Sashe 287
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
karami. Amma kina fadan hakan iyayyensa sukaji ba zasuji dadi ba wallahi haba dai don Allah mama salima ke fadan hakan ga uwar tasu. Mummy wa zai tsaya saurarenta ma yaron da uncle ya bude baki ya kirashi da arziki sanadin haihuwanshi dukiyan uncle ya fito jiya kowa na murna da farin ciki ke kina kirawa yaro mugun abu ? Wai tsaya Aminu me kake fadine mama fa bata gane ba naji kamar kana son fada mata wani magana ita kuma bata gane hakan ba sai fada takeyi. Ai shine mummy jaki brain kega tsohuwar nan no school kayan uncle da suka bace a can kasan waje sune aka kirashin angani kowa na murna da farin ciki ita tana kirawa yaro tsiya. Gashi har anata zuwa mashi murna ana kiran yaro da arziki ke kuma kina nan kina zuba shirmen tsufa a gida baki gane ba kanin mu arzikine babba sanadinsa yazo muna da alheri. Aminun ta kurawa ido tana sauraren bayanin shi don a yanzu ta fahinci me yaron yake fada mata ga katobaran datayi game da yaron kala kala laifin uwarshi ya shafi dan jinjirin da baiji bai gani ba a duniya. Allahu Akbar kai Aminu kace min alherin Allah ya sauka muna a gida lalai wanan yaron arzikine tunda alheri ya baibayemu a yau. Salima ke fada cikin jin dadi tana nuna farinciki nisawa mai karfi mama tayi tana fadin lalai da ya zamo arziki kwana uku da haihuwanshi alheri yazowa mahaifinshi. Kai kuma duk kai min karya kam abuda bashi ba saina saba maka a gidan nan ta yaya abu irin haka zai samu amma mu bamu sani ba saikai zaka jiyo kazo fada muna shi. Shi yana fadin a,a ni banzo fada maki ba cewa nayi kanina arzkine don zuwamshi duniya alherine a garemu tunda ga irin hasken da muka gani a sanadinshi kai, arrrh mamata ta katseshi da fadan hakan. Salima kuma tace mama ai dole yace haka tunda yaga baki san alherin da ya samu ba amma ai tunda,zun yake zaune gidan nan bai fada ba. Tayi shiru na dan lokaci ta nisa take fadin abinda ban gane ba shine kudine masu yawa ya samu ko kuma wani aikine ya samu a kasan wajen ? Ban fada ba don ban sani ba nidai naga mutane suna zuwa kuma naji ana murna a gidanmu din nasan kuma alherine insha Allah. Ni baein tafi karki matsa min da tambaya ace kuma nice ba ruwana ban fadi komai ba tayi mai dakuwa ya fita yana dariya salima tasa mai kira ya dawo take fadin gida zaije ko wani waje a lokacin. Yake fada mata ba gida zaije ba tudun wada ya nufa yanzu mama ta aikeshi ya bada kudin abincin dabbobinta can ya nufa. Har yakai kofa yaji mama na fadin can kuma ka koma kaima ana kullawa dakai yanzu na fara tsoronka a rayuwata. Ya fita yana dariya baice da ita komai ba bai jima da fita ba yaya ya shigo ya samesu a waje suna magana mama na tambayan su abin arzikin meya samu Nusaiba tace bata da labari bayan wanan haihuwan wahalan da akai mashi. Haba dai haihuwar kuma itace wahala Asmau ta fada cikin nuna mamakin jin hakan a fili Nusaiban tace ban daiyi dake ba don Allah don ai nima bance kinyi dani ba kalman takice dai ke bukatan gyara gaskiya. Naga kowa na haihuwansa ai ba wanda aka aibantawa sai ita da babu ko ruwanta da kowa batama saka kanta a cikin duk abinda akeyi gidan nan ba. Kai ku rufa min baki don Allah ku wasu irin marasa hankaline wai baku da kishin juna saina abin banza ana maku kokari mijinku ya dawo hannun ku. Amma kuda baku raina abin fada nazo ina tambayan akan abinda da naji game da mijinku kun tsaya kuna min shirme yanzu . Yanzufa yaron nan Aminu yake fada min ta kwashe abinda sukayi da Aminu din ta fada masu abinda Aminun ya fada saida ta kai karshe Asmau tace gaskiyane dazun naji yana waya da yake cin abinci saidai ban kula dameya faru ba. To kunji abinda ke nan Saiba ta tareta da fadin yanzu shine bai iya fada muna ba koke mama saidai Aminu yaji a wajen wacan yarinyar yazo nan ya fada. Ke nan mu dai duk bamu da amfani yanzu idonsa gaba daya ya rufe akan wanan yarinyar ita kadai yake dauka a matsayin mace ke nan ? Har yana kiran danshi da arziki ko mu ke nan namu yayan ba arziki suke ba shiyasa bai damu dasu ba ko sai yanzune aka haifa mai dan gwal. To ni dai banga wani abu cikin zancen nan ba tunda abin nan in an samu kowa zai amfana dashi ai Asmau take fada ta juya zuwa kitchen duba girkinta lokacin ya shigo ya samu mama da saiba din a tsaye. Kallo daya yai masu ya fahinci wani abu na faruwa ya dai bude baki yana fadin sannu da gida mama lafiya dai na ganku haka tsaye. Ai dole ka ganmu nan Malam tunda har alheri na iya samunka ka boye muna saidai muji a wajen wace ka maryar mata yanzu ? Menene kuma akayi mama yake tambayanta cikin mamaki tace yanzun har wani abu zai iya samunka sai dai inji ga ahanun talla Malam ? Yaron nan Aminu yazo yake fada min wani zance dazun shine abin yake ban mamaki nake zance da matanka ko sun sani ? Meya fada maki kuma zancen wai wani aiki ko kaya yake fadi ni bam dai gane zamcen ba gaskiya don kasan haka yake kamar shu,umi wani lokaci. A,a mama yake dai gyara maki zance amma ai Aminu bai zo don ya fada maki maganan ba da kike irin maganganunkine fa yace shi kam kanninsa arziki aka haifan masu yake kora maki maganan salima ce data fito a cikin shiri ta samu suna zancen take fadin haka. Wai zancen kayana eeh anga kayana da akace sun bace wani abokina ya rike a wajensa dama kada su salwanta shine yanzu da yaji naji sauki ya fito min dasu ya kirani. Yanzu na gama shiri gobe nake son zuwa cika wasu bayanai don ina son inbi kayan idan angama sha,anin sunan nan da za ayi. Haba malam zancen nan baiyi ba badon yaron nan ba kilama ba zamuji ba ina zai fada kuwa mama tunda ba dole bane sai mun sani ai ba dai wa yanda yake son su sani sun sani ba. Ashe kin gane nufina wanda zasuyi min addua da fatan alheri suna fadawa don nasan ko banza suna farin ciki da samuna ko rashi. Zata fara masa haushi ya dakatar da ita da fadin kina sake fadin tak wajen sai kin bar gida bari na har abada kuwa in kuma kin dauka karya nakeyi ki tanka a yanzu din ? Shiru tayi tana mazurai da ido ta kasa magana ya juya ya dubi mama kamar zsiyi magana sai kuma ya fasa ya shige ciki zuwa dakinsa. Barshi kada ki tanka mashi don baya cikin hankalinsa yanzu komai yana iya faru dama haka akeso to ki kyaleshi. Salima ta kawar da zancen da fadin mama ni zan je kasuwa in dubu wani yadi da nakeso bata bata amsa ba ta juya ta tafi.