← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 306

Sashe 100

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanan dalilin karban maganin a hannun hardo don gaba dayansu sunsan cewa maganine mai tasiri wanda sunsan zai amfane su sosai nan gaba. Don akwai magani sahihi a wajen fulanin asali dama ance ba a hardon banza sai wanda yasan abinda ya taka yake zama hardon kewaye. Don haka suka dakata da tafiyan nasu aranan a nan ruggan suka kwana suna ganawa da hardo don kawai su mallaki maganin daga hardo . Wanda shida kansa hardon ya kwadaita masu din don ganin a yanzu yaran sun zamo a halinshi tunda suna auren yayansu. Yaga ya taimaka masu da abinda zasu kare kawunansu dashi daga magautansu wanda su basu san hakan ba sai kaura da kai da suke faman yi tare da makiyansu. Mussanman kawu dauda da abu yake cinsa a zuciya da dadewa game da diyan yar uwar tasa duk da bai fito fili yayiwa hardo bayanin akansu yake nema ba amma shi hardon ya san hakan ya boye mashine kawai . Kallon kawu din yake karr don hakane ya taya masu maganin da bakinsa da suka fito da zancen jifan da akewa ya jafar din kuma jifan yana cinmasa har yana kaishi kwance kamar ba za,ayi dashi ba. Hakan yasa irin hikimarsu ta manya ya fara kebewa da kawu yaji ta bakinsa inda ya bashi iya abinda zai iya bashi don shi kawu din cewa yayi a taimaka masa da wanda zai rika karban abu wajen wanda duk ya bukaci abin hannunsa an kuma bashi din. Saida kawu zai fita yace ya turo mashi Jafar yai wani magana dashi daya shafi zancen wajen aikinsa hakan yasa kawu din ya fadawa Jafar da ya shiga zai gana da hardo. Jafar din ya dan tsaya jim yana dauka akan zancen Rahamane kawu ya gana da hardo din sai bayan ya shigane yace aida sun shigo tare da Habu inda ya kira wani yaronsa ya nemo habu yazo shima. Bayan sun zaunane ya soma magana yana fadin ku saurareni kuji abinda zan fada maku don yanzu kun zama yayana tunda kuna auren jinina. Don abinda yasa na nemi ganawa daku shine kuna tafiya inwanku a waje don haka kowa ya taka ku lokaci daya zai sameku don ku din kamar yayan rokone. Suka dubi juna a tsakaninsu yace akwai wani abu da mata keyi yayin da Allah bai basu haihuwa ba sai su kasa hakuri suga kamar Allah ya manta dasune. Idan mace ta tsunci kanta cikin irin halin nan zata daga hankalinta har na tare da itama a lokacin kowa yace ya iya zata kai kanta gareshi neman haihuwa don ta samu taga jininta a duniya. Saidai kash irin hakan akwai hatsari a cikinsa indai ba malamaine suka bada wanan sa,an ta wani is,simin sani da baiwan da Allah yai masu daga Al,kur ani mai,girma ba. Mafi yawan mata suna halaka zurian su ta wanan hanyan zuwa wajen malaman tsubbu da yan bori dake aiki da aljannu da sunan samun sa,a su wa yan nan diyan sune yayan roko da nake nufi. Wani irin zufane ya tartsowa habu a gaban goshinsa take kuma mafalkinsa na baya ya fado masa a rai har hankalinsa na neman gushewa a garesa lokaci guda. Muryan hardo ya dawo dashi daidai hardo dake fadin irin hakan uwarku tayi shine kuma a yanzu yake shafan dan uwanka kai habu harkai baka tsira ba saidai saukinka gudane haduwan auren ka da maria shine hasken taurarinta ya hasko naka din. Zama ya gyara yana fadin nasani baba nasan hakan tun ban hadu da maria ba don a ranan da zan taho cameroon wata mace ta fada min kusan hakan a dunkule. Nan ya kwashe komai har da zuwa neman matan da sukayi da mama dubu da kuma mafalkin da yayi daga baya har yazo zancen bada maganin da nayiwa ya jafar din. Sai lokacin Jafar da yayi suman zaune ya iya budan baki yana kallon dan uwan nasa yace yanzu habu kasan da hakan kaki fada min komai na tashi tsaye inata wahala ? Baisan komai ba iya abinda aka sanar mashi ke nan amma shi wanan kawun naku yasani yasan komai a game daku saidai nasa manufan akanku ya hana ya fadawa uwarku gaskiya don amfanin kansa da yakeyi daku yanzu. Sanda dake gefensa ya dako ya aje a gefensa yace kunga haka hakan kuke tsakaninku dashi ba zaku iya komai ba saida izinin wanan mutumin. Saidai ku a wajen ku hakan biyayyane a gareshi wanda ba haka bane tsananin karfa ce dake tsakanin ku dashi yanzu dai idan Allah ya maida ku gida lafiya ku san yadda kukayi da mahaifiyar ku takai wanan sadakan da aka umurce ta dayi shine maslahan ku dasu haka shima abinda yayi a kanku din duk zai karye. Kofa habu ya duba kamar kawu din na tsaye yana sauraronsu yaji Hardo din yace wane shi nan ai tuni na hadashi da abinda zai sakashi kwana ba zai taba jin abinda muke fada ba a yanzu. Ku saki jikinku kuyi maganan da duk kuke son yi a wajen nan kun dai san baku tambayeni ba nice naga dacewan in fada maku gaskiyan abinda ke a duhu gareku. Shiru wajen yayi kafin habu din ya fara kawar dashirun da fadin baba na rasa me yake damuna haka kudi zasu shigo amma ban iya abin kwarai dasu zasu lalace min h,,,,,,,, Wanan sherin wanan kawun nakune da matarsa dake dorasa a hakan aiba halinsa bane sherin matane matarsa ce matsalan taku tana hassadan da za ace uwarku ta fita sa,an haihuwa. Jin zancen hardo sukeyi a wani bakon yanayi da basu taba zato ba a zukatansu wai kawune da wanan halin hardon ne ke magana yake fadin. Aishi baffa tsoron Anini yakeyi shine ya saka ya jata a jiki fiye da yar uwarta don da tana wajen shi har yanzu na tabbatarda sai Anini ta karya duk wani shirinsa akansu. Nan ya kwashe tarihin mu kaf yabasu da irin yadda baffa yaci kurwan dan uwansa mahaifinmu a cewarsu ya gwada na yaran saidai tasu kurwan duk a boye take don duk aka haifesu sai na boye inwarsu. Shiko dan uwansa ya samu nasaran samun damansane a cikin abin sha da magariba sa,an mugun duk wani mugunta da magariba mugu ke aiwatar dashi don a lokacin mumunai suna gagawan saduwa ne da ubangijinsu sun sake komai a lokacin. Taurarin Anini yafi duk taurarinsu karfi shi baffan nasa ya sani yau ko katsa ta diba taba mutum da sunan magani sai karbu ga mutum balle wanan dafa,in mai karfi. Sai daga bayane suka fahinci wace hardo din yake kira da Anini sunana na gado da suke kirana dashi a ruggar tamu ke nan. Zaka samu alheri sosai dan samari zaka ji dadin zabinka sosai koma ince haka dukkan ku auren ku da yaran nan alherine gareku babba. Saidai a hada da hakkuri yana fada ya dauko wani dan kullin magani a cikin jakkarshi ya banye kullin yake fadin habu ya miko mashi hannunsa ya dinga murza mashi abin a tafin hannunsa yana fadin da bafullace kake sai kowa yasan garakanka a nahiyar ku amma yanzu kai bansan abinda ka dosa ba. Hakan yasa Habu sakin murmushi yana ajiyan zuciya hardo na daure maganin Jafar yace nifa hardo saida hardon yayi murmushi yace wai ta Allah ta isheka bari dai kagani kofafinka zasu bude nan ba da jimawa ba da zaran kun hade da matar taka ai. Ai wanan baiwan taka yaja maka haduwa da hadadrun da kake fuskanta saidai Allah na karekane don ibadan da kake dashi hakama mahaifiyar ku. Duk da ana bata karfa kullum amma bata yarda tayi sakaci da ibadanta ba wanan ne ubangiji yake kwato ku har zancen dan kabilan ibon daya jefeshi a kafa ya kumbure saida hardo ya fada masu da zancen kawu dayasa suka kara shiga natsuwansu akanshi. Kusan dai raba dare sukayi a wajen hardo din koda suka koma masauki sun samu kawu yana ta sharan barci ba kwanciya sukayi ba alwala suka dora kowansu ya tayar da nafila. Washegari dasu akai sallah asuba a ruggan an idar jama,a zasu watse hardo ke fadin akwai daurin aure a kofan gidanshi da karfe bakwai na safiya. Gabadaya kowa yayi mamaki dajin sanarwan hardo din inda suka fito da mamakin hakan sam basu kawo cewa sune da auren ba don gidan hardo gidan jama,ane. Hakan yasa suka dakata da tafiyan don kara gasu hardo din sai da akazo daurin aure ne abin ya basu mamaki da hardo ke fadin kawu ya matso ya amsawa dansa auren Anini din. Sukuma sune waliyan amarya su kawo sadaki dubu hamshin daga garesu kowansu yayi mamakin hardo nan danan habu ya kirgo dubu dari ya mika a matsayin sadakin hardo yace baiki ba amma jafar ya bayar da kansa yake so don shine mai aure. Ya saka hannu ga aljihunsa ya ciro dauri biyu na yan dubu guda ya aje a gaban hardo din ka shiga hidimar daurin aure kamar yadda sharia ya gada. Kamar ance habu ya dago kai ya kalli kawu yayi mamakin yanayin daya hango kawu a cikinsa ya dan radawa J din daya dubi yanayin kawu din a lokacin. Anyi lafiya an watse sai lokacin sukaje godiya wajen hardo nan yake fada masu cewa idan sun koma sun saka ranan tarewa sai ummah ta bugo waya mata suje ayi bukin acan wajenta kaduna tunda tana kusa dasu shidai yayi nasa na uba a nan. Haka suka bar rugga cikin jin dadin halarcin hardo garesu suka nufo gida cike da farin cikin sa,ar tafiyan tasu zuwa ruggan mu. Har suka iso gida ba wanda suka fadawa ga abindake faruwa tsaraban da suka dawo dashine irin na wajen mu yasa Yanda tambayan ga kaya kamar na wajen mu dai ? Yana daga kwance yake fadin daga can suke ai har can din muke hardo ya hadomu dasu akawo maku. Yanzu yaya Habu zaku rugga shine baka fada min na bada sako zuwa wajen hardo ba saidai naji kunje kawai kun dawo hannu sake ? Waya fada maki hannu sake mukaje maria kinsan koni bankai abuba J zaikai don bai saba zuwa waje haka hannu sake ba,shi. Tashiga juya abin da mamaki saidai babu daman magana don haka ta kyaleshi ta shiga kawar da
Chapter 100 · 0% Book details