← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 298 OF 306

Sashe 298

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe biyar na yamma ta shigo garin zaria a by pass ta sauka ta nemi shatan mashin zuwa gida kai tsaye tana bin ko ina da kallo. Kofan gida ta sauka bayan ta gyara mayafin kanta da kyau don kada a shedata don ita kanta tasan ba daidai take ba balle wani ya ganta a hakan . Dakatar da mai mashin din tace tana zuwa bayan ta dan shiga da kayanta ciki kadan tafiya take tana bin gidan ko ina da kallo indai ba idonta ke mata karya ba a yanzu sai tace gidan nasu a yakuce yake kamar babu kowa dake zama a cikinsa yanzu. Daba don sautin karan tv dake aiki shiyan Yazid da shine fara isa ba da taja da baya ta koma waje don sai tace gidan kaf babu mai zama cikinsa yanzu. Cikin sanyi jiki ta karasa kofansu ta dan buga tanayi tana waigen kayanta data baro a kofa don kada mai mashin din ya gudu dashi a tunanen ta uwar zargi. Bugun kofan da mama dubu taje ga kuma muryan saratu dake kiran sunanta da mama yasata mikewa da sauri zuwa kofan ta bude. Itace dai saratu din ce a tsaye tana ganin uwar take fadin mama akwai dubu biyu in biya dan mashin kudinsa bata samu magana ba illa juyawa da tayi ciki don dauko kudin ta mika mata. Jun maganan su yasa salima bude kofan part dinsu ta leko tana fadin umm,ummm saratu dama zaki zone bamu sani ba tana magana ta karaso wajen ta kama mata kayan data jawo niki niki zuwa ciki. Ban karya ba tun safe wallahi ta fada ta nufi kitchen din mama da salima suka dubi juna suna mamaki akwai abinci shi ta debo tare da ruwa ta nufo falon. Ta zauna ta fara ci duk sun kafeta da ido yadda take aika cibi a bakinta kamar mayunwaciya sai lokacin mama ta nisa ta soma fadin wai sararu lafiya kuwa ta dauki kofin ruwan data zuba tana fadin ba dai kun gani ba mama ku godewa Allah dana samu kaina gida a yau. Ta duka taci gaba da cin abincinta can kuma saiji duka ta fashe da kuka mai karfi irin na tashin hankali din nan da sauri salima ke fadi ke kuma daga magana sai kuka ai saiki dagawa mutane hankalisu kuma ? Ni take son ta dagawa hankali bayan wanan da nike ciki yanzu ace mutum baida kwanciyan hankali akan yayansa duk kokarin da nakeyi kanku karshe irin abinda zan gani ke nan kuma ? Da wani zanji da zancen yan uwanki da suka juya min baya suka bi matayesu koda naki dana yar uwarki barakha ko salima dake gabana ba aure ? Mama ai gara salima da bata da auren hankalinta da nake a kwance yake nida suna nayi aurene fa tunda naje ba kwanciyan hankali kullum cikin tashin hankali da fargaba nike wallahi . Tana kuka ta shiga labarta masu irin abindake faruwa ta basu labari kaf na irin zaman da takeyi gidan aurenta da abubuwan daya faru da ita a can din. Salima ta nisa tana fadin wai wanan lamari dame yayi kama don Allah sai kace wa yanda akaiwa baki kamar mu kadaine a duniya yau a tashi da wanan gobe wancan za a tashi dashi kuma ? Ga wanan sakaran taki barin gida sai fitina takeyiwa mutane kuma yaya yace bai mayar da itakuma ta zauna tana hauka akan sai ta koma sabon gida itama. Ta saci kallon uwar tana fadin kici abinci kije kinyi wanka ki kwanta ki huta in kinyi sallah har su yaya su dawo dan basu garin nan gaba dayansu ba kowa garin nan suna wajen tafiya. Salima kona kwanta ban iya barci yanzu sai inga kamar za a zo min da sabon fitina kuma wallahi na gaji niba zan koma gidan nan ba kuma . Ki daiyi hakkuri yanzu ki huta kafin su dawo asan abinyi akai amma don Allah ki daina wanan kuka haka kina daga muna hankali in kina wanan kukan ?. Kallon salima din mama tayi don tafita karfin hali a lokacin don ita jikinta ya gama mutuwa da zancen tana zaune tana ganin kamar a mafalki take gani saratu di a hakan. Hankalin salima duk ya tashi auren har yaushe akayishi da yar uwarta zata koma haka ba dadin gani da badon tasan waye saratu ba da sai tace gaskiya hakan ba zai faru da ita ba. Sun zauna shiru falon kafin saratu ta kawar da shirun da tambayan naga part din su yaya kamar ba kowa mana ? Sun kwashe sun bar gidan nan ai suna sabon gidansu daya gina sabon gida yaushe ya gina gida kuma bayan tafiyana ? Waya sanar mashi ance gidan ya jima ashe yana aikinsa bai fadawa kowa ba sai yanzu da zasu tare shida iyalinsa shidasu suka tare ke nan ita Rahama har yanzu tana gidanta daban koya hadasune ? Haba dai tana nata gida Asmau kuma tana sabon gida saiba fa shiru salima din tayi bata bata amsa ba ta kawar da kai hakan yasa ta juya ta dubi mahaifiyarsu. Saiba fa mama bada ita aka tare bane a gidan mama din ta nisa kafin tace jiya ta tafi ta koma gidansu kaduna jiyan . Gidansu kuma a to tunda tace bata da mutunci bata iya bin abu sannu ba sai tayi tujara ai taga karshen tujara a wajenshi kuwa. Nifa ban gane ba don ta kwana biyu bamuyi waya da ita ba ranan ma na kirata waya na ringing bata dauka ba nace ko bata kusa da wayan ne ? Ta dauka tunda kowa laifin ya shafa a wajenta yanzu rashin mutuncinta ya karanto mata karya kuwa a wanan lokacin don cikinta yayi. Kema banga dalilin kiranta ba kina fada mata sirin ki tana baradaki a gari tana yawo da sunanki kan cewa bakiyi dacen gidan aure ba ? Mama ta juyo a hasale tana fadin ita data dace ai halinta yasa ta zauna a gidan daula ko banda dai sherin kishiyoyi ai ita Saratu ba a ji tayi cin mutunci ba. Wai mama meyasa ta koma kaduna kuma ana zancen tarewa sabon gida ko sunyi fada da yayane kuma yace ta tafi ? Salima ta mike tsaye tana fadin kin damu da ita ke nan matar da tabi kowa tana fada masu duk abinda kike kiranta kina labarta mata a waya zaki tsaya jin meya faru ? Ko ba,a fada ba aikin sani rabuwa sukayi mana dashi zata kawo mai iskanci ya nuna daidai yake da ita ya sallameta ta kuma koma ganin laifin mamanki a karshe ta hadasu ta zage tsula har tana fadin mama ta tanka in bata shigo ta murjeta ba a falon nan. Yau ga yar iska mama din zata duka ai ga mama din kiji a bakinta in,ni baki yarda da zancena ji da kanki don Allah fita batun wata mara mutunci can . Mama wai don Allah da gaske salima takeyi haka akayi ta dago tana fadin Saratu don Allah kiji da abinda ke gabab ki bar min zancen wanan yarinyar mara kan gado. Eeh lalai kuwa Saiba takai yar iska mamace zata zaga har da fasin ta yi magana ta murjeta duk halarcin da mama tayi mata a gidan nan. Aita manta hakan yanzu tunda dan mama yafi karfin mama tace don yabar yarda da ana labawa ga mama ana tauye mashi hakkinsa . Nikun isheni da rashin hankalin ku don Allah mama ta fada a tsawace garesu shigowan iya yasa duk sukai shiru a dakin. Wa nake gani nan iyan ta fada ta amsa da nine iya ko baki shedani bane kema zamani ke amarya har yaushe aka kaiki da zaki zo gida ? Jiya ta amsa ma iyan tana daure fuska don ba shiri sam tsakaninsu wai yaushe tazone iyan ta juya wajen salima tana tambatanta kafin ta mayar da idonta kan kayanta dake gefe daya aje. Iya dazun nan ta shigo mama taba iyab amsa takai zaune tana fadin lafiya dai ko sai saratun ta mike taja bag dinta zuwa daki tabar mama na mayarwa iyan da zuwanta din. Kwance yake yana barci a dakin matarshi ta biyu yaji sallaman uwargidanshi a kofan dakin ya mike zaune yana fadin shigo mana fati ta karasa shigowa daga ciki tana gaisheshi cikin hade rai wanan dabi,antane matukar ba dakinta yake ba yana wani dakin har in ta fahinci ya kwana da mace zata wuni tana hade mashi fuska a gidan . Bashi ba har yara a wunin ba zasu gane kanta ba lokacin gata haihuwansu takwas amma yana bala,in shakkunta ta riga data shige mai gaba sai abinda tace za ayi a gidanshi. Hakan yasa sauran matan da suka san irin rayuwan kishinsu sukaci maganin zama da ita suke binta sauda kafa don a zauna lafiya. Amma ita saratu taki hakan ta dubeshi tana fadin ina ganin fa amaryanka kamar bata kwana gidan nan ba jiya ? Da sauri ya dubeta yace bata kwana ba sai wanan matar da yake dakinta tace ta kwana mana don ko dazun da zan shiga bandaki na ganta har mun gaisa. To zan mata karya kika nufi ko mai dakinta dai a rufe take inko ta kwana ina take yanzu shiru matar tayi kada a dora mata laifin daba nata ba a kai. Ya mike tsaye yana fasin ina zata amma koni naga haske a dakinta da zanje sallah maganan jamilata sai dai inda sahena tabbar gidan ya mike zai fita ta hararoshi tana fadin in kuma zaka ? Ya koma ya zauna da sauri yana fadin wai da in dubuta ko tana gidan su ladi don can naga ta lakanci shiga kwanan ga ? Na tura ance batazo ba yasa nacema bata nan ta juya ta fita sai lokacin ya samu ya mike tsaye yana zura riganshi dake rataye. Dama naji tana waya tana fadin ita gida zata bata iyawa sai ya hauta da fada da kinkaji shina baki fadamin ba ai dauri ki hwada min in sani. Ya fita yaga dakin kargame da kwado ya nufi wajen gidab nasu ya tsaya idon matan dake zaune waje suna aiyukansu duk a kanshi bai damu da hakan ba wuce wajen gidan yana dube dube. Allah ya gani
Chapter 298 · 0% Book details