← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 306

Sashe 67

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

fice daga wajensu babu kowa cikin matan nasa duk suna dakinsu a lokacin. Na samu yan matan mama sun tashi suna falo zaune su ukkun don yanzu zaman nafisa an karu a gidan ban dauki komai ba nake gayar dasu da kwana suka amsa min. Aina zata kina kwancene har yanzu nace a,a kunu na damawa mama nakai mata part din yaya J wai meya hadasu fada da safe haka ? Wallahi ban sani ba na fada Saarece ke tambayana sai naji tayi tsuki tana fadin ni wallahi halinsu ya fara fita min rai mutane kamar awakai sai surutu tsiya haka abu ba abu ba fada. Mutanen kine ai kunfi kusa gashi tun dawowan Saiba ta dora gaba dani don kawai na fadi gaskiya akan me zamu zauna kamar muna tsoronsu kullum. Ban fahinci zancen ta ba na danyi yan mintuna naji tanawa anty Nafisa bayani akan abinda ya hadasu fada ita din wanda nayi mamaki kwarai jin cewa akaina ake wanan abin. Bafulace da rikon gaba a take naji gaba daya na tsani wanan Saiba din don haka na mike ban karasa jin sauran maganganun da sukeyu ba na shige dakin iya na kwanta. Barci nayi don ba aikin da zanyi sai bayan azahar mama ta shigo tana tambayana daga dakin na amsa mata take fadin to yayan ku yace a kara dama masa irin kunun dazun din nan. Ai mama da zamu samu ganyen tsamiya fresh muyi amfani dashi da zaifi jin dadinsa sosai ace wanan garin kuma sabon dakane zaifi jin dadin shansa. Ni dubu Rahama yanzu ina zamu samu ganyen tsamiya a garin nan tsamiya da mutane kejin wahalan dibansa . Sai abin ya ban mamaki na tareta da fadin tsoro kuma mama niko hawa nake na debo to ai kuma kamar mutanen boye kuke Rahama in bashi ba yaya za ayi ku kwana dokan daji ku kadai. Kodana dama nakai yana zaune saman gado ya hade kai da gwiwa jikinsa saye da singlet fari na maza mai yan hannuwa iya damtse. Na samu matan tare dashi da iya na shigo dashi ina gaidasu na aje a gaban Asmau na fita ya kallota yana fadin ta zuba mai tana zubawa ta mika mashi ya bita da kallon mamaki kafin yace cikin karfin hali ba zaki iya fifita min ba ? Na dauka da zafi kake son shi ai ta fada tana mayar da kunun gefenta tama rasa yadda zata fifita kunun saida iya ta fada mata yadda zatayi. Yana sha yayi gyatsa ya koma ya mike zuwa falo saman dogon kujera hakan yasa suka fito daga dakin iya dai na zaune don mama sun fita da kawu a lokacin. Ganin basu da niyar gyara mashi dakin yasa yace da Asmau sai magariba ba a gyara min dakin ba ko ? Washegari dai suka tafi sokoto don yafi masu kusa jikin kuma gaskiya da dan dama sosai ya habu da kawu da mama suka tafi dashi sokoto din. Matansa an barsu a gida ba aje da kowa ba saboda fitinan da suka soma na wace zata yasa mama ta tafi ita aka barsu a gida. Asibitin sunyi aune aunensu basu gano komai a cikin kan nasa ba komai nasa yana normal hakan yasa dole washegari suka nufo gida. Nikan da yamma ina gyaran dakin iya da duk na gyara tulin komatsen dakin irin na tsofi ina wayan mopping dinsa lokaci lokaci sai dakin ya canza ma,ana a yanzu . Muryan Anty Nafisa naji tana fadin su mama sun dawo fa hakan yasa muka fito gaba dayan mu zuwa taron su yanayin mama kawai zaisa ki fahinci tana cikin tashin hankali lokacin. Gaba daya muka nufi part din ya J wanda yaya Habu ya rike mashi hannu zuwa cikin part din a hankali suke tafiya dashi a falo aka zauna. Kallo daya yaiwa part din ya kau da kai idan ba karya zai fada ba yana ganin tun tafiyansu ba a share falon nan ba. Duk da yana cikin halin ciwo tsabtan nan nasa yana nan mashi har yanzu gashi kuma Allah ya hadashi da kazaman mata a rayuwanshi. Wanan dawowan kan sun bazama wajen neman magani sosai idan kinga ya habu ya fita yacinsa sosai a yanzu don tashin hankalin da suke fuskanta na dan uwansa. Nikan sosai na mayar da hankalina wajen yar uwata da mahaifiyata zanyi girki a part dinsu in kwashe in kai masu sai iya da nake zubawa don mama ba zama takeyi ba. Wanan yasa koya kira yaji lafiyan matarshi take fada mai komai ina kawowa basai ya damu ba Allah yaba yaya J lafiya. Don sun kwasa sun tafi wani gari dashi a cikin Niger state nima kuma akwai kudi a wajena wanda shi ya J ya ban daya kaini Abuja. Ga kuma wanda mijin anty salma ya banda sallah da zan kuma dawo hakane ya kara ban kudi masu tsoka gidan daddy ma haka donshi banda wani matsala da kowa yanzu gidan balle in tsaya ina rabe rabe. Dakinsu kuma ban shiga ba tun wanan koran wullakancin da Saare tayi min na kora da hali abu daya shine na shiga na kwaso kayana dana bari a dakin. Na kwashi wanda na dawo dashi nakai duka can part din yar uwata na aje abina don haka na koma banda case dasu indai ya habu yana gari zan zauna nan wajen iya din amma kayana nacan wajesu. A can inda suka je wani kauyen agaye wajen wani banufe da wani ya turasu shine yayi masu bayanin jifansa akayi jifa kuma mai karfi koya mutu ko ya haukace ya koma bai moriya. Dalla dalla mutumin ya soma masu bayani yana fadin uwarsuce tayi sakaci har hakan ya faru ba kuma J ba kadai har duk diyanta ana kokarin ganin an raunanasu ga baki daya. Abin mu na mata abuna farko dayazowa mama a rai shine abokan zamanta mutumin yace ko daya suma gasu nan suna kallan nasu amma wanan ba irinsa bane. Don hadashi akayi da dodon tsafi dake shan jinin jikinsa don ma yana da tsarin ubangijine basu samu yadda suke so dashi ba ai. Ka tuna mutumin daka gaisa dashi ya kama maka hannu da sunan yana tayaka murna a yan kwanakin da suka wuce ? Shiru J din yayi yana tunane ko waye yace kadai tunana gashi nan baki gajere mai dan fadin kai da tumbi baida tsawo sosai dai haka dashi kafirine bai sallah bai chochi ? Still yana shiru yana tunane na dan lokaci don ya kasa gano ko waye wanan mutumin da akai masa kwatancensa saboda abokan hurdan nasa ai yawanci kafiraine. Hjy kinyi sakaci sosai akan yayan ki akwai matar data so fada maki gaskiya a baya amma baki mai da hankali ba kan hakan ? Itama mama nunawa tayi bata gane matar ba a daidai lokacin da J yace malam kwarai kuwa na tunashi tabbas anyi hakan bayan shan ruwa na fito na sayo abinda zanyi buda baki bakin wani shago na hadu da wani daya kira sunana ya nuna min sani ban sanshi ba amma shiya sanni. Yake min murna da cewa shiya dade da sanina ai muka sha hannu dashi sai malamin yace a lokacin ya shafama abin don da shirinsa ya fito dama. Yanzu malam yaya za ayi yace Allah shine maiyi mu saidai mu danyi namu dubarun da Allah ya hore muna ai. Yana ta jan tasbahan da yake aikinsa dashi kafin yayi murmushi yana fadin dewa ya,i wanan yarinyar da karanbani take saidai ba zasu iya komai da ita ba. Wace yarinya ke nan kawu ya tambayi mutumin yace gata nan dai a cikinku take wata mai dan tsayi da manyan idanuwa saura kiris ta kai ga nasara a shirinta. Amma baku bata daman hakan ba da zaku bata dama da anyi nasara koda baku zo nan ba saidai tana shakkun wani abu a zuciyarta kuma. Wacece ke nan malam gasu nan dai a tare daku su din alherine a wajenku kasan wani lokaci Allah kan muna wani baiwa amma bamu fahintar hakan sai muyi sakaci da abin. Amma shi nan gaba zai fahinci komai kai yake jijigawa yana fadin yarinyar tana da gwargwadon sani amma a yanzu tana tsoron aiki da hikimarta . Nafisace ko mama ta fada wata kila itace inji kawu ya fada daga gefenta sai mutumin ya dora da fadin hjy lalai ki samu wanan matar dake son maki bayani don tasan komai. Ya dai basu magani bayan surutan da yayi tayi a ciki harda zancen matan yaya din da abin ya kara daure masu kai suka maishi alheri yace dari biyu kawai zasu bashi sadaka in an samu lafiya su dawo su bashi abinda Allah ya hore a garesu suka fito suna mamakinshi.
Chapter 67 · 0% Book details