u sunzo daidai yaya aka kare balle ka dauko a wani kasa kazo da ita nan ? Idan yazo kuma yace saman kanki ko a karkashin wani zai zauna da iyalin nashine wai meyasa kukewa aure shigan kutsu dubu aurensane bancin ranki a yanzu ko dawowansa kusa daku ? Iya abinda nake son ki fahinci dubu a nan shine da yaron nan ya dawo gida yayi aurensa a cikin gata kamar yadda kowa keyi zaifi mutunci kinsan halin mutanen yanzu da maganan da bai shafesu ba iya. Sai abarsu suyi tayi yanzu ai tunda aikin gama ya gama ko aure harda haihuwa biyu yanzu meya rage don Allah ? Ni kawu banga abin tayar da hankali ba a nan tunda shi zai zauna da matarshi na fadawa mama addua kawai zata bisu dashi yanzu don Allah. Yaron nan da karatunsa inma yace bai sana,an nan sai aikin gwaunatine yana dai da ilimin sa ko da zai iya rike iyalinsa tunda acan aiba mu ke rike mashi dasu ba. Yarinyace karama kwarai matar nasa yar wani malaminsune yaga kirkinsa ya aura mashi yarsa ba ba tare daya san kowa nasaba fa mama . Yanzu kuma munan sai muce hakan bai muna ba mu nuna bamu ksunat yarsa mu don kawai bata fito cikin nahiyar mu ba amma dai ai musulmace ko ? Nasan dama bakin ku daya dashi tunda kai ya iya fadawa zancen ai dole ka fito da wanan zancen yanzu baka son a fada tunda kuma kun auro matanda suke son sunfi karfin mu. Zancen duk a kunnena yake muke nan mama ke nufin muna son fin karfinsu da mukai mata me na rashin mutunci don kawai mun fito yayan fulani ba zage zagi ba kome ? Saidai kafin nakai karshen maganan zucina naji iya na fadin shi auren kabila ai ba bakon abu bane don kowa yayi a cikin mu dagani har ke kuwa dubu ? Mahaifinki ai asalinsa banufene suka dawo nan da zama aka saje kuma na aurensa tun asalin yarensu bai bace ba haka kema kuma kika auri mahaifin yaran nan kowa garin nan yasan zuwa Alh yayi garin nan nema daga Adamawa koba haka bane meye bambancin zance a nan ? Sai mama din tasa kuka don me iyan ta fadi hakan Biba najin kukan mama ta mike tsaye kamar zata fita a dakin na zabga mata harara ina fadin karki soma haka ace dake munafuka. Yaya irin abinda nake gudu ke nan tunda Habu yazo da zancen aurensa naso hanawa amma ka daure masa gindi akan babu komai gashi. Jin dadin auren har kanwarta ta cinnawa shi Jafar a yanzu gaba daya kowa yasan yaran ran sun juye min kan yara don ba haka na tarbiyarta da yarana ba duk kun sani a nan ? Dubu ki shiga hankalinki wallahi kafin na saba maki a wajen nan meye hadin auren Yazidu dana jafaru kona habu yanzu ? Kin fa kusa kai yaran nan makura akan zancen nan idan yaran ku sun sauya ku kuka sauyasu ai ba wasu ba ? Ko har kin manta da cin mutuncin da kukai mai keda diyan ki da dan uwanki gashi ? Nace kin mantane in tuna maki yanzu yadda suka zugaki idonki ya rufe akan danki dake tausayin ki kan dukiyan da yake kula maku dashi yanzu ina dukiya nan ku yake ina tambayanki dubu ? Iya meya kawo wanan zancen ai taimakonshi akayi don an karbi dukiya a hannunsa haka kuma shi bai nuna komai don an karba ai kawu dauda yake fadan hakan ga iyan. Haka zakace tunda ka damka kana bushashanka dasu ai dole kace bai nuna bacin ransa ba ko tunda shi ba mutum bane ko ? To in baku sani ba ku sani duk da kuna ganin bai sauya ba dole abinda akai mashi ya bata mashi rai don haka kuyi kuka da kanku kada ku dora laifin ga yayan mutane da basuji ba basu gani ba . Aure kuma mukaddarine ko a ina matanka take sai kaje ka aurota don haka ina son ku fitar da idon ku akan yaran nan daga yau jafar dai yana zaune da matanshi lafiya inma wani abune kece dai dashi dauda gashi kune matsalan yaranku nan ba wasu ba. Kuka mama din ta kara dorawa sosai tana fadin meye zaisa aga laifinta shi kuma kawu yana yan kame kame nan dai basuji din zuwan ba don tsohuwar bata yarda da zancen da suka zo dashi ba din. Tace kowa ya fitar da idonsa kan yaran nan da matansu inba rashin hankali ba yaran nan meye matsalansu da auren yayan ku da kuke son sakasu gaba hakane ? Ke in kina da hankali yadda yaran nan keda tarbiya ai abin farinciki ne ya sameki ba wanan hakan da kikeyi a yanzu ba haka akan matan yayan ki. Sai yanzu na kara tabbatar da kinfi bukatan ganinsu cikin tashin hankali da matayen nasu sama