← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 277 OF 306

Sashe 277

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read

fadi ni yanzu na gane malaman nan macutane wallahi don suci kudinta sai su kakaro karya su sharawa mutum don hankalinsa ya tashi a banza. Haka dai akai komai har daurin aure ba tare da sun samu yadda suke so ba din salima kuma tunda ta fita har ranan buki bata leko part din ba tana wajen iya zaune har yan kai amarya suka wuce da amarya bata fito ba. Anje dasu yaya barakha da maman tudu sai mama hafsatu matar kawu wace zuwanta din yaso ya jawo matsala tunda taje wajen jere don kawu yace amayarsane zata kai amarya. Su yaya suka tsaya sukace da inna hafsatu za a dole ya kyale ya bari ta tafi mutum biyar dai suka je raka amarya dakinta a ranan. Duk daba gida daya muke ba saida baji shakat da tafiyan nata don nasa an rage wani annoba a yanzu matar yazid ce ta fara magana ta soma fadin. Wai an rage wani kaya a nan wanan matar batayi min ita sam kamar ba ciki daya suka fito da yan uwanta ba ta fita daban a cikinsu komai nata baida kyau wallahi. Muna wajen iya har yamma nidai koda aka fito wai aje a sallami mama kin zuwa nayi na zauna nan a barandan iya har suka fito muka fice daga gidan.
Chapter 277 · 0% Book details