Sashe 128
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaune yake falin yaya Ai itama a nan cikin tudun wada gidanta yake saidai akwai dan nisa da family house dinsu din daga gidan daya sauke iya daketa bashi hakkuri akan rayuwa da kuma iyayye da yan uwa ya nufo gidan yaya Ai din. Da murnanta ta rasa ina zata sakashi a lokacin don jin dadin yau dan uwanta yazo wajenta abinda basuyi mata ke nan kamar yan uwana na gudunta take gani saboda talaucin da Allah ya dora masune. Don ita yaya Ai din mijinta dadtijone sosai kila kuma gami da talaucine yasashi tsofa a zamanin kurciyarsa ya danyi tashen kudi saidai irin na rufin asiri din nan za ace. A haka kuma iftila,i ya sauka,mashi a hanyansa na zuwa fatauci lokacin ya hadu da barayi suka karbe duk abin hannunsa tun lokacin yake fama da rayuwa shi da iyalinsa. Kasane bana hadin kai ba aure abu zai samu dan uwa maimakon a samu yan uwansa yan kasuwa su tallafawa mutum a dagashi sai dai a sakawa mutum ido har sai yakai kasa waras kamar jira ake hakan ya sameshi dama. Na tabbatar da mata Allah ya umurta da kasuwanci kamar maza za a ga hadin kai da taimakon juna a tsakanin su🙋. Sai ya kasance yan uwa ma sam basu damu da ita ba da iyalinta don bata da komai a rayuwanta saidai duk sallah nasan idan an fita ana zuwa gidanta boyan Allah ga son jama,a saita rasa ina taka saka mutum idan yazo wajenta. Yanzuma da J din yazo sai godiya take masa daga ita har mijinta da kishiyarta kamar wanda sukaga yazo masu da wani abu a lokacin duk da hannu sake suka ganshi amma sunji dadin hakan sosai a lokacin. Ta kakabe wajen da zai zauna tukun a dakin nata da babu komai a cikinsa sai dan gadon katako mai dungu da wani tsohon zani gado shimfide duk ya kode. Gefe guda wani tsohon kujerane da tsufanshi har yasa katakonshi ya fito fili ya zazzage an tula raga don ya danyi taushi. Nan aka gyara mashi ya zauna suka fara gaisawa da yar uwar nasa dake mashi sannu da zuwa a lokacin take tambayan dazun nake jin kana gari a wajen malam yake fada mun yaji ance kaine kabada gyaran massalaci kofan gidan mu . Yace shekaran jiya na shigo da dare jiya kuma abubuwa sun min yawa yasa ban samu zuwa nagai dake da gajiyan buki ba. Haba dai aiyiwa kaine ya kara mata da godiya take fadin Jafaru aini ka karrama a zancen nan da har ka tuna dani baka kyamace niba ka turo ayi komai a gidana akwai abinda yafi haka dadi a wajena. Wanan ai yafi dan uwa yazo ya baka kudi indai ana zumunci haka da zumunci bai taba lalacewa ai a duniya amma ina su isa gamu gari guda a waje daya sai inyi shekaru ban saka kowansu a idona ba garin nan kuma ana raye inaga yaya in sun taso kuma kaga ba zumunci ke nan ai a tsakanin su idan sun taso. Hakkuri ya bata yana fadan in sha Allahu za a gyara yaranta da suka dawo daga islamiya suka shigo su uku mata maza biyarne ta haifa a gidan. Wanan yasa tsufan wahala ya taso mata saika rantse batayi primary ba balle secondary idan ka ganta lokacinsu sune yan mata masu tashe a gari duniya ke nan yanzu saboda talauci da yara ta koma haka abin tausayi. Ya Allah ka duba muna wanan zamani cikon tausayinka ya Allah ka sakawa duk wata uwa da alheri kasa albarka ga zuria wa yanda suka kauce kuma ga tsufa ga zuria Allah ka shirya munasu badon halinsu ba ya Allah mun tuba kaiwa kasan mu da musulman kasan mu agajin wahalan rayuwan da ake ciki Amin ya Allahu. Yaya Ai me malam keyi yanzune na ganshi a gida a wanan lokacin ko har ya taso daga kasuwan ne ko yake tambayanta kan mijinta din ? Haba ta kama tana fadin malam kace Jafaru ai malam yaushe rabonshi da kasuwa yau kusan kimanin shekaru goma sha,ai tun wanan abin daya faru dashi. Da yana dan zagaya abokan hurdanshi na kasuwa don samun abinda mukaci a gidan har yakai sun gaji dashi sun fara kyamatarshi yazo ya daina fita yanzu dai sai abinda Allah ya kawo muna idan rabon mu ya ratsa. Innalillahi yake nanatawa a zuciyarshi har yakai fada a fili ya gyara zama yace yanzu kina nufin haka kuke zaune bai sana,an komai ? Haka muke Jafaru aiko nayi mamaki da baka san hakan ba duk zuwan nan da kukeyi ai kuna ganinsa gidan nan ko ? Na dauka dai don sallah ne kinsan nafi zuwa nan da sallah wani lokacin a,a wallahi halin da muke ciki kenan ai shekara da shekaru kai dai Jafaru. Allah ya sauwaka ya fada yarta datazo a karshe tana gaudashi zata kai shekara goma sha uku da haihuwa yake fadin wana takice tace tawa ce ita autata take biwa takwaran iya ke nan ai Habiba. A,a,a ashe kin samu mai sunan nan kema tace ina da ita ai gata nan yace ina ga ni zan dauketa kuwa ko ita ko wanan autan naki ko inbawa Amaryata rikon ta su zauna tare idan zaku ban don banson zamanta ita kadai don ni ba mai zama a garin bane sosai wanan yasa yanzun nan naji hakan ya fado min a rai. Amma abinda ya kawoni nan shine ina son dake da anty Rakiya kuzo wanan gidana da amaryana take ku dauki kayan tausan gaban wa yan nan kukai masu duk da nasan na daiyine kawai amma sai kuma yai shiru bai karasa fadin abinda yayi niyar fadi ba din. Sun dan jima ganin magariba daya gabato ya mike suka fito bayan ya aje mata kudi yan dari biyar biyar ya samu kishiyar ta tana bakin murhu ya ciro dubu ashirin ya bata ta bata ai kuwa suka shiga godiya. A waje ya samu malam sule na masa gadin motarshi saboda yaran unguwar sun dan jima dashi kafin ya fada mai makasudin zuwansa din gidan. Yaji dadin hakan don daga mijin har matan mutanene masu son zumunci saidai babu karfin yin hakan a yanzu dole yasa suka lafa. Shima dubu hamsin ya bashi ya barsu cike da tausayinsu a cikin ransa masalacin kofan gidansu da mahaifinsu ya gina da yake raye nan yayi sallah magariba tare da jama,an unguwar. Ana idar da sallah ya sulale ya fita bai zo gidana ba saida ya koma gidan daya sauke iya ya dauko ta zuwa gida haka kuma yana son yai ma iyalinsa saida safe duk da ba dadin rai ya samu ga hakan ba . Bai shiga part din iyan ba kodaya fito ya ja motarshi ya bar gidan don Nusaiba bata ko amsa sallamashi ba daya shigo. Sauri yakeyi yaje yaga halin da yar mutane take ciki donshi bai tsatsaya ba ya juya zuwa gidan amma duk damuwa akan halin daya samu yaya Ai su ya daga mashi hankali. Wa yan nan sune abin taimako a duniya shine amfanin samu a cikin dangi ina amfanin kana dashi dan uwanka na cikin irin wanan rayuwan kuma ? Tun fitanshi na shiga kitchen na dafa ruwan dumi na saka a flask na juye saura naje bandaki dashi naji dadin tsarki da ruwan dumin sosai don haka na kai har magariba ina gasa kaina da ruwan dumi hakan da nayi yasa na samu walwala na iya yin girkin dare dan abinda zamuci da dare din. Ko kafin ya dawo nayi tuwon semo da miyar busassan kubewa don shine gareni lokacin amma nayi amfani da nama dake shake a cikin freezer kitchen din. Inda na dan cika tattasai da albasa da dab attah kadan sai kayan yaji dana barbada don kamshin miyan yabada dan dano nama kuma na dafeshi sosai tunda miyar yaukine nayi ga kamshin daddawa dake tashi a ciki na hada komai na shiga wanka a gurguje na dade zaune a ruwan dumi kafin na fito nayi wanka sabulu da soso na dauro alwala na fito na tayar da sallah ina idarwa na mike kada jikina ya bushe sanyi ya sauka min na nufi mirro na gyara jikina sallah isha nayi na saka wani dogon rigan cotton mai mayafi rigan anyishi mai sharp na saka hula kalan kayan sky colour na dan yafa gyalen shi a wuyana. Nasan don inda yake a lokacin ya kusa dawowa gida hakan yasa na kara feshe ko ina da air freshener take gidan ya dauki kamshin dadi ban shafa turare a jikina saidai roll on a arm dina zuwa wuya don zufa. Karan bude get din gidan dake bada wani sauti saboda nauyinsa yasa na gane ya dawo a lokacin. Yana shigowa direct dakina ya nufo ina kwance nayi rigingine saman gado da littafi a hannuna da nake dubawa ya shigo dakin da sallama. Na dan dago kai ina mashi sannu da zuwa na sauke kafana daga saman gadon don in mike in karbi ledan dake hannusa don malaman mu Lubbunah ta fada muna hakan waje biyu yake da amfani karban kaya a hannun miji. Na farko ladan da zaki samu daga Allah don girmama mijin da kikayi da aure sai na biyu kuma hakan na saka wani irn kauna a tsakanin miji da mata na ban girma donshi ta horemu dayin hakan komai kankanta abu muyi saurin karba daga hannuwan mazajen mu. Mu,sanman mazan mu na hausa dake amfani da addini da al,ada lokaci guda hakan ya zama addini da dabi,an malam bahaushe. Ya gane me zanyi don idona na kan ledan hakan yasa da sauri yace No ki zauna abinki ba wani abu bane ai a ciki kazace sai fresh milk na kawo maki kisha. Ban dai zauna din ba na mike nazo na karba ina gasheshi da dawowa jikinsa ya hada da nawa ya matse waje daya yana fadin yaya jikin naki yanzu ? Naji sauki na fada a cikin kunya dajin nauyinsa don irin yadda ya hade jikin mu a waje daya din kamar yana neman wani abu a jikin nawa. Kin tabbatar ya kara fada nayi dan murmushi kawai ban bashi amsa ba yake fadin hankalina ya tashi sosai dazun Rahama iam sorry banyi hakan don kaina