← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 248 OF 306

Sashe 248

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai daga baya na fahinci daddy daya fada masu cewa banda lafiya don haka sai naji sauki saudi ce ke fada min ai gata yayi min da fadin hakan . Yanzu kinga ko kin koma gidansu bake ba sauran wanan aiyukan da suka bar maki ke kadai dole za a canza tsari yadda ya dace ko kuma ya dawo naki gidan kamar yadda akeyi a baya tunda ya samu lafiyan fita a yanzu. Saidai wanan kaunar tashi kamar har yanzu tana da sauran ja don yanayinta ya nuna bata saduda ba ? Bam tsamani cewa zasuje wancan gidan dayar matarsa yada sukaiwa yarinyar nan caaa a kai ita kuma munafukace dai ta karshe watau ? Kinsan ya rabu da ita meye na kiranta a waya kina fada mata sirin gidanku koda yake uwarma da alama goyon bayanta takeyi yadda takw ba diyan nata amsa. Murmushi nayi kawai bansan me zance a zancen ba tunda gaskiyar ke nan ta fada na rasa gane mama ko wace irin uwace ita ? Da bata iya tsawatawa Saratu wanan halin yan wutan da takeyi na hadin hasumi gashi ta sani ba abu mai kyau suke aikatawa ba ita da Nusaiba amma sai ta tsare kada ayi mata fada. Saidai wani lokacine ita kan dan tsawata mata idan ta wuce mata gona da iri a lamarin ta koshi ba ko yaushe ba sai can ba a rasa ba zakiji tana tsawata mata din. Nidai har barci ya daukeni tana zuba bansan tashinta a dakin ba saida na falkone na ganni ni kadai a daki ina barci hakan yasa na tashi na kashe tv na koma daki na kwanta duk da dare baiyi ba sosai a lokacin . Sai bayan kamar kwana biyune da zuwansu ina zaune ina shan iska a waje da yamma saiga ummah da kudi a hannunya ta zauna a kusa dani tana fadin. Ungo wanan daddy yace a baki koda akwai abinda zaki saya a nan kafin ki koma zaiwa antyku Nuratu magana tazo ku fita tare da ita . Kudin nabi da idanu ban karba ina mamaki nace ummah me zan saya kuma komai yaya J yana sayo muna a can ? Kingani ai munsan da hakan shiya muketa baki hakkuri don shi bai maki komai ba uwarsace da kanninsa sukai maki laifi bashi ba ? Don haka ba zaki hada duk dashi kice kina fushi ba ko ranan har suka koma baki kirashi kinji yadda suka isa baiyi fushi ba ya kira kuma kikaki dagawa ? Da sauri na dago na dan dubeta na maida kao kasa na sada tacigaba da fadin banga dalilin da zaki hada dashi kina fushi haka ba ? Su dai da suka tabaki ai dasu zakiyi bashi ba ummah idan banyi hakan ba ba zai dauki mataki ba wata rana kuma har sai kuji cewa sun kai ga taba jikina tunda suna da niyar hakan dama a manufarsu ? Kinga kuwa da ace sunsan bai kaunarki da yanzu sukai ga abinda suke so don ba wanda yayi tsamanin cewa zaiki kai har wanan lokacin a gidan ? Yau gashi har Allah ubangiji ya kawo rabo a tsakanin ku abinda basu taba zaton zai faru ba ke nan don ance suna fadi wai saidai kiyi zaman wahala kina jinyarsa din da kikeyi a kare ga hakan. Kwatsam saiga shigan cikin nan na jikinki koshi bai isheki godiya ga Allah ba a sanadin cikin ne ai ita dayar kishiyar taki ta fita tabar gidan ko ? Don Yanda na fadin sosai suka girgiza lokacin da baiyanan wanan cikin na jikinki don haka dole ki daure ki koma dakinki a yanzu koyi goyon cikin nan a gidan ubansa yadda basu kaunar gani din suga Allah ya fisu. Don Allah Rahama ki koma kiyi hakkuri a dakinki ki dubi mijinki dake fama da kansa don Allah ko sun kiraki da yar wahala kinfisu morewa Rahama don ladanki yana ga Allah. Allah ya gani mu munsan da zuciya daya kike zaune da Jafar kosu sun sani abu daine na hassada akan mutum kawai sukeyi. Don ni uwarsu na kasa gane alkiblanta har yanzu na rashin kaunarku da yayanta da batayi ban taba ganin uwar da bata da tunane irin wanan matar ba a rayuwana. Tanayine don zugin da dan uwata ke mata a kanmu ummah tanayin ne kuma don kawai an sakata tayi muna hakan kada mu mamaye masu gida kamar yadda dan uwanta ya fada. Dan murmushin yake ummah din tayi tana fadin kaiya ta makaro wallahi ai tunda ta haifa sai an mora din yadda bata so. Yanzu dai ki karbi kudin nan ki shirya din gobe ku fita da antyn naki don jibi zasu mai dake dakinki in sha Allahu. Jibi kuma ummah na tambaya da sauri ta mike tana fadin me zaki zauna nan kiyi Rahama ga mijinki can yana bukatanki a kusa dake. Ta juya ta tafi nabi kudin dake hannuna da kallo zasu kai dari biyu kila da dan kai don nauyinsu da naji a hannuna din. Koda na shiga daki na samu wayata dake makale a caji tana ta rigin na duba shine a kan layi yake kirana har yayi min three mis called a lokacin ina waje. Kamar zan share sai kuma na daga da sallama ya amsa yake fadin ina ta kira baki picking ba tun dazun dama nace in tura habibane ta gyara maki daki ? Ai Key din suna wajena na bashi amsa da hakan yace saida nayi tunanen hakan saidai falon da sauran dakuna ko nacewa Yazid a kawo maki kayan abinci fresh a kwashe wa yan nan tunda sun dade . Nagode kawai na fada a darare yake fadin please Rahama kiyi hakkuri kada kice baki dawowa yanzu rayuwana tana bukatanki a kusa dani wallahi. Da sauri nace dashi aiba ni kadai bane bayan haka akwai yan uwa kaida kake cikin gatanka ga kowa naka a kusa zakace kana cikin wani hali a yanzu ? Haka dai kikace idan kika wuce satin ban Allah saidai in dawo kaduna daddy ya bamu daki a nan mu tare baki dayan mu. Kit na kashe layin cikin takaicinsa don ni dai shine ya jefani a wanan halin da ya barni yadda muke da shike nan yanzu muna zaman mu lafiya da kowa a gida yaje ya kawo zancen aure a tsakanin mu daya jawo min bakin jini a cikinsu yanzu. Zama nayi ina tagumi a bakin gado tunanen abinda zan koma in tarar yanzu kuma a gidan nakeyi duk da nasha alwashin cewa ba zan kara kulasu ba duk abinda zasuyi min nasan wanan karyane muje dai din don dole wata rana in kula. Nusaiba kuwa daga ranan da suka shigo kaduna din zuwa wanan ranan tashiga tashin hankalin dayafi a girka duk iya shige shigenta bukata bai biya ba yadda malamta suke mata karyan zai faru din. Don gashi har kaduna suka shigo amma ba wanda ya kula da lamarinta har waya da tayi da mama ta fahinci maman batayi na,am da hakan ba. Koda basu zo donta ba ai zasu shigo su duba yarsu dake tare da ita amma kememe tayi ta jiransu sai sakon Saratu data samu cewa sunma kusa shiga zaria ai. Hakan yasa ta kasa hakkuri ta dinga tura masu sakon bakar magana a cikin bacin rai tana kara dasa kiyayarta a zuciyarsu wanda ta dauka hakan gwanintane a wajenta ai. Abinda nake son mata su kulla a nan shine matukar kina shuka gaskiya cikin lamarin ki ubangij Allah yana tare dake a ko wani hali saidai idan kece kika raina abinda kika gani din a kanki. Ban taba zato ko tsamanin cewa zasu shigo haka kamar yadda daddy ya bukaci ganinsu ba amma sai gashi Allah yayi ikonshi dole sunzo din har gaban su ummah suna bada hakkuri. Washegari anty Nuratu tazo gidan ta daukeni farko wajen wata mata muka tafi yar maiduguri ina dai kallonta a raina nace nu dake da mummy a abuja ana gwada min wanan abin ? Saidai lokacin da matar ta fara fitar da kayanta na fahinci kowa da nasa sabin ashe ita anty Nuratu din ta biya da kudinta muka fito daga gida. Muna mota take fadin ni naga no need asai maki wasu sutura a yanzu haka zaifi kyau bayan kin haihu muyi wanan shirin . Nima ban ra,ayin wasu sutura wanda aka dinka a baya suna nan cushe ta juyo tana fadin wallahi ki dingawa mijinki kwaliya kanwata. Kada ki yarda ki saje da wa yan nan matar nasa marasa kan gado ga miji tsab tsab aje aga matansa kamar rainon kauye ba kyau gani . Ni tun a nan na raina masu wayau wallahi suna ganin don yana kwance yana jinya ba zaiji dadi bane idan sun gyara jikinsu ? Krdai abinda nake so dake ysnzu Rahama shine kada ki yarda ku zama daya dasu don Allah ki bambanta kanki dasu ta wajen kwalliya abinci da gyaran gida. You are lucky ma ba a gida daya kuke rayuwa da kazantannan ba don wallahi dazaki sha wuya ga hakan don haka ya kasance ya zamo yana mararin dawowa gareki ko yaushe wanan ne kishin zamani ai ba zama ana hauka ba. Haka kuma zancen yan uwansa daddy ya fada min komai kada ki kara damuwa da lamarin su don Allah shi dan uwa marfin jallone basuyi saida shi haka kuma shi bayayi saida yan uwansa. Ki dai dauki matakin zama da kowa don Allah kada ki kara bada daman da zasu rainaki kuma ki daina cacan baki dasu haka ko yaushe. Sufa yanzu takaicinki sukeyi sister suna ganin kece star din gidan duk wani shawaransa dake yakeyi so kinga dole suyi bakin ciki dake haka ? Yaushe zaki wuce servuce dinki jn haka yasa na gyara zama ina nsawa nace zuwa next month ne in sha Allahu. To ki mayar da hankali don Allah Rahama ki dage sosai ki zamo wata a cikin family dinku don Allah kece Allah ya zabo kila da zaki tallafi kowa. Ki daina yawan shiga cikinsu sai un wani abu mai muhinmanci ya faru ke leka kada ki jima ki fito sosai zaki dauki girmanki fa Rahama . Ita wanan kanwar tashi ba komai bane illa zallan hassadanki da takeyi tunda
Chapter 248 · 0% Book details