← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 306

Sashe 50

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

harsai sun haife cikin saboda tsaro irin hakane sa,an jahiliya mace tayi ta daukan ciki tana samun mata har mahaifa yazo a karshe ya kasa daukan cikin don wahala. Ita kuma yanda abinda Allah ya jerabeta ke nan dashi a rayuwanta har wasu naganin hakan samun wajena kawai da jin dadi irin na wasu matan da sukeyi da gangan. Bayan na idar da sallolina na shiga wanka na fito na zauna na gyara jikina ina dakin nake jin muryan Saiba a falo wai tazo idan masa da miyar sun rage a zuba masu su kara wanda aka kai masu sun cinyeshi gaba daya. Naji muryan mama tana fadin ba za a rasa masa da miya ba ai fruits salad din daine ban zata yaran nan sun rage ba ? Muryan Salimace ke fadin mama kinsan fa nida Ramaah bamuci komai ba sai anjima kada ki kwashe ki basu duka bamuci ba. Salima meyasa kike hakane masan nan mai yawa ina zaki kaishi don Allah azumi akeyi balle kice da safe zaki shi . Mama meyasa basu fito anyi aikin dasu ba aimu ba bayinsu bane da mukayi tunda aikin mijinsune ? Sai abin yaso ya zamo kamar fada a tsakaninsu da anty Salima din har Saiba na fadin ai dai mijin su ya kawo ai masu dole kuma suci ko bata so ai itama zata gidan wasu za a rama masu abinda take masu can. Muryan ya Habu naji sai lokacin nasan ya shigo gari ashe shima yana garin tunda yamma tare dashi akasha ruwa. Shigowanshi gaida su mama shine kashe fitinan da saboda sanyin hali irin na mama ta kasa kashewa a lokacin. Saida naji fitan ta na fito ina gaidashi da dawowa ya amsa min kamar kullum ba yabo ba fallasa a fuskanshi yana tambayan ya gida ? Na amsa da lafiya kalau nan dai muka zauna suna hira dasu mama wanda hiran akan saiba ce data fadi maganan banza. Naji ya habu din yace da mama daga yau duk abinda ya kawo ki barshi yakai masu can kome za ayi suyi masa da kansu sune dolensa ai tunda shiya ajesu. Nima dai a raina haka nagani mutum mai mata biyu kamar yaya jafar sai ya tsaya yana wahal da mahaifiyarsa da kannesa kuma ko kuma ya dauko yar aikin da yace zai dauka mana a baya ya dinga biyanta duk wata. Ina zama na debo masa kwara biyu da miya sai gashi ya shigo part din daga rakiyan abokan nasa ya ajewa mama leda yana fadin. Kai mama yau kun fitar dani kunya da bakin yan sherin nan kinji yadda Anwar yake santi kuwa ? Gata nan dai itace zaka godewa yanzu haka zancen ka samu munayi a nan matar ka tazo nan kan wanan abin tana fadan abinda bai dace ba. J don Allah daga yau din nan duk abinda ka samu na laluranka ka dinga bar masu can suyi ai suma matane kamar kowa ? Me zai gagaresu iyawa da har zata shigo nan gaban mama tana fadin magana haka komai na gidan nan suna zaton nakane don haka yaran nan basu da daman magana a kai ? Me tazo tayi nan Habu ba naga Saratu ta shiga masu da nasu ba dazun kafin a sha ruwa ? Koma dai meye sun din suke da alhakin irin wanan aikin gareka basu mama ba da yaran nan don a kaucewa fitina irin haka. Kuma ka kyaleta tunda nayi mata magana ba sai kaje kayi fada da ita ba ita wanan halintane gori da rashin kunya So ka barta don Allah. Ranshi dai ya baci amma ya kasa magana don yasan halin matan nasa sarai kome akace tazo tayi zata iya don yar rainin hankalice ita. Bai jima ba ya fice daga falon zuwa part dinshi shima ya Habu din ya fita saida mama ta tambayeshi koya leka asibiti ? Naji yace ai can ya jima daya shigo gari can ya fara zuwa ya dubasu kafin yanzo gida nan yake fada mata cewa likitocin sunce jibi zasu shiga da ita suyi mata scaning a duba lafiyan cikin ta din. Washegari kamar kullum ban fito da wuri ba kamar jiya daine kodana fito a falo na samesu ana ta kasafin kayan shayi da abubuwan more rayuwa na dan adam a falon . Nagaidasu nashiga kitchen har lokacin kayan da akaci ya rage suna wajen ba a samu wace ta saka a cikin fridge ba dole na tsaya tunda miyar baiyi komai ba na adanasu a cikon fridge din. Rahama ku karbi key kukai min kayan nan a part dina ya habu ya fada nida salima muka kwashe kayan a hanya take fada min wai ashe ? Jiya ya J sunyi fitana sosai da Saiba har ya mamareta yana fadin sai ya sake ta don ta isheshi tana son jawo mai matsala da yan uwansa. Ina gyaran falon take fadin ai har Saare yau mama taci mata mutunci sosai da safe tace ta daina shiga part din ya J din tunda duk tsegumi ya taso da sunanta a ciki. Wayanta da mama ta kira tana tambayanta ina muka tsaya gashi tana jiran mu mu mikawa makwabta munje can mun zauna take fada mata Ramaah ke gyarawa yaya part din. Bayan mun dawo muka dauki kayan da aka warewa makwabtansu niki niki muka shiga gidajen muka bayar ba hutu kuma muka dauki na tudun wanda wanan ya habune ya kai mu da motarshi muka ba kowa nasa ana saka albarka muka fito daga unguwar. Ranan kan bamu iya komai ba sai mace tayi muna abincin buda baki ita da Saare saboda mun gaji sosai a ranan wajen raba abin buda bakin da ya J ya rabawa yan uwa da abokan arzkin su tunda mune kamar yara a gidan. Sai bayan shan ruwa a buda baki iya ta soma magana tana fadin gidan nan kan ranan da yarinyar nan ta barmu zamuji daban . Yau kadai har munyi kewan girkin yar nan to iya kina nufin ni bam iya girki ba ke nan shiyasa bakici ba saiga mama kuma na fadin ke salima jeki kitchen ki dumama muna miyar jiya wanan kan ina zai ciyo ga yaji ga gishirin tsiya miya kamar an wanke kan mahaukaciya haka ? Fushi anty Saare din tayi tana fadin ita shiya bata zama duk abinda tayi yanzu sai ace bai yi ba Ramaah ta fisu iya komai.
Chapter 50 · 0% Book details