Sashe 117
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani yanayi na wasan yar tsamane ke gudana a tsakanina dashi agaban yan uwansa a lokacin don saiki rantse da Allah dama akwai shakuwa ko soyayya sosai tsakanina dashi lokacin a haka muka nunke zuciyarsu da kasa fahintar mu. Suma din sai faman mamaki hakan kowansu keyi a zuciyanshi don yadda komai nakeyinsa a natse cikin wayewan kai nafisace ta fara mikewa wanan lokacin. Don barin falon wanan dakin da sukaiwa kansu masauki a cikinsa ta shiga da sunan kewayawa bandaki daga nan bata fito ba kuma. Kafin Salima itama tabi bayanta zuwa dakin suka barshi shi kadai a falon zaune yana waya. Don lokacin na mike ina kwashe komai da akai amfani dashi zuwa kitchen na dawo na gyara wajen nan na samu su dukkansu sun bar wajen a lokacin. Zuwa lokacin barcine duk a idona don nima hidimar bukin da jewadi ya kashe min jiki don sai a lokacin nake jin tsamin jikina na gama na nufi dakina na barshi nan a zaune falon kofan na rufo na fara zuge zip din rigan jikina na fada bandaki. Ina shiga na fara cude jikina da wani ruwan turarensu na madara irin tasu ta mutanem maiduguri wanda mama tabani tace dinga hakan dashi da dare kafin na kwanta. Bayan na gama na fito na dauki Rigan barcina dana dauko na dauka saman gado ina zurawa a jikina ji don barcine sosai ne a idanuwana nake jiba a lokacin . Ina kokarin zura rigarne naji anrugumeni ta baya ana sakar min nauyi da sauri na iya furta subbahanallahi na ambata a fili duk jikina yana rawa lokaci guda don tsoron hakan da naji . Danshina nayi kokarin juyowa cikin faduwan gaba don ganin ko waye haka ya razanani lokaci guda duk da ban faye tsoro ba amma hakan dai ya firgitani. Saidai haka din bai samu ba a gareni don irin rikon da akai min sam na kasa jiyowa din inga waye a lokacin. Amma saboda sautin numfashinsa dake shiga kunnena a lokacin naji a cikin wani yanayi wanan yasa lokaci guda jikina ya dauki rawa tsoro yana dada shigata. Wani abu naji yana min yawo tundaga tsakar kaina har zuwa yatsun kafana jikina sai kyarma yakeyi don ban tsamaci hakan a lokacin ba. Nauyin Kanshi da naji ya kwantar a kafadana yana fadin relex baby Rahama ba komai zan maki ba just live me to hug you. Na samu natsuwa kawai nake son samu a wanan lokacin yanzu gareki ya fada kamar mai yin rada a lokacin cikin kunnuwata. Kalman na natsuwa na sake maimaitawa a ciyana kamar wanda ya karanto zuciyana din naji yace please Rahama don't judge me accondin to my sin ina kaunarki har cikin raina ke din kamar zabinace Allah ya kawo min a sauwake har gida don Allah kada kice zaki hukuntani bisa kuskuren fahinta . Hawayen da nake kokarin tarewa kada su zubo daga idona sune suka dinga diga saman hannunshi haka ya sanar dashi kukan da nakeyi a lokacin mara sauti. Subbahanallahi are you crying Rahama sabodani No no no no don Allah ki daina nasan ni mai laifine a wajen na shiga maki rayuwa bada sanarwan ki ba. Amma ina son ki dauki hakan a matsayin kaddaran mu gabaki dayan mu Allah yayi sai munyi rayuwa irin hakan a tare dake koda iya hakane kuwa a rayuwan mu. So ki bari na gama dan abindake gabana kafin mukai ga matsaya a tsakanin mu ba zan maki dole a kaina ba Rahama ko haka Allah ya barmu nasan kinyiwa iyayye biyayya dani. Naji dadin natsuwan da kika nuna a gaban sisters dina ko iya wanan kika barni dashi nagode Rahama don kinyi min abinda ban taba zato ba a wajen ki. Na dauka sam ba zan samu kallon arziki ba ko tarbo sannu da zuwa sai gashi kin fitar dani kunya a lokaci guda wanda ni ban taba kawo hakan agareki ba. Yana maganan yana kokarin dago habana dake dage yayin dana gane nufisa na cije cikina a waje daya naki yarda hakan ya faru. Sai naji yayi murmushi ya dan rage rikon da yai min din da farko wanan karon hannuna ya kama zuwa bakin gado ya zaunar dani shima ya samu waje ya zauna a kusa dani. Dan shiru ya biyo baya a dakin kafin yace wallahi Rahama banyi haka don in tauye maki rayuwa ba nayi don ni a wajena komai naki wallahi yai min ina sonki sosai Rahama saboda halaiyan ki don haka ki ban hadin kai mu zauna lafiya. A raina nace bakai bane yanzu fa ya gama cewa jn bashi time in rufa mai asiri ya fara fuskantar abindake gabanshi yanzu. Yanzu kuma ya dawo yana rokona da mu zauna lafiya bisa amana kada dai ya zamo munafukin namiji mai baki biyu ? Wa yan can suma Allah kadai yasan irin dadin bakin da yaje yayi masu a kaina duk da ban tabbatar ba amma akasarin maza haka suke da baki biyu ga matansu. Me aka fada maki Rahama akan zargi wata zuciya ta tuna min da hakan daga bangaren zuciya tiryan tiryan nake tuno zancen su hjy yabi da sukai min a karshe don haka dole inyi taka tsantsan da rudin zuciya mai kai mutum ga halaka . Wanan aure dai matukar bashi yace ya fasa ba dole in hakkura da komai in zauna da yaya saboda biyayya kamar yadda su daddy suka rokeni dayi don haka alkawari na dauka in sha Allahu zanyi biyayya ga zaman aurena a gidan ya Jafar har inda rabon zaman a tare dasu. A zatona zai koma dayan dakin daba kowane kamar yadda anty salma take sheda min wancan dakin yurakanshine nan kuma nawa sauran dakunan biyu kuma na aje don baki daya kuma na dinga amfani dashi ni kaina daki biyu ke nan suka ware min ni daya ko ina zan kaishi oho ? Hannuna ya sake rikowa yana dan murza yatsuna a hankali kamar dai wanda ke wasa da hannun yaro yayin da wani boyayyen sakon da ban,saba dashi ba ke bin ilahirin jikina yana sakar min da kasala. Kan na tantance sai ji nayi ya sumbaci gefen wuyana nan da nan jikina ya fara rawa tsoron hakan karara ya baiyana a gareni lokaci guda. No kwanta ki huta akwai gajiya a tare dake ya fada yana kokarin kwantar dani saman gadon kamar karamar yarinya banki ba nayi yadda yacen na dunkule a waje daya ina mai kame jikina. Wani ajiyan zuciya ya sauke yana kaiwa kwance daga gefena nima din na sakankace da zancenshi hakan yasa na lumshe idona ina sauke ajiyan zuciya. Ido a rufe zuciya tab da fargaba da zullumin hakan dana tsunci kaina a cikinsa lokaci daya naji saukan hannunsa saman jikina a daidai wajen da nayi shekara da shekaru ina boyon abina da hijjabi ko gyale yau sai gashi a saukake hannun wani ya kai ga wanan abin. Bai dai min komai ba a ranan kamar yadda yace saidai nasha luguda kamar mangoron da akeson ya nuna a lokaci daya. Da misalin karfe hudun asuba naji tashinsa already na falka a lokacin don sabo da hakan danayi a rayuwata ban daki ya shiga ya dan jima kafin ya fito yana dan kiran sunna da intashi kada in nakara ganin na falka ya bude dakin ya fita hakan ya ban daman samu na mike na shiga bandakin. Wanka nayi ina hawaye har nagama na fito na dauko kayan sallah acikin wardrobe dina na tayar da sallah ina idarwa na koma barcin don idona cike yake da barci a lokacin. Alhamdullahi don ko na samu barcin nayi ban falka ba sai wajajen takwas na safe na tashi dakin na fara gyarawa duk da a gyarensa yake amma haka bai hana na kara tsayawa na gyara ba na sauya zanin gadon na sharo na kawo kamshi na feshe dakin dashi na shiga wanka. Bayan na fito na saka kaya wasu light green lace mara nauyi da akai masu dinkin riga da skirt na saka sunji duwatsu anyi kwaliya a gaban rigan da bakin lace din saina zauna gyaran fuskana a gaban mirro. Lokacin ya shigo dakin a cikin shirinsa na wasu fararen shadda da akaiwa dinkin gajeren hunnu sai bakaken takalma a kafasa kansa babu hula. Da sallama na amsa ina dukar da kaina kasa ya karaso yazo daidai bayana ya tsaya muna kallon juna a morron nayi kasa da kaina na zame kasan kujeran na duka ina gaidashi da kwana. Wani irin mamakine da yarinyar nan take kasheshi dashi yaushe rabon daya tunama ana gaida miji da kwana a addinance ko al,ada ? Wani irin son ta yaji yana kara shiga zuciyarshi don tunda yake koda tuntuben harshe matansa basu gaidashi da kwana wani lokacin ma da fada suke tashi tsakaninsu tun asuba. Hannuna ya kamo muka koma bakin gado muka zauna naji ya ambaci sunana yana fadin Rahama jiya kin shayar dani farin ciki a rayuwata kin tabbatar min ke din yar mutuncine data gaji hakan. Kin tsare mutuncinki dana iyayyenki ko a hakan da kikai min nagode sosai Allah yayi maki albarka nayi kasa da kaina a cikin nauyi da kunyarshi. Wallahi Rahama komai naki kara burgeni yakeyi ina son ki sosai wallahi don Allah ki ban hadin kai mu zauna lafiya Rahama". Abune a baiyane da kika sani tun bayan wata ukku da aurena da Asmau farin ciki ya gushe min ba zance banjin dadin zama dasu ba don su din matanane amanatace kuma su din. Amma sun kasa ban irin farin cikin dana taso ina mafalkin kansancewa a cikinsa sun hana min kwanciyan hankali sun kasa gyara kansu wanan duk ba bakon abu bane a wajen ki don kinsan komai. Wayanshi dake ringing bai kula dashi ba nakai ido na kalla sunan ya Habu na gani a wayan ganin ina kallon waya yasa ya dauka yana fadin. Hello Habu ganina shirya yanzu zan karya in fito kana gida ko ban daiji amsan da habu din ya bashi na daiji yace hakan yayi daidai zanzo da salima din. Mike tsaye yana fadin tashi muje ki karya yaran nan sun hada muna abin kari yana falo ina son in mugama zan shiga gida mu gaisa dasu don ban samu zuwa jiya ba na