← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 306

Sashe 6

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baiwa da albarka yana ga yayan baiwa da Allah yasawashi yai masu arzikin duniya da lahira saidai yana da wuya mu yan adam mu gane hakan da sauri . Ko wani mahaluki yana da kalan tasa baiwan arziki da Allah yai mai sai mai natsuwa da kula zai gane hakan mama Duba ta yarda da hakan akan diyanta sun taso da baiwansu saidai rashin hayaniyansu ya boye wanan baiwan da Allah yai masu. Yana da kyau uwa tasaka hope akan yayanta ta zamo mai kawar da ido da son nuna kaunar yayaa fili irin yadda wasu uwayen na yanzu keyi. Yana da kyau nuna kaunar amma idan kun kebe da yaran don nunawan a fili yana kai idon mahassada su illanta maki yara ko da bada mugun nufi ba kuwa don wani nasa baiwa a hassada yafi aiki wani ko daya furta ba daidai ba ga mutum sai hakan ya tabbata akansa din. Ansan ko wace uwa tana kaunan danta manya sunce badon kaza bata son danta bane take takashi sai don ya kula da duniya. Wanan akidar ta mama Dubu shine ta shammaci mutane ta kawar da kanta gun yayanta tun suna kanana take turasu koyon sana,a basu zama gida ana nuna masu kauna ko so da gata da akewa yaran yanzu ana kashe masu zuciya daga boko sai boko ko islamiya sai anyi wa yaro jan ido zai tafi islamiya din. A bangaren mama Dubu wanan tsare yake yaro zai tafi boko daya dawo yaci abinci zai sauya tufafi zuwa kayan aiki ya fita wurin sana,anshi hudu nayi dole ka dawo daukan karatun Allah wanan kai,dace a wajenta don dokan data sakawa yaran nata ke nan a gidan. Yana da wuya ka kyala ido da rana kaga dan mama dubu a gida yana shawagi haka kwana bibiyu dan uwanta zai ziyarci wurin aikin yaran yagano mata halinda yayan nata suke ciki. Yayin da ita kuma takan ware lokaci da yayan nata da dare suna hira tana jin shakuwar kowansu na gyara ta gyara masu maikyau kuma ta kara dorasu a hanya madaidaiciya akai goma zasu watsa zuwa neman wajen kwanciya zata kashe kallo cikon hikima da nisa tana fada masu akwai boko da safe ga zuwa wajen aiki gara ka kwanta da wuri ka samu natsuwa yafi zaman wanan kallon . A cikin irin hakan tasan weak point din dukkan diyanta kuma tana tsaye a kansu idan suna dakin nan zaki dauka yaya da kannentane suke hira a tsakaninsu. Yar uwa mai karatu idan Allah ya halicceki gidan gadu ma,ana gidan dake da iyali fiye da daya mata biyu zuwa ukku ko hudu zaki fahinci abinda nake son maki bayani a nan. Zama a irin gidajen nan zamane mai kama da zaman haya idon kowa na akan danuwa wani bai kaunan wani da karuwa ko cigaba. Amma a zahiri zamane zakiga anayi a fili kamar ana kaunan mutum da ciganbanshi sai a badili abin ba haka yake ba yadda ake nunawa a zahirance. Mama Dubu ta fahinci haka ta dalilin tsaikon haihuwan da tayi ta fahinci yadda abubuwan suke tafiya a tsakanin abokan zaman nata ta fahinci wanan akidar sosai ga yayansu. Za anunawa dakin ana kaunarsa a gabanki amma a bayan ki kamar Allah Allah akeyi yayi wanin abin magana da kowa zai tofa albarkacin bakinsa a kai gidan yawa kenan . Irin wanda iyayyen mu ke tara mata fiye da daya zuwa hudu ko wace mace da kalan tarbiyan da zataba yayanta ko wani daki zakiga shige dabiansu gudane dama hausawa sunce Nono alkalin da. Don kowani da irin tarbiyan da uwarsa ta bashi zai taso a cikinsa kusan haka wanan abin yake idan ka bibiya mafi yawa suna tasowane bisa ga irin jajircewan uwa a garesu wanan ke nan. Mama Dubu yau ta tashi da zuman zuwa gidansu idan nace gidansu ba wai ina nufin gidan iyayyenta bane a,a gidan da suka gadane ita da yayanta data haifa . Gidan da suka saida gadonsu suka hada da na wajenta data soma gidana suka mallaki wanan din da yanzu yaya Jafar yake rayuwa a cikinsa shida mahaifiyar mama Dubu da suke kira da Iya mai mai. Iya ita ta haifi mama dubu da kawu dauda sai mama dije dake aure a kaduna unguwar sarki sune Allah ya bar mata a raye amma a baya iya ta haihu basu tsayawa sai ukun nan suka tsaya raye. Itama iya suna da dan nasu rufin asiri daidai gwargwado saidai ba can can ba auren yaya jafar da zai tare a gidansa saboda girman gidan sukai shawara da iya ta dawo nan da zama tunda akwai wadattacen waje a gidan wanan dalilin yasa ta dawo gidan don ta zauna dashi. Ance a wajen aurensu babban kawarta da tayiwa amaryanshi kawance tunda ta kyala ido taga yaya Jafar ta daga hankalinta da ita taga miji . Don bai dace ace wanan hadaden guyen dan bokon irin da take mafalkin aure shine mijin kawarta da take kamar bagidajiya da ita dai ya dace kuma shi take so . Ita din yar kadunace don a kuduna iyayyenta suke da zama yayin da ita kuma uwar gidannasa Asmau mutumiyar Gwambe ce amma mazauna garin zaria aikine ya kawo mahaifinta zaria har yai ginan kansa zama ya kamasu a garin zaria. Da farko ance shi yaya Jafar din baya son Nusaiba don yarinyar da ba tsarinsa ba saidai kamar abin sihiri kuma ya dan soma kulata har abu yai karfi a tsakanisu ta shawo kansa sai zancen aure. Wata shidene tsakanin aurensa da Asmau dashi da kuma ita a lokacin zancen aurensa da Saiba kamar yadda nickname dinta yake a wajen kawayenta shi kansa mijin haka yake kiranta da wanan sunan sai ba. Lokacin farkon komawansa Lagos da harkan business dinsa ne don ya fahinci can akwai harkokin da zai iya wanda zai hada da nan arewa. Sai sana,anshi ya karbu sosai dan kudi sun fara shigo masa sosai a lokacin don haka bai samu matsalan komai ba don bai bukatan taimako a wajen wani. Haka akasha wanan bukin amare biyu a kusan lokaci guda duk ko da tashin hankalin da uwargida Asmau tayi kan ba zata zauna da kawar nata ba. Amma abu da manya kuma tsakanin miji da mata ance sai Allah haka ya shawo kan abinsa manya suka inmata ta zauna. Don hakane babu shiri ko zaman lafiya a tsakaninsu ko kadan ita uwargida tana ganin anci amananta dashi da kawarta. Yayin da amarya take ganin abinda yai mata kome mutane zasu fada su fada mana ita dai bata damu ba tunda ta kama mijinta irin yadda take so. Nusaiba Best friend din Asmau ce sosai saidai wanan kaddaran da Allah ya kawo tsakaninsu ya hanasu kwantar da hankali su fahinci kaddaran rayuwansu ce hakan. Na hada miji daya da sunan aure a tsakaninsu zauna suba kansu lafiya a tafi tare zama yayi dadi. Tun daga wanan lokacin kawance ya watse aka koma zaman kishi kinshin ma irin na hauka din nan sukeyi a tsakaninsu. Ga miji ba mai zama baneshi iyaka yazo yayi yan kwanaki ya koma ya barsu nan da iya da itace zasu zauna har zuwa lokacin daya dawo kuma. Wani irin zama mai wuyan fasara a tsakanin su suke gudanarwa agidan zama duk da part daya suke zaune wanda ya kara fadada girmansa lokacin auren Saiba ya mayar masu dashi two two bedroom babban falo a tsakiya. Wanda haukan kishi ya saka babu mai tsayawa daga cikinsu ya gyara part din zakice wa yanda basuyi boko bane a cikin gidan. Sai in sun fito waje zaki gansu fes dasu kamar ki wanke hannu ki taba sai kinje gidansu ki raina masu ni dai zee nace har da hali a irin hakan . Don wani baiyi ba aiba zance ba zanyi ba ko don lafiyata sai idan miji yazone dole mai girki zata tsaya ta tsabtace mashi falon koshi bawai can ba don kowa na bakin ciki da dan uwansa kada ya gyara dan uwa ya huta. Haka kuma bangaren abinci akwai matsala a nan ma din don kuwa idan ba miji ke gari ba haka zasuyi ta horar da junansu da takaici har sai lokacin daya dawo. Farkon zuwan saiba taso ace miji ya tafi da ita lagos don ta fadawa yan uwa da abokai ita ba zata yarda ya barta zaria ba don ba sakarai take irin Asmau ba miji yana lagos ita ta zauna a gida. Sai bayan ta shigone taso nuna hakan amma uwar miji tace bata kai can ba yadda ta sama sun tsara abinsu haka zata bi dole shine wanan rawan kan nata ya dan fara lafawa tun lokacin. Saboda ta fahinci ashe a karkashin iyayyensa yake wanan yasa Asmau dake gabata bata motsa ba take biye dasu a zauna lafiya. A cewan mama ba zata bari ya dauki iyali yaje zaman lagos ba don kada ya shagala da dukiyan marayu dake hannunsa . Haka zalika zaman shi a can din zai iya dauke masa hankali da gida dudu nawa Jafar din yake inbada rigima yaushe ma ya isa iya aje mace daya balle yace biyu. Allah ya taimaka jafar da yan uwansa mutanene dake matukar girmama iyayyensu a yadda suka taso da tsoron mama da iya kakarsu har girmansu haka suke masu biyayya sau da kafa. Zaman iya a wani bangare na gidan yayi tasiri sosai a rayuwansu dontane suke rage wani iya shege idan su fara yanzune iya zata tsaya tayiwa wace bata da gaskiya fes hakan yasa suke dan ragewa. Rayuwan malam bahaushe akwai kalubali da yawa a cikinsa inda wani zubin ake yawan tauyewa mace incinta da sunan aure. Akwai part din da babu kowa a cikinsa instead daya ta zauna a cikinsa amma iya tace sam hakan ba zai yuyu ba wanan din dai shine kasonsa don haka shida ya dauko auren mata biyu lokaci guda dole ya zauna a cikin nasa hakana. Sani Allah sani ma,aiki aka samu kawu Dauda ya rokan masa wanan filin daya fadada girman ginansa har ya bambanta dana yan uwa saboda kara fadin wajesa da akayi. Saboda raba gado da akayi yasa yaran mama Dubu tun bayan auren yayansu Jafar da hjy Iya ta koma gidansa da zama suma kusan rayuwansu a
Chapter 6 · 0% Book details