← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 211 OF 306

Sashe 211

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A galabaice na fito daga bayin wanda yakai har mama tudu saida ta shigo tana min sannu yayin da gogan ya wani tsareni da ido yana kallona daga kwancen da yake din. Mamace cikin kidima take fadin me kikaci ko baki da lafiyane nace ina ganin zazzabi ke son kamani don harda kaina yake min ciwo sosai. Jam aima kikana da karfin jini ko yaushe kina tsaye tunda mukazo laluran nan ban taba jin kince ga inda ke maki ciwo ba. Bari a duba in akwai panadol saiki sha ki kwanta ko zai fada maki ta kara min da sannu na amsa da kyat tare da fadin nagode. Asmau take fadin balle kwanakin nan akwai sauro ko jiya saidana kunnawa yaran nan maganin sauro muka samu barci dasu. Ina gama shan maganin na nufi dayan dakin na kwanta barci mai nauyi ya daukeni har yamma ban falka ba don na samu barci mai dadi a lokacin. Kodana falka na danji dama wanka nayi na dauro alwala na fito na tayar da sallah ina jin marata tana dan yanka min lokaci lokaci hakan yasa stil nake expecting din zuwan period dina na monthly da mata keyi tunda yakan zo min da ciwon mara wani lokacin. Abinci kasa ci nayi duk yadda mama ta matsa min kan naci amma na kasa ruwan zafi nasha na samu waje na kara kwantawa banyi barcin dadi ba a ranan don yadda jikina ya gashi nake jin zazzabi. Cikin ikon Allah zuwa asuba ya fada min sai gashi na tashi nayi aiyukan dana saba na dauraye mai jiki yadda na saba yi masa don ban yarda in barshi da najasa a jikinsa ko datti hakan kan kasance ko da mun yi aurataya nice zan masa wankan tsarki bayan na umurceshi da daura niya kafin kowa ya fito na gyara ko ina kamar komai bai faru ba tsakanin mu. Koda gari ya kara haskawa na gama da daki har falo lokacin ne mama ta fito tana fadin yar nan keda kika kwana da zazzabi kece ke aiki haka tunda safe daki bari ai zan iya in kama maki ai ? Murmushi nayi na dago daga sharan da nakeyi nace naji sauki mama na gaida ita da kwana take tambayana karfin jiki nace Alhamdullahi . Nagama komai na shiga nayi wanka na saka wani dogon riga na samu waje na kwanta a dakin duk wanda ya shigo a gidan zamu gaisa dashi yayi min yaya jiki ? A haka har aka kawo abin karyawa ina jin iya na fada tana fadin doya haka a bushe babu komai da zaca hada dashi kaci ya gogema makoshi. Hakan yasa banji sha,awan fitowa na karya din ba don nasan kayan takaici zan sama a wajen yasa banko fita da sunan karyawa ba a lokacin. Barcina nayi sosai a ranan don idona dama da barci ban samu barci da dadi ba da daren don zazzabin dake damuna din. Muryan mamace dake tsaye a kaina take fadin ki tashi haka tun safe baki karya ba kina kwance ko jikin ne har yanzu ? Na daga ina fadin a,a na mike da idona da sukai min ja zuwa bandaki nan kuma na kara jin aman yazo min saidai ba komai a cikina haka na wahala na fito daga bayin . Dashi muka fara arba ya kura min idanu yana bina da kallo kamar maye ni kallonsa har damuna yake a yanzu idan ya kafeni da idanunsa. Wai Rahama aman ne har yanzu badan mijinki na kwance haka ba ai sai ince ko Abba ya samu kani ne Asmau ke fadin hakan. Duk da gabana yayi wani irin faduwa amma saina dake nayi murmushi a fuskana kawai na samu waje na zauna ina goge fuskana da dan kwali a cikin wahala. Ki samu abinda kikaci kisha magani ya fada yana mai bina da kallo na dan sauke ajiyan zuciya na mike tsaye na fita zuwa part din su mama. Suna falon mu ita da mama da iya dasu inna na gaidasu na fita zuwa wajen anty Salima ko zan samu abinda naci a part dinsu don ko shayi ba zan iya sha ba a lokacin saboda yadda zuciyana ke tashi. Nan ma din ba wani abinda suka dafa a lokacin ma take girkin abincin ranansu take fadin bari ta hada min tea da sauri nace a,a ta barshi nashiga dakinsu na kwanta. Ina jin zazzabin na son ya dawo min haka na daure nayi sallah na koma na kwanta sai gata ta shigo min da furan gora mai sanyi shi nasha sosai don yayi min dadi a bakina sosai lokacin. Barci na koma sai zazzabin ya kara rufeni kuma mama tudu ce mai tambaya ina ina don bata ganni ba ake fada mata ina can dakin su salima kwance. Duk mun dauka dai zazzabin gajiyane haka kinsan halin malam ba haushe ba komaine ake saurin kaiwa asibiti ba sai anga yan dabarun gida sun kiyane za a kai kafa asibiti. Don kuwa ciwon kwana biyu ina kwance ragaraga dani abani wancan a bani wanan sai yayi dan sauki zai dawo kuma gashi banson yawan hayaniya ga tara miyau a baki saina faki ido na zubar shiyasa ban ma zama a cikin mutane a kwana biyun nan. Na idar da sallah a dadafe na dawo part din mu inda na samu su mama dashi a zaune shi kuma yana kwance a inda yake tunda na shigo mama ta bini da kallo tana min sannu ta dora da fadin. Ni dai ko ince an samu dan jinyane wanan ciwon Rahama kamar na mai shigan ciki haka komai kaci baya zama a ciki sai an amayeshi ? Daga inda mama dubu take zaune ta dago kai da sauri tana fadin ciki kuma yaya don Allah ki daina zancen nan . Wanda ke kwance haka rai a hannun Allah ina zancen ciki kuma ya fito nan gareta kuma ciwon daine yazo a haka balle dama wanda yai jinya haka ai sai yaji jiki daga karshe shima. Dadina dake sai ki dinga magana kamar karamar yarinya dubu to ko cikin ne Allah ba yana iya kawosa ba ko a hakan akwai abinda ya gagari Allah ne ? Iya ke fadan hakan ga mama din mama tudu tayi murmushi tana fadin shi dai nagani nawa akayi irin hakan muna gani dan wajen Rakiyana da mukaje jinya sokoto kwanaki da kariya ba sai anyi dori ya gwauce ba sai daga baya likitoci suka gano inda matsalan nasa yake dole aka rabashi kwana da matarsa a dakin . Ai kariya kikace yaya wanan da yake kwance haka shatkaf dashi bako motsi ina wanan zance ya fito haka kuma ki tashi ki danci wani abu kafin ki kwanta ta fada a karshe. Gabana sai faduwa yakeyi duk da zancen ban dauka zai iya faru haka ba na mike zuwa falo ban iya kallon abincin ba na samu wuri na zauna nayi tagumi. Sai a wanan ciwon na tsani halin maria ta da mama ke zaginta dashi ina kareta ashe wani shirun idan yai yawa wa mutum akwai illa don bata iya tabukawa kanta komai balleni ni kadai ta bari ina zugata a cikin dangin miji tana gefe ta fake da laluran ciki ta fita batuna yau wa zan tunkara in fadawa wanan magana. Ban koma dakin ba saida su mama din suka fara fitowa don neman wurin kwanciya a nan falo suka sameni kwance maman tudu take fadin ayyah dama aina fadi mu baki waje ki kwanta . Na dai daure na kawar da kayan da komai dana saba na koma dakin kwanan mu na fara shirin kwanciya a ranan har wani sanyi nake ji a jikina hakan yasa na nemi waje na kwanta na lafe a kujera. Da farko na samu barci amma da tsakar dare barcin gagarata yayi na soma kaduwa hakan yasa ni kuka ni kadai a inda nake din. Cikin karariyar muryasa naji yana kiran sunana yana tambaya yayane nace ba komai na kara nadewa don komai haushinsa nake ji a lokacin. Dole ya gaji ya kyaleni don bai iya tasowa zuwa inda nake nasan yadda banyi barci ba shima baiyi barci ba a ranan haka ya nade dai don ba yadda zai iya. Washegari mamace ta shigo jin bataji motsina ba tashigo tana tambayan ko jikin ne da kyat na iya daga kaina na bata amsa takai zaune tana dafani tace kina ko shan magani Rahama ? Na dai amsa mata ta dade zaune tana kare min kallo kafin ta mike ranan ita da kanta ta gyara muna part din su suna aikinsu na karfi yayansu daine sai a hankali gaskiya kuma abin kamar a jininsune yake haka gaba dayansu yayansu mata basu da moriya sam. A ranan itace ta bashi abinci na dai daure na gyara mai jiki da shimfida na koma na kwanta sauran aiyukane har bashi abinci duk mamace tayi a ranan tana falo tasa min kira nazo mu karya dole na taso nazo din. Cibi daya nayi na taliyan da aka dafa muna wai abin karyawan safiya na dawo dashi da gudu naje na amaye na jima na fito ina haki na kwanta mama ta dubeni tace anya Rahama kuwa. Yanayin ki ya nunafa kamar cikine dake komai da kikeyi na masu cikine fa Rahama baki na turo ina fadin haba mama na gyara kwanciyana . Ina wajen nade na dunkule yazid ya shigo suka tsaya suna magana dasu mama da matan yaya Jafar yake fadin Ke yaya dai mijinki yace nazo na kaiki asibiti baki da lafiya gata dai kan kamar maman biyu zazzabi kamar na mai ciki haka ta kwana tana wahala . Ciki kuma mama kamar wace tasha a ruwa aida an saka mata ayan tambaya akan cikin nan kuwa Saarece ta fada tana turo baki gaba har ta fara tafiya ta nufi dakin ta juyo tana fadin watan yaya J na takwas ke nan fa mama hakan kwance ake zancen wani ciki kuma yanzu gareta ? Dakuwa mama tayi mata tana fadin ja,ira mara kunya kinbi kina wani hakilo inma cikinne ina ruwan ki yarinyar da mijinta zaki kama wani zance can ? Har ta shige mama tudu naci gaba da fadin nina rasa menene tsakanin yar nan Rahama da saratu
Chapter 211 · 0% Book details