Sashe 44
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
da ya samu bawa mukkadarine nata kaddaran haihuwan ke nan yazo mata a hakan kuna magana kamar baku taunawa wani zubin duk wanda kika gani a nan ba dadin rai ya kawoshi wurin nan ba asibiti fa akace ba gida ba ? Shiru tayi don tasan abin ya taba zuciyar mama din don ba wanan karon suka fara tsegumi kan matan Habu din da mama din ba. Suna fadan mama tafi son matar Habu dasu tana nuna banbanci a tsakaninsu ta fifita matar Habu alhalin duk wani moriya a gidan mijinsune . Taba wace suka gulman da ita sakon da take kyautata zaton yakai masu da cewa ta fifita din don ance ka kyautatawa wanda yasan darajan ka. Kuma da sauki tunda ba habu ta fifita akan jafar ba ai idan sune aida sauki suyi mata yadda matar Habu din ke mata idan basu ga canji a wajenta ba. Wanan yasa suka kama bakinsu don ta fadawa yar sakon cewa su shiga hankalinsu don lokaci guda zata iya fyacesu gaba daya a gidan kirsis take jira ga hakan. Don saita sa ya j ya sakesu ta aura mashi masu hankalin ya zauna dasu tunda basu iya cin arziki ba su kuma su tambaya suji ita a ratuwanta bata gaji tsiya ba ko jafar din da arzikinta yake barazana. Aiko da J din yaji yai masu tsiya sosai lokacin har yana barazan sakinsu run wanan lokacin suka shiga hankalinsu da mama din ta samu lafiya dasu . Sai a yan kwanakin ma suke dan ganin fuskanta idan tazo gidan wanan yasa a yanzuma sukai gum kamar ruwa yaci su a dakin. Tare da likita suka shigo dakin hakan yasa muka fice waje sai mama aka bari a wajen nan muka zauna saman babban tabarma a wajen . Mai hali dai baya barin halinsa akace don ko a nan gulman wata mace mai tsohon ciki sukeyi ina mamakin yadda halaiyansu ya kasance a hakan. Banga abin tsegumi ba a nan duk da yake basu irin hakan ya sama ba a yanzu dole su mayar da abin kishin tsakar gida su da yar uwata da suke ganin ta shiga rigan arzikin mijinsu a yanzu. Don ni a zatona shine mai dukiyan gaba daya don bansan cewa dukiyan yan uwansa kaf da suka gada yana hannunsa ba lokacin. Sun dan jima ya fito yana fafin muje ko kafin ya juya wajen iya yana fadin to iya ni yau zanyi tafiya fa zan koma port,harcurt wajen sana,ata . Ayya Jafaru zaka koma yau ke nan sai kuma yaushe eeh to iya saidai kun ganni yanzu kam amma insha Allah kafin azumi zan dawo na dan fara azumi a nan din. Hakan na da kyau Allah ya tsare ya kare ta fada gabanta ya gurfana yana fadin to muka hannun ki mana a cikin hijjab dinta ya dunkula mata kudi sai murmushi iyan ta sake a fuskanta tashiga mashi sabon addu,a kuma. Ya mike tsaye yana kallon kannesa yana fadin to ku yaya za ayi nifa zan tafi yau din nan ana nemana a can . To yaya zancen kudin da nayi maka fa Saare ta fada yace ban manta ba saratun mama ba kince sai next mont bane saiki tuna min ko ina can din in turo maki. Ya dago ya kalli Salima yace yan mata nasan kedai na shan ice cream ne ko ko yanzu kin dainane tayi murmushi tana fadin ban daina ba yaya yanzu kan harda na powder da jan baki . Ya nunata yana fadin see you nine zan baki kudin jan baki ina saurayin ki dan karya ta kebe baki zakice wata karamar yarinyace kudi ya mika masu . Kamar zai wuce sai kuma ya kallo inda yake yana fadin nakan manta da sunanta fa Ramaah ko ka kirata da Rahama wai dama sunanta ke nan aka sauya da wanan din. Ke kuma kudin me zan baki ya fada yana kallona murmushi nayi ina fadin nagode yaya yace shike nan kin hutar dani ? To ku kunji yadda akeyi ba kamar ki ba Saare da kullum kedai a baki kudi nakan rasa me kikeyi da kudi haka wallahi yana magana yana kokarin cusa hannunsa a aljihunsa na gefe daya. Sweet J muje mana kasa mun taso kuma ka tsayar damu haka a rana ya juyo ya dan kalleta hakan bai hana ya fasa abinda yakeyi din ba Salima naga ta kebe baki data fadi hakan tana magana kasa kasa tace akgunguma duk ranta ya baci ana bamu kudi. Nice kusa da ita a zaune ninaji hakan data fada ya miko min kudin yana fadin kin gani ko kin fisu sa,a ke yan dubu dubu kika samu. Na karba da hannu bibiyu ina godiya rakasu mukayi har bakin mota suka shiga ko anan ma din saida ya tsaya da kannesa suka dan taba barkwanci a tsakaninsu suko duk sun sha toka a motan . Nice na fara juyawa ganin ya tayar da motan tare da mamakin irin zama da naga sunyi a tafiya dukkansu suna zaune a bayan motar shi kadaine a gaba da yake jan motar. Suka tafi su kuma suka dawo inda nake zaune da tsohuwar kakan tasu dake kiciniyar boye kudinta cikin lalitarta dake manne a jikinta. Kai yaya ho daga shi dai sai matansa shike nan sunyiwa kansu tsiya babu wace zata shiga gaban mota ta zauna tare dashi don jidalinsu din. Ai maganinsu ke nan yan iska masu fitinan tsiya kawai haka kawai akan shiga mota su kama dabe a gaban mutane sun zubarwa mutane da mutunci. Ni na rasa yadda mutum irin yaya jafar mai hakkuri da kirki yake iya zama da wa yan nan matan da basu son suga wani komu nan mun rabeshi. Jifa yanzu kudin nan da Saiba taga zaibawa Ramaah shine ta kasa hakkuri take fadin wai yazo su wuce ya shanyasu a rana wai ita yar iska mai wayau banza. Ai shima ya gane me take nufi bakiga ya fita batunta ba ko kwanaki daya dawo tafiya ta aikawa part din ya Habu da tsaraba suka ki saida ya dawo ya diba da kansa bayan yai masu cin mutunci yabani na kai masu. Tsam na mike na nufi wajen mahaifiyar mu dake can dan nisa damu a zaune cikin damuwa nasan ba komai bane sai halin data samu yar uwata a cikine ya daga mata hankali. Ina isa naji salima na fadin ummah kin zauna kinyi shiru kamar baki wajen tayi murmushi tana gyara mayafin jikinta da ya rufe mata jiki lif har kasa. Idan kinga Ummah duk da wahalan da take ciki zaki rantse kice ba itace ta haife mu ba sai kice ita din yar muce ba mahaifiya ba. A cikin yare take tambayana da shi wanan din yayan Abu ne ko na amsa da ehh shine babban yayansu namiji amma suna da yaya mace tana aure a wani gari ita. Ayyo suna ko da kama sosai da Abu din saidai haske dashi ya dan dara Abu din dashi nace shi Habu din kebiwa shima dan mamane su kuma su Salima da Saare kanne sune duk uwarsu daya.