Sashe 151
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wasu jajayen atamfan super wax mai dan surkin flower yellow a jikinsu da akai min wani dogon riga yaji kwaliya har yagaji don kyau zakice jallabiyace rigan don yadda aka fitar da shi. Takalman kafata kuma half cover ce ta mata mai duwatsu new design sai gyale yellow mai duwatsu dana yafa hakama kunnena fashion na saka dayai shige da kayan sai agogo a hannuna da yar karamar jakkata yello. Ki firhita kishiya ga shiganki ko ta yaya yafi ace sai mace tagani ga kishiya taji haushi inji anty salma take fada min hakan ko yaushe. Donshi na tsaya na gyara yadda ya kamata ga wani kamshi da nakeyi na ban mamaki a haka na fito na rufe dakina kamar kullum idan zan fita daga gidan duk da muna rufe falon da ko ina amma ban yarda saina kulle dakin nawa kuma hankalina yake kwanci. Ya fito yana waya mukai arba dashi ya sake wayan yana fadin dankari wanan kwaliya haka Rahama ai sai ace yau din ne sunan ma ga baki daya. Yau ba suna bane yaya amma yau din ya kasance rana mai muhinmanci ce a gareni na juya wajen Biba ina fadin dauko basket din da muka shirya ki fita min dashi waje sai ki dawo ki dauki sauran ledojin nan kuma. Ta juya zuwa kitchen din ta fito da basket din dana shirya din da zamu jewasu iya da mama dashi na tsaraba ba komai bane yasa hakan don basu taba zuwa gidana sunci girkina ba yasa nayi wanan dabaran hada masu abincin muje masu dashi. A kofan gidan ma saida ya tsaya yana tambaya meye wanan kuka dauko hakane wai yana nuna basket din da nake gyarawa biba zananshi a bayan mota da take zaune. Na juyo ina fadin iya da mama zan kaiwa girkina suci sai yayi murmushi ya bude mota muka shiga maigadi yana tsaye har muka fita yana muna a dawo lafiya . A hankali yake jan motan har muka kai wani shago ya tsaya yace mu jirashi ya fita sai gashi da drinks na kwalaye masu sanyi saida ya zauna yake fadin ki hada masu da wanan din idan kuje nayi mai godiya a fili. A raina kuma nace Allah na godema da dabaran hakan yazo min nayi wanan abincin don iyayyensa din. Tunda muka doshi gidan na fara jan addu,a a bakina na neman tsari gako wani irin fitina daka iya tasowa ga zuwan namu har ya dosa kan motan zuwa cikin gidan muka shiga. Da Saiba muka fara ar,ba tsaye da wasu matan abokanshi da sukazo barkan haihuwan da farko inaganin bata san tare muke ba saida dayan take fada mata haka yasa ta dago tana bin mu da kallo. Da alama tayi matukar razana da ganina don ba karamin tsoro shigana ya bata ba tagama fada masu akan yar kauye yake son ya wofintar da ita itako zata nuna mashi ko wa take. Sai ga matar Nura na fadin kai Nusaiba kardai ince wanan kike kira da yar kauye ina itace amaryan taku ai ko ? Jin hakan data fada yasa ta dago da sauri ta kallomu tabbas din kuwa nice nake fitowa daga motar ina dariya don cewa da yayi bai ban bakin shiga wurin yanda ba sai wani lokacin nake fadin haba yaya kaima kasan aiko don Abba da akace baida lafiya zan shiga ai yace don kinsan ban iya hanaki zuwa duba babana ko kikace haka ? Part din su iya muka nufa da kayan dana dauko din muka bar saurab a cikin mota don ba anan zanyi amfani dasu ba na abokan zaman mamace da yace zamu je gaidasu daga nan. Shine agaba muna biye dashi mukai sallama muka shiga iya na zaune da tasbaha a hannunta mama na kasa zaune tana waya saidai shigowan mu yasa ta katse wayan da takeyi din cikin bacin rai ta amsa gaisuwan da muke mata din. Don tun kan na zauna na rusuna ina gaida ita kana na juya wajen iya dake fadin kai kakai amaryace yau a gidan namu haka ? Lalai marhabin da amarsu ta ango bakya laifi ko kin kashe yar masu gida kuwa laifinki kadanne a wajen ango nayi murmushi ina fadin iya mun sameku lafiya ya bayan rabo ? Yaki nan ki zauna ta fada tana nuna min kusa da ita a gefen kafan mama dake zaune a kasa din nace a,a iya nan ma yayi min barkan mu da arzikin saukan anty Asmau Allah ya raya muna. Tace amin yar nan haka akeson Allah ya sauke sauran al,umman Annabi baki daya na amsa da amin iya na sake juyawa wajen mama din nace mama barka da arziki ? Ta amsa da barka dai Rahama tare kuke tafe ashe ban amsa mata wanan ba din take fadin barakace ta bugo waya tun dazun suna rikici da mijinta akan kudin ta wai dake wajenshi. Ta fada tana kallon dan nata dake kokarin zama a gefen iya inda tace in zauna da farko din naki. Naji yace jam rikici kuma akan me ba ita tabashi kudin ba son me kuma zatace suna rikicii kan hakan ai dole suyi rikici ya karbe mata dan kudin ya cinye yanzu kuma ya dauko mata kishiya. To meye laifinshi a nan Dubu yayan kima ai kusan haka dinne shima ba aure ya kara yanzu ba da kudin ku ya shiga hannunsa abinda duk nakewa gudu ke nan ai tun farko gashi ko ya faru. Shima kawu aure yayi kome yana tambayan iya din cikin mamaki tace au bai fada maka ba ke nan to ina zai fada tunda yasan bai da gaskiya koshi ? Na juya wajen anty Saratu da fuskanta ke hade kila don zancen anty baraka dinne ko wani abu ke damunta nace anty saratu mun sameku lafiya ? Ta sauke ajiyan zuciya tana fadin ke dai Rahama lafiya kalau yaya gida ya amarci kuma ta fada tana kokarin gyara yanayinta din na farko. Ta dora da fasin wai wanan yar kamar yar wajen yaya Ai ko da cewa biba data aje basket din nace tazo gefena ta zauna itama a kasan da nake zaune din. Itace habiba na fada don ban tsaya wani sanyin da zataga hanyar sakar min wani zance ba don nasan zata iya indai anty saratuce shiyasa na sake ina magana ta bajin nauyin su kamar yadda suke zato da farko idan mun hadu. Wanan yasa na zake na shanye duk wani kawaici a idona ina bata amsa a lokacin saidai bana wuce gona da iri ba irin hakan . Iya zancen yaya daban da wanan fa don yaya ko yayi aure bai farawa ya taba muna kudin mu dake hannunsa ai wanan kuma fa duka kidin ta dauka ta mika mai don sakarci. Akwao kudinku ke nan a hannun kawu ya tambaya sai tasha kunu a fuska tana fadin akwai mana zai fara ya taba min sune tunda yasan yadda kudin suke? Mama meye rashin zama dayansu ai gaskiya iya ta fada gashi ya ban kudi daga cikin kudina ya hana kusan wata daya ke nan fa ana binsa ya bani sai yace wai suna hannun wanda ya dankawa. Saratu nikan wai meyasa baki da hankaline wai don Allah haba kinyi maganan kudin nan yace ga uzirinsa ba sai a jira kayan su zama kudi a kawo maki ba ? Hakafa kike abinki wani lokaci baki tunane idan abinki ya motsa saiki koma kamar da yaso fitowa ciki ranan ni banson irin haka wallahi yanzu da zancen yar uwarki zamuji data dameni da koke koke ko naki da kike son dagawa mutane hankali dashi. A,a mama ni bance zan dagawa ko hankali ba ai adai bani abin dana tambaya ko aban kudina duka tunda abin ya fara zama haka ? Ke tashi muje ki gyadasu ya fada ya mike tsaye ba tare daya tofa komai a cikin zancen ba sai na mike da sauri kamar yadda ya umurceni din na juya ina fadin iya ga abinci nan na girko maki tunda baki zo kin ci a can ba ? Kai kai kai kice girki amarya yau zanci gidan nan ke nan bari na kurkure baki nazo na dandana ko kin iya girkin muka fita muna dariya. Bayan fitan mu takecewa yar kin gani ai abinda kike nema ke nan dama har dan uwanki yasan abindake gudana yai muna dariya ana zancen yadda za a kwantarwa yar uwarki da hankalinta a samu kudinta ya fito kin dauko wani zance kina son tayarwa mutane da hankali. Mama nifa bance komai ba kudin nan tunda kikace kawu za aba nace maki a,a kika hakeni na yarda yanzu kuma kinsan abinda nake sonyi da kudin nan kuma za a ga laifina ? Don ganin iya ta mike zuwa baya yasa mama din tausa murya tanawa Saratu fadan abinda take kokarin yi din akan kawu gaban yayan nasu duk daya nuna bai damu ba amma sai bataso hakan ba a lokacin. Tare dashi muka shiga part din akwai mata sosai a wajen nasu yan barka wanda na sheda wasu don harda salima da Nafisa suna part din tare da yan gidansu Asmau don a unguwa daya suke don haka ansan juna. Ihu suka saka min ita da Nafisa kafin su shiga gaida yayan nasu na dan dara muka rugume juna aka gaisa su suka kaini dakin mai haihuwa dake zaune kanta babu ko dan kwali balle hulla kan ya dankare da kitson da akai mata din zanen yawo. Muka gaisa yar uwarta na fasin ga waje in zauna a gefen gado da aka shiga tattara kayan wajen saidana zauna nida habiba aka miko muna yaron muka dauka. Nayi mashi addu,an Allah raya mun dan kai kamar minti ashirin a zaune shiru na mike na karbi ledan dake hannun biba na mika ina fadin ga zanin daukan yarona. Yan uwan nata suka shiga godiya muka fito daga dakin dake wani irin bashi duk da kanshin turarena ya bi dakin lokaci guda amma haka bai hanani jin wanan bashin ba kona meye oho ? Falon muka fito muka kara zama banjin ya fita lokacin nafi zaton yana dakinsa don can ya nufa tunda ya gama gaisawa da mutanen falon. Ina anty Saiba tana ciki kije ku gaisa kizo