← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 219 OF 306

Sashe 219

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yazid shima ya shigo ya sameshi suka hade nan wajen iya da mama din suna fada muna daki da Yanda alokacin tana faman ban hakkuri. Habu sai fadi yake ban taba gani kojin irin wanan abin ba su lokaci da sukai cikin su wayayi kokarin sheganta masu cikin su duk da kowa yasan abunda take zuwa yi kaduna lokacin. Haba haba kada ka biye masu a zama daya mana kome mutum yayi don kansa ai ba za a biye mata a zama daya ba . To tabari yarinyar nan dai bata shiga zancen ta don haka itama ina son tafita zancen ta tun muna sheda juna tsakanina dasu a gidan nan . Ranan naga haukan kannan miji a gaban kowa akai tujara har saiba na fadin ashe su ake cuta da aka hansu kwana daki dashi ansan abinda aka kulla ayi yasa aka kakabesu da karfi da yaji karshe dai yazid yai tsaye yace. Wallahi bata kwana gidan idan kuma mama tace sai takwana sai ya kusa kasheta a ranan hakan da tajine yasa ta fice daga part din. Don daga inda yaya yake kwance shima bakinsa bai mutu ba a ranan fadi yake matatace nayi abinda nake gani daidaine a gareni anyi din kije kiyi duk abinda zakiyi. Yana magana kamar zai daga daga inda yake kwancen ya karaso gareta ganin da mama tayi auren saiba zai iya mutuwa yasa ta izata zuwa wajen. Nan Yazid ya dage kan lalai sai tabar gidan a ranan inba haka ba sai ya halaka ta dole da yamman nan ta nade tabar gidan don tdoron yadda taga yana kokarin cin mata a lokacin. Bani ba har yar uwata tayi koka sosai da tsohon cikinta don a yanzu tana cikin watan haihuwantane ummah muka iya kira muka sanar da ita abinda ake ciki tace tana zuwa. Ashe daddy ta kira abuja ta fada masu saiga kiran mummy tana fadin mu shirya gobe zasu zo su tafi damu duka idan basu son mune suda suka haifemu sun san darajan mu ai. Hakan ne ya faru don kamar hadin baki saiga iyayyeb Saiba sun dawo da ita suna bada hakkuri ana cikin wanan zaman su daddy da mummy suka iso tare da anty Salma. Sai ummah da mijinta da suka shigo suma a tasu motar suka hade duka a gidan gaba daya iya tace yau dubu kinkai ga yadda kike so ke nan Don ba sassauci a wajensu daddy yace dagani har Yanda tafiya zasuyi damu tunda uwar mazanmu ta nuna bata kaunarmu to abashi diyanshi ba zai barsu inda ba a kaunarsu ba. Nan mama ta fara kame kame tana salati tana fadin ita itace za ace tana nuna halin kyara da hattara a garemu don bata kaunar mu ita saidai a dauki alhakinta ga hakan. Daddy da mummy sun kafe akan sufa tafiya zasuyi damu don amana muke a wajensu don haka ba zasu saka ido ana tozarta nu suna kallo ba gara kowa ya kama gabanshi. Banda kuka ba abinda nakeyi a lokacin dole aka shiga ban hakkuri ana tausan su daddy din da suka hakikance lalai tafiya zasuyi damu. Iya ta soma magana da fadin to dubu yaukan sunanki ya cika dubu don dubu ya cika dake saidai ki sani yau ana daukan yaran nan su koma hannun iyayyen su ke kuma zaki rasa dan ki guda tunda baki yarda da kaddara ba a zuciyar ki. Dama irin ranan nan nake maki gudu ranan da hakkurin yaran nan da iyayyensu zai kare a kanki ranan da zasu fito fili haka su nuna maki sun fahinci me kike nufi dasu. Ace ka zauna baka da tunane kai maganan yara kake amfani dashi duk abinda yaran nan suka fada akan abokan zamansu ya zaunu a wajen ji dubu baki bincike sai dai ki goyi bayansu. Narasa me yaran nan suka tare maki haka dubu duk wani kyautatawa da akw bukata a wajen yaro yaran nan suna maki shi a gidan nan amma baki ganin hakan ke abinda nake maki gudu ke nan a kullum dubu ? Yanzu dai Alh kuyi hakkuri kubar yaran nan a daku nan su don Allah tunda kowa ya gane kuskurenshi cikin zancen nan a taru ayi hakkuri don Allah dama haka zama ya gada wani lokaci. Daddy yace ai yayi hakkuri amma tafiya damu ya zama wajibi a garesa tunda har aka nunawa yarsa haka shiba zai lamunci hakan ba gara dai ya dauke diyansa ya tafi dasu. Mijin ummah na fadin kwarai tunda abu yakai har ana kokarin shegantawa yarinya cikin jikinta ai gara kawai ayi hakkuri aje a zubar da cikin kowa ya kama gabansa. Jam jam Alh kana dattijo bai kamata ka fadi hakan a bakinka ba ai kai mai bada hakkurine cikin nan kasai ya ishi mu nan ishara don wani hikimace ta ubangiji ga hakan. Ace cikin nan bai samu ba saida yaron nan ya shiga irin halin nan haka kadai ya ishi bawa ya kara yarda da lamarin ubangiji ai don Allah Alh kuyi hakkuri da zancen tafiyan nan ku bar yaran nan a daku nan su zaifi. Yunkurin da yaya Jafar yayi don ya sauko zuwa wajen daddy ya bashi hakkuri sai akai rashin sa,a ya fado saman gadon saida yan uwansa suka tare shi hakan yasa hankalin kowa a falon ya koma kansu kuma . Ihu mama tasa tana fadin a ceceta don Allah kada ta rasa jafar don suman da yayi a lokacin mahaifin Saiba yace to Nusaiba kin gani kinga inda fitinan kishi ya kaiki yau ? Rashin hakkurin ki ya jawo mijin ju zai rasa ransa saboda bakin ciki ke yanzu wani dadi kikaji ga hakan don Allah ? Ki tunafa mutumin nan Allah ke talkafe damu shine tallafe damu ta sanadinsa muke a cikin gidan da muke a yanzu shine cin mu da shan mu amma sha shancun ki ya hana ki natsu ki kwantar mashi da hankalin gidansa. Komai ace nusaiba ce silla ke wani riba kika samu ga hakan wai haba dai baba ai wanan kyautatawan tsakanin miji da matanw ba kuma sai ka fada a nan ba tunda kowansu yanayiwa ai ? Wallahi a,a don ni baiyiwa iyayyena hakan ba Asmau take fadan hakan cikin jin haushin abinda taji din a lokacin don ranta ya baci matuka. Ke yi shiru nan sulhu akeyi mama tudu ta fadawa Asmau din daddy yace tana da right din da zatayi maganan ta yadda bai maki ba haka muma sai bai muna ba a bangaren yata kinga ashe yarsu itace da riban shiya take fadan wani yazo ya rabeshi shima yaci arzikin nasa .. Habu da yazid suka fito daga dakin suke fasin ya samu barci don Allah daddy kuyi hakkuri yanzu dai ai taji abinda take son ji haka kuma kowa yasan cikin nan da ubansa tunda ga matakin da maicikin akaga ya sauka wajen sheganta masa cikin sa din. Magana ta gaskiya duk ranan data kara wani magana akan acikin jikin yarinyar nan ta kwana da sanin zamata a gidan nan yazo karshe. Nan dai aka samu aka lakashi daddu yayi hakkuri bayan ya kafa hujja akan duk ranan da wani dan uwansu ko wata mace ta fadi wani maganan daba daidai ba kotuce zata rabshi da maishi a rayuwansa
Chapter 219 · 0% Book details