← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 306

Sashe 60

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ana hada hadan shan ruwa a lokacin. Baya bata da kadan don ko tana fita ba,a jima ba ya iso gidan bai tsaya ba ya sauke abinda ya sayo a hanya ya nufi cikin gari don samun sallah a unguwarsu inda suke shan ruwa. Maigadi ya jido kayan zuwa part dinsa dana iyayyenshi iya take tambayan maigadi ina Jafaru ? Yace ya fita yanzun nan kayan kawai ya sauke ya juya ya fice daga gidan ba zai shigo ba ai tunda yasan abinda ya aikata uwar ta fada. Keko meya aikata kuma ba zancen ki bane asalima nasan saboda ke yaron nan yake son daukan mataki tunda kinji wayan da sukayi da dan uwasa don haka ki sa masu ido kawai yayi iko da iyalinshi. Yarinyar nan tana bukatan gyara a gaban mu tazo tana zagin yarinyar nan koke maisa ya dauki matakine kan abin nan data aikata ai. Shawaran Iyan mama tabi don koda Jafar din ya dawo batayi mashi zancen ba shiru tayi har ya gama hiranshi da iya ya nufi part dinshi. Takaicine ya kamashi yadda ya samu fslon nasu a ya mutse ga kujerun falon da basu dauki wani lokaci ba a gidan har sun fara ya mutsewa da auren Yanda ya sayo masu shi da akai gyaran gidan. Abin takaici ranan daya shiga falon Habu yaga nasu zakice ranan aka kawo masushi part din don komai ba suyi ba sai walkiya da sukeyi. Takaici ya kara kamashi haka ya taka zuwa dakinsa ga wani bashi dake tashi ba alaman ma tayi wani soye soye don shan ruwa a ranan. Yana gab da shiga dakinsane yaji muryanta a bayanshi tana fadin ai kadowone ashe na dauka ba yau zaka dawo ba ai naga Saiba ta tafi kaduna da yamman nan ? Bai tsaya bata amsa ba ya murda kofan dakin ya shiga ya rufo sai lokacin ya shaki kamshin dakin don ko yaushe shike tsayawa ya gyara abinsa yadda yake son ganinsa. Kayan jikinsa ya rage yashiga wanka yaso ya kwana a Abuja saidai saboda ya kure saiba ya dawo zaria a ranan tayi arziki daya dawo ya samu tabar gidan don daya shayar da ita mamakinsa a ranan. Why zata zargesa da irin wanan mumunan abin ta rasa wanda zataiwa sheri irin wanan saishi kuma ? Dashi dan iskane yadda take zato akanta zai fara nuna halinsa ai amma sai ya juya abin zuwa aure a tsakaninsu tabbas itace da farko ta fara nuna mashi so da kauna . Don tun bai gane ba har yazo ya fahinci me take nufi da farki yaso ya guje mata amma ta hillanceshi da dadadan kalmanta har yaji ya kamu da kaunanta itama saboda yadda take matukar bashi kulawa zakice ko itace matar nasa duk a lokacin ta fake ga besty dib Asmau take masa wanan. Tsoki yaja lokacin daya murda famfon ruwa ya kare hakan ya tabbatar mashi da ta kasa fita ta kunna ruwa ke nan a ranan . Dole yayi amfani da ruwan roban da suke tarawa acikin kyankyami saboda ruwan ya dade a rufi bayan ya fitone ya shirya kansa bai fito daga dakin ba nan ya zauna bakin gadonsa yana waya da wani mutumi da zasu hadu dashi a Onicha. Tashi yayi ya sakawa kofan key yana mai jin haushin matan nasa aransa a haka barci ya daukeshi don koda Asmau tazo tana murda kofan duk yayi barci a lokacin. Sai tsakar dare da yunwa ya tayar dashi irinta wanda ya wuni da azumi a cikinsa hakan yasa dole ya fito ya duba falo ko zai samu abincinsa aje sai dafa duka da ganye. Kitchen dinsu daya dade bai shiga ba ya nufa a can ma ya kwammace da bai shigo kitchen din ba a lokacin don kayan takaicin daya sama a kitchen din. Drinks ya dauko a fridge sai bread dashi yai sahur ya kwanta cike da takaicin duniya akan matan nasa. Idan kaga Asmau a zahiri zaka dauka mace ce mai tsabtan bala,i don iron yadda jikinta yake ashe abin ba hakana bane halittace kawai a hakan . Ita kuma saiba datayi mai dadin baki tana da dan dama saidai ba sosai ba ga kuma cin mutunci har na tsiya a bakinta. Abin yana daure mashi kai yadda mace tayi boko zata tsaya tana wanan kazantar haka sai wace batayi karatu an koya mata tsabta ba tafita. Da safe kuma asubanci yayi yabar garin zuwa Abuja inda ya shiga jirgin zuwa Rives don haka koda mahaifin Nusaiba ya nemeshi baya gari bai sameshi ba. Saarece wajen binciken ta ta dauko kayan nan da matan ya J suka dawo min dashi a cikin kayana tana nunawa mahaifiyarsu. Tana fadin wai mama kinsan yarinyar nan ashe bata dauki ko tsinke daga cikin kayan nan ta tafi dashi ba. Yanzun nan ina neman gyalena na gansu a kayan ta yadda aka bata haka ta ajesu a nan din bata dauki ko tsinke daga cikin kayan ba. Haba dai Saare yanzu bincike kikai mata a kayanta kema kinsan babu gyalen ki a kayan Ramaah wace take hada muna kayan mu itace zata daukar maki gyale kuma ? Mama yarinyar nan tana min katsalamdan a ciki zancena kwanan nan wallahi idan tana min hakan za a jimu da ita. A cikon takaici mama ta juyo tana fadi rufa min baki mara hankali ai gaskiya ta fada inba rashin wayau da tsegumi ba meya kaiki cikin kayan yarinyar nan yanzu don Allah. Wanan wani irin dabi,ace Saratu ina kula dake a gidan nan idan nabi ta naki yarinyar nan so kike ki hadani da yaran nan sam bansan meyasa kike haka a kansu ba. Haka yarinyar nan dake asibiti tun tana tambayana ke har tagaji ta kyale ta daina tambayanki kwata kwata a yanzu kinki zuwa ki gaida ita. In habu ya gane wana halin da kika tsiru nasan ba zaku kwashe dashi da dadi ba tsorona Allah a yanzu kada sunan ki ya fito cikin zancen yarinyar nan Nusaiba. Don ban tantama idan ba kece kika fada mata cewa yarinyar nan zatabi yayan ku ya sauketa a Abuja kika haddasa wanan fitinan a tsakanin su. Kallon uwar tayi tana fadin haba mama ni ina naga Nusaiba a ranan balle in fada mata ga Ramaah zatabi yaya idan ma kece ai ji zamuyi don Nusaiba fada zatayi kin sani. Wanan ai shashancine jafaru din ta zarga ko wanan yar komu ta dauka bamu san abinda mukeyi ba lamarin wanan yar yana ban mamaki ke kinyi kwancen mijin nan hannun kawarki kuma ki koma kina nuna kowa bakya son yai mu,amula dashi saboda me hakane wai ? Har kizo kina neman batawa mutane suna akan abinda bashi ba isan wani yaji wanan shirmen ai zancen zai juya wani abu daban kuma ? Iya na sauke zancen mama ta dauka da ai yanzu tagani nafi da son ya gani ko yaji ya dauki mataki da kansa kada ace na zubawa yara ido na hanashi zaman lafiya da iyalinsa amma yanzu ai zata gane uwa nake ga jafar. Tsuki iya taja tana fadin yaushe kuma ai tun za a ake shiri ba sai anje ba kin rigada kinyi kuskure tun farko ya kamata ki nuna ke uwace agaresu . Amma haka kike shaye duk wani wullakanci akan yaran nan kuma ki hana mijinsu ya dauki mataki akai waike kada a zargeki. Yo an dade ba a zarga din ba da wanan halin da yaran nan suke sakaki ciki a kullum wana karon dake dasu kunkai yaron nan makura don haka ki barshi ya dauki matakinsa ido kawai zaki zuba masu tundama baison zancen dake iyace tasa mama a gaba cikin fada ganin yadda ta daga hankali wai ga sallah ya gabato ga azumi ya tura yarinya gidansu. Abuja Rayuwan gidan anty sallama rayuwace ta turai tsantsanta don sai ankai karfe dayan rana kowa na dakinsa kwance ba a fito ba. Sai hakan ya zama min bakon al,amari a wajena don saboda wahala da jikina ya saba dashi na ba hutu gareni da zaran karfe hudun asuba ya buga. Don hakane a bangarena ba barcin na koma ba don ban saba da hakan ba idona biyu ina dai kwance ina faman tunanen duniya. Hakan yasa na jawo wayan nan na kunna ina shige shige a cikinsa har na fara gane kan wayan don ban san kan waya ba a lokacin gaskiya. Ban kuma damu da insani din ba don waya bai gabana a lokacin tunda nasan ba zan mallaki waya a lokacin ba kila sai gaba kamar yadda anty Yanda tasamu sanadiyar yaya Habu. Amma sai gashi nice da wanan wayan dake hannuna da yazo min a bazata wayan da kana kallonsa kasan babban wayace ba karamar waya bace bakace wulk da ita. Taba can tabo nan har na gano abubuwa da dama game da wayan na shagala sosai a lokacin har anty sallama ta shigo dakin bansan lokaci yayi ba na yarda da wasu ke fadan waya kanin shedan . Tabbas haka yake don ko sai gashi ya mantar dani duk wani irin damuwan dake zuciyana lokaci guda har na shagala da dakilanshi. Ramaah aina zata har yanzu barci kikeyi muryan anty salma naji a tsakiyan dakin har ta karaso bakin gadon da nake kwance rub da ciki. Na dago ina aje wayan tare da gaida ita da kwana duk da wunine lokacin ba kwana ba amma tunda ban gaida ita da safe ba dole na kira hakan da kwana. Lafiya Ramaah ta fada tana zama tare da tambayana i hope ba matsalan komai dai nace a,a anty. In kina da matsala fa kiyi magana flee free don Allah nan gidankine fa idan kina da damuwa ki fada kawai nasani ? A,a ba komai tace Ok akwai wasu perfume na dade da sayan su da kayan kwalliya ban amfani dasu ina maji har na aurena akwai a ciki idan kin fito sai ki duba ki zabi iya yadda kike so kiyi amfani dashi. Kinsan ni nafi son naga mutun so clasic ba irin yadda kika koma din nan ba anyi mace haka duk da azumine babu dan gyaran jiki haka Ramaah ? Ki gyara jikinki tsab ki saba da hakan ko har kin manta da tarbiyan mamace wai kinsan mama
Chapter 60 · 0% Book details