← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 306

Sashe 141

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ZAMFARA STATE
zaune take saman kujera abakin murhu tana tsigan alaihu yarta karima tashigo da kayan islamiyansu a jikinta.
Sallaman yarinyar ta amsa ta dago tana fadin har kun dawo ke nan amma yau kun taso da wuri karima ?
Ba a tashi ba mama na dawone ta shige daki uwar ta bita da kallo ta juya taci gaba da aikin ta yar tana daki bata fito ba can tasa mata kira ta amsa ta fito tana fadin gani mama ?
Kallo yar dake fitowa daga daki tayi ta juya taci gaba da yanka alaihun data tara a hannunta tana fadin ki wanke kwanukan can da aka tara.
Ta amsa a cikin sanyin jiki ta sake juyawa zuwa dakin nan ta dakatar da yar nata tana fadin kin shigo sai tukuburi kikewa mutane kamar an maki wani abu ?
In baki da lafiyane ai sai ki fada amma kya kamawa mutane hade rai a cikin gida haka mama ni lafiyata kalau karima din ta fada tana shiga daki.
Ta fara wanke kwanukan ke nan yan uwanta suka shigo suna hayani suna fadin muna ta nemanki ashe kin dawo gidane ke muga suwaiba tace taga kin nufo gida kina kuka.
Tashigo gida tana cicika na tambayeta tace ba komai ita ta sani tunda zurfin cikin tsiya yayi mata yawa ita.
Kodai zancen baba kikewa kuka anty Karima kanwarta mai,gado ta fada tana kwabe hijab din ta nan uwar ta juyo tana fadin zancen baba da yai me kuma ?
Kallon kanwar nata maigado tayi tana mata alaman kada ta fada amma ina bai mai,gadon taba da amsa ba Zarah ke fadin wai don ance baban mu zaiyi aure ?
Wani baban naku baraka ta fada tana sake yukan dake hannunta baban na nan gidan mana mama su Rabi,a ke fada muna dazun da zamu islamiya.
Wai har ya biya sadaki satin sama za a daura aure shida anty Safiyan gidan aska .
Kirji ta buga take fadin babanku fa tace haka sukace shima baba wallahi ya rasa wace zai aura sai wanan mai zubin yan erea din don Allah ?
Mikewa tsaye uwar tayi tana fadin a ina kukaji labarin nan wajen su Rabi,a mama ta nufi daki lokacin ita karima ta mike tsaye tana fadin a,a mama don Allah ina zaki ?
Kada kije gidan su Rabi,a tunda a sace ta fada muna tace wai
ba,a son gidanmu a san da zancen saidai muji an daura aure kawai wai inkiji ba zaki bari ba.
Ni wallahi mama yadda baba yaje yana bataki wajensu shine yayi min zafi.
Bata jin me yaran ke fada a lokacin ganin ta fito da hijjab dinta yasa yaran tareta suna hanata fita tare da rokonta da kartaje don Allah dariya za ai mata tunda duk unguwa sun sani ashe .
Ke ban hanya gidan uwani zan tafi ta inji kome ke faruwa uwani tasani wata uwani kuma mama uwanin da kullum a nan gidan nata anty Safiya ke tsayi da maza.
Da kyar yaran suka hanata fita ta koma ta zauna tayi tagumi tana jin wani irin abu yana rufe mata zuciya lokaci guda.
Lalai in wanan zance gaskiyane malam ya cuce ta kuwa da kudin gadonta yake nufi zai auro mata kishiya ?
Kishiyar ma Safiya da suka sha artabu da ita kafin ta samu tabar mata miji taje kauye tayi aure ashe data fito din nan ma suna tare bata rabuba dama lafewa yayi don ba ko sisi a hannunsa.
Sai yaran suka karasa girkin ranan gashi maigidan yaje kauye cin kasuwa bai dawo ba ko zai dawo sai cikon dare sosai sunkan iso saboda nisan garin da suke zuwa din dauko hatsin.
Zancen yaranta gaskiyane Safiya bata wanka ta bushe tana gidan uwani ko yaushe wanan yasa halakansu da uwani din a yanzu yayi sanyi sosai tunda ta fahinci hakan.
Abincin da bataci ba ke nan ranan don yadda take jin kanta tana ji a ranta har in zancen nan gaskiyane hakan zai kawo masu matsala da mijin nata kuwa.
Bata yarda ta kwanta ba tana dakon jiransa ga wayanta ba caji balle ta kirashi taji yana ina don ta fara tabbatarwa tun a wayan.
Shiko a daidai lokacin suna cikin daji motarsu ta lakace masu a daji har barci barawo ya saceta bata san lokacin daya dawo ba sai asuba da yake tayar dasune ta gane ya dawo gidan ashe ?
Ta daurene don kada su raba gari da asuba mutane suji hayaniyarsu har yaje sallah bai dawo ba kuma saida gari ya waye tangararan ya nufo gida da ledan kosanshi daya sayo ya hada da kunu.
Tana jin dawowan shi din batayi magana ba saida ya samu waje ya zauna yana kiran zarah ta dauko mashi kununsa ga kosanshi ya aje tare da kullin sugar dari aganshi.
Baba ba a dama kunu ba yau yarinyar ta fada cikin mamaki yake fadin ba dama ba saboda me ?
Lokacin baraka ta fito daga daki tana fadin bandama ba don banjin hakan kana iya zuwa wajen karuwan ka ta dama maka ai ?
Karuwa kuma Baraka a ina na sameta kuma ya fada yana mata kallon mamaki tace eeh karuwan unguwa da kuka saba sheke ayan ku da ita mana.
Kaje ta dama maka dama ai kun saba da hakan dama malam cutata kaso kayi ka yaudareni kayi aure ban sani ba ?
Aff zancen banza ke nan to tunda kinji baraka meye na yaudara a ciki aurene fa sunnan ma,aikin Allah zan raya kike kira da zina ?
Lalai malam ashe kuwa zancen nan da gaskene auren kuwa zaka kara wallahi baka isa ba kaban kudina dake hannunka in yaso kaje kayi ta auren ka bai dameni ba ?
Kai mata hooo yanzu ke wanan abin yar yakai kiyi min gori a kansa don kawai zan kara aure baraka ?
Ai kaji abinda nace ba zancen gori a cikin zancen nan ka bani kudina kawai shine magana tunda da bakai zancen aure ba sai yanzu dana dankama gadona a hannun ka ?
Gadon mu dai tunda ko mutuwa kikayi yanzu nida yaran nan muke da gadonki baraka kuma aure ba karya aka fada maki ba aure zan kara kiyi abinda zakiyi .
Kudi kuma banda su yanzu a hannuna kin dai gani kema da idon ki sai ranan da kayan nan suka zama kudi na sayar in baki kudin ki.
Aina dauka zaki min adalci shekara nawa ina zaman hakkuri dake a gidan nan ban kara maki kishiya ba ashe ban sani ba son kanki yayi yawa har haka baraka.
Meye amfanin namiji kama ya zauna kullum da mace daya kamar laya a wuya ba kari kullum kana fama da abu daya kiyi min adalci ma ?
Kuka tasaka sosai lokaci guda tana fadin malam ka cuceni ashe duk dadin bakin da kake min don ka karbe kudin nan ne kayi aure ?
Kudi ban je gidanku na karba ba ke kika kawo min su nan da hannun ki ko kinga naje gidanku na rokesu subani kudin ki ?
In zaki zauna kiyi hakkuri ki dubi diyan ki ki zauna in kuma baki hakkuri Baraka hanya a bude take kya iya tafiya nikan aure ba fashi jumma,a mai zuwa insha Allah.
Shi munafukin dan naki daya fada maki bai maki karya ba na biya sadaki da ko mai Safiya tana matsayin matana a yanzu kije duk wanda zaki fadawa na karbi dukiyan ki a garin nan ki fadi bandai je gidan ku na tasa yan gidan ku gaba suban kudinki ba.
Don haka ba a hanani ra,ayina a yanzu aurene ba fashi na fada maki na biya kudin komai na al,adan aure.
Ya mike yasa kai ya fice daga gidan ya barta nan tana ihu hannu a kai wanan yasa Aliyu dake dakinsa na soro ya fito yana tambayan abinda ke faruwa ?
Sai maigadone ke fada masa wai baba aure zai kara kuma da kudin mama fa ta fada cikin wani yanayin damuwa a fuskanta zuciya da rauni.
Kasan me kuma yaya wai wanan matarfa yar bala,in shiya baba zai aura na sani ai bashi nake son fadawa mama ba lokacin taki saurarena.
Don da bata nan wallahi kullum sai kowa ya rufe gida suna waje suna hira har ana gulmansu a shiya sau nawa ina haduwa da baba wajen mai nama yaje a yanka masa wajen hiran mu ?
Cikin kuka Baraka tace shine baka fada min tun lokacin in sani ba sai yanzu da yaran nan suka jiyo sukazo min da labarin ?
A,a mama nayi niyar fada maki a lokacin kikaga kamar kudin ki nake so a lokacin kika zageni ni kuma nayi shiru.
Shima baba ya dauka zan fada maki tunda duk muka hadu sai yayi min kashedi duk yaji zancen nan a bakin ki sai ya saba min rai ni kuma na share nabar zancen tunda kin yarda dashi.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

5️⃣3️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Chapter 141 · 0% Book details