Sashe 37
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
gidan hjy Fannah Abuja idan wani daga cikin iyalinta yaje tafiya ya dawo haka zai bimu da tsaraba gaba daya gidan ba wani raba kai ko nuna muba yan gida bane a wajensu haka zasu kawo muna tsaraba mai yawa da sunan mu. Haka kuma zamu dunguma anawa wanda yakawo din godiya group group yadda muke gidan tana saka muna albarka gaskiya don in tuna da wa yan nan mutanen arzikin a rayuwana. Naso antyna ta barni naje ko nidaya na ganosu tace min sai idan mijinta ya yarda da hakan dana kara tuna mata kuma sai cewa tayi dani wai yace tare zamu gaba daya da ita tun lokacin ban kara magana ba kuma. A wajen su mama din gefe muka koma sai can mama din ke fadin idan kin tashi maria ga taku tsaraban nan ta nuna mata wasu kaya harda na abinci shi yaya Habu din yazo ya kira mama din da kansa . Sun jima a can har iya yayin da antyna ta kwanta a nan falon tana barci don maganin da take sha a yanzu barci yake sata da zaran tasha maganin da safe. Lokacin da suka shiga falon Habu din Jafar ya shakin kamshin da falon keyi ya dan lumshe ido yana sauke ajiyan zuciya bin ko ina ya farayi da kallo komai gwanin ban sha,awa awajen, irin falon da yake muradin samu duk da part dinsa ya kusan ukun wanan din amma kazantar matansa ya hanasu tsayawa su gyara din. Duk da komai na zamani na more rayuwa ya zuba a falon gwaunin ban shawa amma komai yazo ya koma masu shara a yanzu don rashin kulawansu. Yana mamakin irin halin da matan nasa suka dauko yi mashi a gidan gaba dayansu ba wace zai buga gaba da ita a wajen tsabtan muhalinsu wanan abin yana matukar kona mashi rai. Nan ya Habu din yake gabatar masu da abin karyawan da aka aje mashi din a tare su ukkun suka karya a nan mama tazo ta samesu a part din don zancen dasuka zauna suke son magana da yaran nasu baki daya. Zama sukauyi na fahinta yadda ya dace din a tsakaninsu kan matsalolin da malami ya fada a zancenshi . Wanda kusan abin duk kamar akan shi yaya jafar zancen ke nufi da magauta suna binsa sosai bayansa. Sam bai dauki zancen da wani ma,anaba a wajensa don bai faye yarda da irin zancen malaman nan bashi kawune ma ke kokari ko yaushe akansa baiki yake karba. Yanzunma bai ki ta bakinsu ba don yasan dolene irin wanan harkan nasa ya samu irin hakan bayan sun gama kuma sukayi zance akan matsalolinsu inda harda zancen yayata ya fito cikin zancen. Don asibiti suna son su riketa a can wajensu sai zuwa lokacin data haihu sin yanke shawara kan mahaifiyar mu zatazo ta zauna da ita wanda already sunyi maganan hakan da hardo shine ya yanke shawara kan mahaifiyar mu zatazo ta zauna da ita din a asibitin. Azuciyarshi shi kadai yasan yadda yake ji a ransa a yadda yaga part din yar uwata din data gyara shi fes wanda shi a rayuwansa bai samu hakan ba duk da uban daulan da yake labta masu agidan. Haka yasa ya kara jin bacin rai a zuciyarshi yana tuno irin zancen da suke fada akan auren bafulatana da Habu din yayi saida wata rana ya fito ya tsawata masu akan irin maganan da suke yawan fada a lokacin kafin a auro yanda din a gidan. Yau sai gashi bafulatanan da sukewa dariya tazo da tsarin da su suka kasayiwa kansu suna tauye kansu da nasa hakan yasa a yanzu yakan sharesu na tsawon lokaci ya zauna a can abinshi yana harkokin gabanshi. Hakan kuma bai hana idan ya tashi zuwa gida zai tsaya ya sayo masu kaya na alfarma na kyace raini da za,a gani a fada a wajensu. Sai kamar bayan kwana biyune da faruwan haka ranan jumma,a kowa yaci kwaliya da dogayen rigunan daya sayo masu inda na dauki wani kampalana dinkin dogon riga na saka a jikina . Zaune muke muna kallon film tare dasu mama dubu suka shigo part din gaidasu muka farayi ban faye zama a falon ba idan suna falon nakan daga in koma ciki ko in fice zuwa wajen anty na muyi hira. Sai bayan sun gama gaisawa na mike na nufi cikin dakin kwanan mu lokacin mama dubu ke fadin niko Jafar ina ta son in maka magana akan wani abinda kayi da ban samuyi ba sai yanzu. Ya kamata ace kayan nan daka sayo ka hada da wanan yarinyar da zamanta yanzu ya dawo a nan bai kamata ace idan zaka sayowa matanka da yan uwanka abu kana debeta a ciki ba. Naji nauyi sosai da kunya tunda yau da kowa ya saka tsarabansa yai adon jumma,a dashi a gidan nan sam banji dadin hakan ba wallahi. Mama wace yarinya kike nufi tace kanwar matar habu din nan mana da take tare da yar uwarta gidan nan . Yarinyar da kwazonta wallahi ko wanan abin da kake ta yabon matanka sun hada itace yarinyar nan ta hada masushi . Hakan ma ba girma bane duk zancen da suke kanyi baice uffan ba don a saninsa ya fada masu cewa da matar Habu da yar uwar nan nata a cikin tsarabansu sai Habu din yake fadin . No ki barshi mana mama aiba sai ya basu abinda duk ya kawowa matanshi ba hakan wani sabon fitina zai iya kawowa kuma a tsakaninsu ai. Ke nan itama matarka ba a bata ba ke nan kake nufi ba,a bata ba gaskiya yaya Saare ta fada daga gefensu tana kallon yayyun nata. Nasan udan kince sai anyi hakan zai iya kawo matsala a gidan nan don Allah a barshi kada a kafa wanan hujjar don ni kaina ba zan iya hakan ba ko wani lokaci. Amma Habu kai kace kai ai karami sama dashi ba dole bane sai yabawa matarka amma yar nan dake tare da yaran nan hakan da nauyi gaskiya ace komai ba a bata ba cikin abindaya sayo a gidan nan . Mama ta dauki takakmana idan zai mata ban faye son takalma irin wanan ba dama Salima ta fadawa uwar nasu dake magana cikin damuwa.