← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 296 OF 306

Sashe 296

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

matar na kawu kawai ba mutumiyar arziki bace duk ita ta jawo wanan abin sam da ba haka kawu yake ba ai daga bayane ya koma hakan. Zan fada maki wani magana yau don irin hakan nake son na kakkabe Nusaiba tun yanzu a rayuwana. Sam ban ra,ayin maiyin shirka mai hada wanin Allah da Allah yana ganin shine daidai na tsani wanan rayuwan tun ina karami salima na tsani masu irin halin bin boka da malami sai gashi na tsunci Nusaiba dumu dumu da wanan rayuwan. Zan iya hakkuri da halinsu in zauna dasu hakana amma banda zuwa wurun boka ko malam gashi har takai ga koyawa Saratu wanan rayuwan . Yana da wuya idan ka fara ka bari donshi kikaga gaba daya a yanzu dana samu kaina ban iya taimakawa kawu ko kadan . Wayan da aka kirashi yasa ya fita daga falon ta nisa tana kallona tana fadin Rahama na suma a zaune ashe yaya yasan komai da sukeyi saiya nuna kamar bai sani ba ? Tun dai gabanin auren nan da saratu zatayi sune har zuwa katsina wurin malamai subbahanallahi na fada tace wallahi. Gashi sunje din kuma abubuwa sunki dadi ga auren kullum cikin bugo waya take tana kuka ashe gidan yawane matan shi hudu kuma dukka zube suke a gidan gado tare da iyayyenshi da kowa nasa duk a babban gida kamar ace ku matan yaya dasu marian ki da hauwan yaya yazid da matan su yaya Auwal duka gaba daya. Kirji na buga irin na bam mamaki din nan tace ai bashi ba duk kinga yawansu girkinsu to a hade wai yake waje daya ake girki gaba daya har kowa gidan. Ance yara cakwal ba iyaka kowa kuma a wanan tukunyar zaici nace innalillahi ai zaka halaka ato ai tagani nan da aka auroki aiba abinda bata fada ba akanki lokacin. Yanzu ita gashi ta fada ga wanda yafi naki sau dubu hankali ya tashi saiban da take tayawa kuma yanzu itace ke gulmanta ranan ina jin tana fadawa wata kawarta tana dariya . Shigowan yayan nata baisa ta fasa maganan da takeyi din ba har saida ta kare yace dama idan kace hassada ka iya sai Allah ya barka da dabaranka. Ni tacewa Rahama da kurciyarta kwadayi yasa ta aureni tsoho ita tana kamar Rahama bata ga kwadayin da zai kaita auren mai mata ba. Duk ta dauka duk abinda da take fada banji irin abinda take fada ba ai shiyasa yanzu na sakawa yar iska ido ai . Allah bai hana min abinda zan kama mata haya ba a garin sokoto yanzu amma na kyale yar iska ta dandana barnanta taji. Haka mama nason muyi zancen da ita amma sai in zame mata sam ban yarda an zauna dani ayi wani magana ba game da ita. Ko shekaran jiya tunda safe ta kira mama tana kuka injinsu nayi kamar banji ba lokacin dana fada mata gaskiya ai wucewa tayi tana fushi dani wai kazafi ake mashi ba gaskiya suka fada ba. Su yaya Ai ne zasuyi mata kazafi ko mama hafsatu mama ta goyi bayanta sukaci min mutunci a lokacin. Ni zancesu ma ya hana in tambayi yan sabon gida wai wayaga Asmau cikin sabon gida Allah yasa dai ta daina kazantar nan nata . Yanzu fa kika gama maganar wata na munafuncin halin ya bita ke kuma gashi zaki dora na anty Asmau tun ba a daga ba ? Ta kwashe da dariya tana fadin bari Rahama abinsune sai addu,a don ban taba ganin kazaman mata irin Asmau da Nusaiba ba. Lokacin mama da dan sauranta ai ko sunyi abinci bata iyaci saboda kazantarsu amma yanzu ni banma ko kula ko tana ci tunda ko yaushe Nusaiba suna tare tunda Saratu ta tafi. Ke dai bari ana abu a duniyan nan wallahi yanzu ai zan je naga gidan da yaya barmu da mamakinshi ace har an gina gida kowa bai sani ba ?. Habu ya sani don tare na fara ginawa da nashi dana yazid lokacin daya samu matsalan nan yasa ya karasa nashi da kanshi amma tare aka soma aikin gaba daya. Dama yaya kai ka ginawa yaya habu gida ashe amma ban taba jin wani na wanan maganan ba sai yau daka fada to kibarshi nan inda kikaji. Shima yazid insha Allahu zasu koma a nasu kwanan nan kafin yacigana tace to yaya gidan mu fa yace nakune mana salima dake da mama da barakha da saratu ku hudu za a barma shi. Binshi tayi da kallo ba ita kadai ba harni dake tunane da fulanin mu ke fadin dan uwa MURFIN JALLONE daya baiyi saida dayan komai bacin zumunci kuwa ga mutum wani abin don dole saida dan uwanka na jini. Wanan kalman tun bayan komawan mu wajen baffan mu nake jinsa idan gorinsa ya tashi a kanmu zaice shi dan uwan mahaufinmune na jini don haka mun zamo mashi marfin jallo a yanzu don ba yadda zaiyi damu . Tare suka fita don kiran da akayi mashi yace gashi tafe suka tafi suka barni da mamaki da yawa a zuciyana har na rasa wani zan kama a ciki don abubuwan mamaki naji a dan zaman nan da mukayi lokacin. Daki nashigo tun bayan fitansu muka kwanta da Amir nake wanan tunanen ranan da yake nasan mama bata gida barcina nayi sai bibane tayi muna dahuwan da zamuci. Ban fito ba sai wajajen biyu da rabi ukku saura nafito daga daki koshi kukan Amir ne ya tayar dani sam ban iya kiran sunan gatsau don sunane mai tsada a ga kowa yasa na laoerl akawa yaron Amir. Koda suka bar gidan can suka nufa su yaya Auwalne sukazo dukkamsu ganin sabon gidan don kowa bai san da zancen ginan nasa ba bayan habu shi kuma ba magana yakeyi ba haka yake dunkum a cikin yan uwa ba wani sakewa sosai dashi. Sun zagaya ko ina sun duba suka dawo falo suka zauna duk da gidan bai gama jin kayan alatu ba amma ya hadu sosai yayi kyau ga abinda aka saka a lokacin don ginan kawai abin kallone . Yaya Auwal ya dubi salima yana fadin ke kira min Asmau ta mike zuwa kiranta din bara jima ba sai gata ta sake gaidasu a matsayinsu na yannin miji da kuma yanninta na cikin unguwa da aka taso a waje daya. Ya nuna mata waje yana fadin zauna magana zanyi dake a gaban kowa yaji ta samu wuri ta zauna a tsarge ya soma fadin to Asmau nasa a kirakine a matsayina na yayanki tako wani bangare. Munzo munga waje masha Allah abu yayi kyau sosai Allah yasa afi haka a rayuwa muna fatan hakan akoda yaushe don Jafar mutumne da kowani mahuluki dake tare dashi zai mashi wanan fatan. To amma ke kuma ina rokonki da ki natsu ki gyara halin nan naki da kowa ya ahedeki dashi na kazanta da son jikin banza. Duk da Jafar yayi hakkuri yana kuma kanyi kuma bai taba kawo karanki kan ya gaza dake ba kema haka to ina son ki sani ba zamu saka ido kina cutar da dan uwan mu ba don son jikinki. Jafar namune kema tamuce a yanzu don koba aure akwai hakkin makwabtaka daya zama zumunci tsakanin gidan mu da gidanku a yanzu donshi nake gargadin ki wallahi in har baki canza halinki ba Asmau zan shayar dake mamaki sosai wallahi. Ganin kallon da yan uwan ke mashi yace wallahi kwarai da gaske don sai tabar gidan nan wallahi kuma in saka Jafar auro mata biyu a lokaci daya su maye ko ina yadda ba zata dawo gidan nan ba. Meye ranan kazanta don Allah kun tauye yaro ba dama ya dawo gidansa ya huta wari da ganin takaici ya hanashi zama don tsaban sakarcin tsiya kawai yayi mata tas a gaban kowa tana hawayen munafunci. Bashi ba duk wanda yazo gidan korafin da yake mata ke nan ko a gabanshine kuwa za aja mata kunne akan kazantansu. Ni dau bance zanje ba tunda batazo nawa gidan ba idan ita watace mai lissafi ya kamata ace da muka dawo asibiti ko daga gidansu tazo ta duba jikina ai ? Amma sai ta share wanan yasa nima na sharesu ban kula da inje in gano ba ga kuma kummalon mata da yake cina a zuciya duk da gidana baida wurin da ya kasa amma wanan halin matane ko yayane sai naji wanan abin koda kadan ne kuwa. Ita kuma saiba da tambaya da yake mutane da munafunci saida ta samu wanda ya nuna mata gidan ta tafi ya riga dayayiwa maigadinshi magana don yasan zata aikata hakan yace koda wata tazo ya nuna mashi photonta yace kada a bari tashiga. Donshi washegari ta juya ya koma son zai fitane lokacin sunan Amir kawai ya tsayar dashi sai zancen tarewansu wanan gidan kuma yazo. Tana zuwa maigadi ya shedata yako hanata shiga gidan ashe harda shirginta ta kwaso nan ko maigadin nan ya rufe get ba ita ba duk wanda yazo a ranan sanadinta ya hanashi shiga gidan.
Chapter 296 · 0% Book details