← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 169 OF 306

Sashe 169

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Motsin kwarai na kasayi a lokacin gashi dai naji fitansu amma jikina ya mutu jikina ya mutu na kasa motsin kwarai sai dubawa nakeyi ina aunawa me nayiwa mama dani da yar uwata a zaman mu da ita ? Saidai na kasa hango inda laifin namu yake gareta matsala dai daya shine zance ko yar uwata data dade a tare dasu bata taba kai korafin mijinta gun mama ba yadda sauran surukanta keyi . Haka kuma bata taba fadawa mama wani matsala daya shafi aurensu har asani manya su zauna dasu ayi sulhun hakan . To balleni da ko shekara banyi a cikin su ba ince mata me akan zama da danta me zan fada ya hadani dashi ko abokan zama da ba waje daya muke rayuwa ba balle kuma ai bai mun wani abinda zankai karanshi wajenta ba yadda take so. Ni dai a ganina wanan ne kawai matsalan amma bansan abinda ke boye ba a zuciyarta amma tsanan yayi yawa a zuciyar mama kan mu. Ban san hawaye na zuba min ba a idanu ina dai kwancene kawai naji muryanshi a kaina yana fadin kuka kuma Rahama meya sameki kike kuka haka kuma ? Dan yunkurawa nayi ina kokarn mikewa zaune saidai kukan yaki tsaya min naga yakai zaune gefena ya sake fadi cikin kallona meya sameki Rahama ? Cikin muryan kuka na daure na iya furta ba komai ina sheshekan kuka tare da kokarin kauda kaina a gefen da yake zaunen. Umm,humm Rahama idan kince kuka zaki dingayi kan mama zaki sha wahala sosai a rayuwan ki don inkin duba bake taiwa hakan ba ni tayiwa don nine zaune dake. Duk abinda takeyi bake takewa ba don nine take hakan kuma zata bari in sha Allahu ki dai kara hakkuri nasan kinayi baga mama ba harda kannena musanman Saratu nasan duk abinda ke gudana a tsakanin ku. Yanzu haka ina shirin zancen auren sune da zaran Allah ya dawo dani lafiya shine abinda nake son aiwatarwa ke nan a kansu. Ki tashi ki shirya zamu fitane yanzu dani dake jin hakan yasa na dan kalleshi ya gyada kai yace ehh akwai inda nake son mujena kafin na tafi tare dake. Naji hannusa cikin nawa yana dan murzawa alaman bani hakkuri yakeyi a zuciyarshi hakan da yai min sai nake jin sanyi a raina har ya mike yana kara fadin in tashi in shirya kafin ya fito ya fice daga dakin. Can falo nake jin muryanshi da iya suna hira ban tsaya saurarensu ba na shiga shiri simple makeup nayiwa fuskana na fito na samu bai falon saidai ban jima da fitowa ba sai gashi ya fito yake fadin kin fito ? Iya zamu dan fita yau har gidan malam Bala nake son mu leka nida amaryata don yayi min korafi ban kaita sun ganta ba sai labari yaji cewa na kara aure. Yakamata kam ku dinga zumunci don zumunci a kafa yake kuko yaran yanzu kun dauka wanan tangarahon ya wadatar maku kuma ba haka abin yake ba. Don baku da kamar malam bala a fadin garin nan kaf shi zaku diba ku tuna da mahaifin ki nakan so nayi wanan zancen sai in mata gashi yau Allah ya tunar dakai hakan Allah yayi albarka kaji ya kare tsare muna ku. Nuna mata tasan darajanka wajenshi don dama mu mata aka sani da zumunci ke kuma don Allah ki rike ki dinga tunatar dashi tunda shi din ba mai zama bane sosai garin kamar uba yake a wajensu bama kama ba ubanne ai. Tunda mahaifinsu dashi Allah kadai yasan tsakaninsu har mahaifinsu ya kwanta dama suna tare abinsu suna zumuncinsu. Sai mun dawo mukai masu har lokacin zuciyana bai sake ba muka shiga mota ya tayar nan yake fadin na rasa kalman da zanyi amfani dashi na baki hakkuri Rahama ? Naga har yanzu zuciyarki yana da kunci akan zancen nan mama fa matukar tana tare da kawu bamu taba gane kanta yadda ake so don kota dauko hanyar daidai kawu dulmiyan da ita zaiyi so banga abin tsayawa bata rai haka cikin zancen nan ba ? Na dan kalloshi ina sauke ajiyan zuciya da kyat bakina ya budu na iya fadin for god sake me nayiwa mama kome yar uwata tayi mata data tsane mu haka ? Naji yayi murmushi yana kallon hanya na sake fadin nasan tun zamana a gidan ban taba samun matsala da ita ba why a yanzu take nuna min hakan ? Saboda kin auri danta take ganin kunci amananta keda yan uwanki don kuci dukiyata shine kawai kada ki kara haka mama take tun muna yara bata son muyi abokin da zai dauke muna hankali da ita. Ko yaushe mama tafi son ta bude ido ta ganmu a gabanta baki ganin yadda take da yaran nan wanda bai san halinta ba sai yace ta shagwabasune amma halinta ke nan ita taji komai namu tasan duk wani motsin mu kuko ba hakan kuke ba keda Maria. Kawai dai tana ganin a yanzu kune kuke kokarin shiga tsakaninta damu yasa take son sakata a gaba a fahintar ta dai kamar kuna muna wayau ne ko wani abu maka mancin haka dai. Wani kwana naga yabi kafin ya sauka daga titi ya juya zancenshi da fadin kinga tsohon gidan mu da muka taso inda aka haifemu daga baya da mahaifinmu zai auri inna shine muka koma wancan unguwar da muke yanzu don nan din yayi mashi kadan da zama da mata hudu lokacin. Suwa ke gidan yanzu na tsunci bakina da tambaya yace su isa da lawal ke zaune ciki da iyalinsu su suka gaji gidan da akai rabon gadon mu. Suna ganin a lokacin sun kware mu sun samu gida ba irin rigimar da ba ayi ba karshe da muka hakkura sai gashi Allah yai muna sakaiya da mafificin hakan. Dama ance mai hakkuri yana cin riba a rayuwa hakkurinkune yaja maku hakan a yanzu ganin kofan gidab daya tsaya yasa nayi shiru ina bin gidan da kallo. Wani tsoho mai farin gemene zaune saman wani babban tarba da shimfida yana fitara da faifain kaba a hannunsa ya cire babban rigan dake jikinsa saboda zafi . Gashi ya kurawa motar mu idanu nasan yana son sheda mai fitowane yake fadin ga baba Bala can zafin nan ya dameshi sai fifita yakeyi ya samu sa,ida. Nakanso taimaka mashi wallahi sai kuma kamar abinda aka mantar dani sai in manta dashi gaba daya . Fita mukayi daga motan dagani har shi muka nufi wajen tsohon da saida muka matso kusa dashi sosai ya gane dan nasa. Murmushi yayi yana fadin yaro mai sunan manya ashe har yanzu dai halin naka yana nan kamar yadda nasanka a baya. Shima jafar murmushi yayi yana fadin baba anyi mun afuwa dan Allah bawai haka bane abubuwane suke shige mingaba yanzu. Tsohon da duk farin gemune a fuskanshi yake gyara zama yace nasani jafaru ina da labarin komai game daku duka ina tambayan lafiyan ku aiko yaushe gun yan uwanku. Tare muka zube kasa gabanshi muna gaidashi ya amsa yana fadin wanan ce amaryan taka ko don dai ba yargidan registara bace wanan ? Kuma ba wace mukaje kaduna daurin aurenta bace yace baba wanan yar Gembuce can yolan cameroon na aurota. Masha Allah ya fada yana kafeni da ido nayi kasa da kaina a cikin nauyinsa kafin naji yana fadin maddala abu yayi kyau sosai Allah ya bada zaman lafiya. Amarya sai hakkuri kin shigo gidan yawa don haka sai kin hada da hakkuri a zauna lafiya da kowa don Allah bisa ga amana sai kiga Allah na tare maki duk wani farmakin da magauta zasu kai maki a boye. Nagode baba na fada daga inda nake zaune ya maida kallonshi kan Jafar yana fadin man Jafar ya al,amura kuma naji duk abinda ke faruwa game da yan uwanka. Ina son ka kara zama namiji haka kuma lamarin iyayye musanman uwa gashi kuma ita ta rage maku a yanzu da kuke tare da ita don itace zaku kalla kuyi bugun gaba da ita koda bata raye balle tana raye to a kara da hakkuri a samu a rabu lafiya damu dai din don wani lokacin sai an hada dole da hakkuri ake cinma manufa irin yadda kakeyi a yanzu din. Duk daba wai naji taka maimain zancen bane saidai ina son jan hankalinka a nan daka kara daurewa dai ayi biyayyan nan dai da aka saba yi ko yaushe. Haka kema amarya don Allah ki bashi hadin kai ya samu ya aiwatar da manufansa na alheri da yakewa yan uwa da abokan arziki naji komaine a bakin Rukkaiya da Ai don su har gobe basu yadani ba suna min bayayya kamar yadda aka taso a cikinsa. Kwanaki sunzo gaidanine suke ban labarin abinda ke faru shine na nemi ganawa din dakai don in kara ja maka kunne akan hakan nasa kuma kazo min da ita wanan yarinyar na kara tausanta taci gaba da hakkurin da takeyi dai. Nan dai ya danyi nasihanshi muna mashi godiya kafin mu muke zuwa cikin gidan inda naga gidan babban gidane shima kamar na mahaifin su Jafar din don da gani anyi zamani a baya tsufa da karayan arzkine ya taso yanzu. Matan nasa duk sun tsufa ba kamar su inna da su mama dake da dan sauransu ba don basu cikin wahalane nasan irin nasu yasa hakan. Dakin uwargidan nasa mukayi masauki anan muka gaisa da kowa wanda Allah yaba ikon zuwa mu gaisa a gidan don wasu kan basu zo ba suna tsabgansu a lokacin. Wata dattijuwa mai dan tsayi take fadin Jafaru an kun manta damu yanzu koda yake Alh yace baka zama garin ashe har aure ka kara kuma duk bamu da labari sai daga baya. Naji yana fadin iya ayi hakkuri auren ne yazo a haka ba kowane yasan da zancen karin auren nawa ba don daga nemane don nisa iyayyenta sukai muna sauki aka daura auren daga nan. Kai masha Allah kaji mutanen arziki ba masu tunane ai nima nace dai akwai dalili da har Alh baiji ba ashe haka abin ya kasance. Ina kallon ikon Allah don yasan duk wani babba na gidan duk wanda yazo zasu tsaya su gaisa sosai dashi yayi masu alheti ashe
Chapter 169 · 0% Book details