Sashe 40
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
gane anshigo dakin a lokacin. Asmauce matar ya Jafar ganin mu a zaune gaba dayan mu yasa ta soma gaida tsofin da kwana kafin ta dora da fadin mama kiwa Nusaiba iya dani dan Allah. Mekuma ya faru da safen nan kasa magana tayi sai hawayen dake zubo mata hakkuri suka shiga bata suna fadin kiyi hakkuri Asmau kinsan halin abokiyar zaman ki sai kici magananin zama da ita ta hanyar kawar da idonki a kanta. Mama don Allah wani irin kawar da ido ake son inyi ga Nusaiba yanzu kuma bayan wanda nakeyi yanzu akan mimi fa da yarta Nusaiba ta dokan min yarinya har wani wayau sanin haka mimi tayi mama saboda Allah ? Duka kuma me yarinya kamar wanan zatayi mata har da duka duka sosai tayi mata mama ki duba yadda bakin yarinyar nan ya fashe wai don kawai suna wasa a falo fada ya hadasu ta kayar da yar uwar shine Nusaiba ta fito ta duketa fa haka ? Tir da halin wanan yarinyar wallahi banda abin namiji banga abinda yaron nan ya gani a jikin wanan yarinyar mara mutunci ba wallahi. Iyace ke fadan wanan maganan inda tacigaba da fadin wanan yar yadda take baka haka zuciyarta yake baki ba digon rahama a tare da ita,,,,,, Iya baki san kan zance ba kin zauna kina zagina ai tana tsaye yaran suke fada bata rabasu ba har ta kayar min da ya tana duka don rama kuma shine wai nayi laifi ni wallahi ba zan yarda da irin wanan ab,,,,, Ke don Allah ku fita ku fita masu daga shiya kuje can ku kashe kanku da yayan naku kada kuzo ku tayar masu da hankali a nan kuma ? Ya Habune ke fadan hakan da yashigo part din ransa a bace yana binsu da idanu duk suka juyo suna kallo shi. Wanan wani irin rashin hankaline da zaku dinga fada akan yaya tun suna kanana ku koya masu mugun dabia wani irin halin banza kuke son yayan ku su taso a cikinsa ? Indai hakane zan karbe yaran a waje da zaran kun yaye kada wace ta raba min kan jikoki mama dubu ta fada garesu . Ace mata baku da abinyi sai fitina a kullum ku kwana jidali ku kwanta da jidali mama sin tacigaba da fada tana fadin maganganu akansu. Dama ace fitinan nan naku shine halin arzikiku da mijin ku zai dawo ya sameku a cikin farinciki da jin dadi da walwala ba yazo kulum ga jidali kuma ya sameku a cikin kazanta da doyi ba. Iyace take wanan katobaran a gabansu daya saka aka kwashe da dariya bandani dasu da suka hade rai tace Allah ko banda kazanta da tijara ba abinda suka koya ga uwayesu da zasu barwa diyansu gado suma. Iya da banda tarbiya ai Jafar ba zai auro niba gidan nan fada kuma kowama yanayi idan antabashi ai ta juya ta fice daga part din ranta a bace. Anan tabar kishiyar nata su mama suka haita da fada ya Habu yaja tsuki ya juya ya fice daga part din a hasale yana maijin haushin abinda yake faruwa din. Iya kin damemu da fada don Allah ki bari idan mijinsu ya dawo ki fada mashi mana Saare ta fada tana kallon iya din dake faman jinini ba fada bane fadan gaskiyane da bakwaso ayi mama ta fada. Nasan maganin su ai idan na hade kan yaran na tafi dasu can babban gida sai muga ta tsiya kuma da sauri Saare din ta kara fadin a,a mama barsu da yaransu don Allah matan nan basu da mutunci . Har sukayi suka gama ban ko daga kai na kallesu ba ina faman tunane kasan raina dan na dauka matsalan yayata din wani babban lamarine na tashin hankali lokacin. Duk da ance mahaifiyanmu zatazo zama da ita hakan baisa naji dadi ba a raina idsn na tuno da sheri baffa a ranan haka na wuni a cikin damuwa da fargaba ina zullumin abubuwa da dama a raina. A haka barci ya daukeni sai wajajen yamma na samu na tashi sallah nayi na fito da niyar zuwa part din anty na sai na samu sin fita da mijinta basu gida ban san dai fitansu ba a takaice. Ga kuma kaina yana ciwo don haka na yanke shawaran zuwa wajen matan ya J in samo ko paracetamol insha ya dan fada min. Sam ban kula ba da shigata nakeyi sallama anty Asmauce na sama kofa don hakan ban hango na cikin falon nake fadin anty don Allah kuna da Paracetamol insha kaina ke ciwo ? Ayya banda shi Ramaah ta fada a takaice nace ko maman sultana tana kusa sai ta dago murya tana fadin gaskiya bansan inda na ajeba a yanzu jin hakan yasa na juya zan fice daga part din. Muryan maigidan da bansan ya dawo ba a lokacin naji acikin tsawa yana fadin you are very stupid all of you ina maganin dana aje agidan don irin hakane wai ? Wai me kuke nufi da wanan halin bamzan a yanzu shekaran jiyan nan mama ta gama yi min complain a kan kayan dana bayar aba kowa gidan nan kun hanawa yarinyar nan da yarta. Niyi magana kunce ban lissafo da suba ai niko nasan abin da nakeyi da badon mama ba wallahi duk inda kuka shiga da kayan nan sai kun fito dashi a gidan nan. Yanzu kuma gashi to tazo neman magani kunce wai baku da magani for god sake wani irin halin banzane haka wai kukeyi kun kuwa san hakin makwantaka balle na wanda kuke rayuwa a gida daya dashi haka kuwa ? To aini bansan ko wani take nufi ba balle in bata Asmau ta fada itako saiba cewa tayi nifa cewa nayi bansan inda yake ba ba cewa nayi ba zan bata ba ai. Kaji takwal Asmau bansan irin bokon da kikayi duniya ba wallahi karatun ki ke kan bai maki amfani ba wallahi ke kuma Saiba bakin hali da iskaci ko ciwo ai yana kan kowa yasan kofan kowa a gidan nan. Ban tsaya jiran karasan zancen su ba na juyo zuwa part din iya na samu kujera na kife ina rufe idona an dan jima kadan sai gashi ya shigo iyace a gida mama tare suka fita dasu yaya Habu daga gidan. Ina yarinyar nan yana tambayan iya yakai zaune a kusa da ita tace wace ke nan fa yana fadin wanan yar uwar matan Habu din nan mana dake gidan nan. Dazun taje wajen marasa hankalin nan neman magani ta hade wai kanta yana ciwo don rashin hankali iya ace wai magani ma rowansa sukeyi a gidan nan sai cewa sukayi da ita wai basu dashi. Kaji marasa kan gado ko dazun fadan sukayi aikan diya nan ta kora mashi yadda abin ya faru ransa ya baci sosai ya mike yana mikawa iya din ledan maganin daya dauko yace tabani. Ai gata kwance iya ta fada tana nuna mashi inda nake kwance abayanshi au itace nan a bata tasha idan ta tashi ya fada ya fice daga gidan. Ficewa yayi daga gidan kai tsaye unguwar iyayyensu yaje ya samu abokansa na unguwar yakanyi hakan idan yana gari ya zauna wajensu suyi hira sai yayi sallah magariba da isha yake nufowa gida. Saida ya tsaya ya sai kayan sanyi dana tabawa ledoji daban daban ya nufo gida dasu kai tsaye falon iya ya nufo inda ya samesu zaune suna hira ni ina zaune a inda na idar da sallah na ina addu,a. Saare karbi wanan ledan kowa da nasa kada kociwa iya nata ya fada sai iya ke fadin ka sako dana yar nan wace ya tambaya yana rabon ido ta nuna mashini da ido yake fadin ya saka ya fita .