← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 173 OF 306

Sashe 173

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rayuwa kenan haka take tafiya da dadi ba dadi ga dan adam amma idan ka saka hakkuri ka dauki komai a saukake sai Allah ubangiji yasa abubuwa su dinga zuwama a cikin sauki ta yaddama baka zata ba. Haka shima rayuwan aure ya kumsa garemu mata idan kina tausan zuciyarki akan kishi zakiga abubuwan suna zo maki a cikin sauki matuka zaki daure ki ba komai baya ki dauka a ranki cewa aure bautan ubangijine a gareki. Hakan ya kasance a rayuwan auren dana tsunci kaina a cikinsa na yaya Jafar auren da bantaba zato ba ko tsamani nasa akaina. Haka kuma nake daurewa da duk wani abinda zasuyi min dashi da matanshi ina nuna ba komai bane hakan a wajena. Idan yazo wajena mijina idan ya koma gidan matansa kuma mijinsune ban damu da irin rayuwan da sukeyi a can ba dasu din zan kawar da kaina ba tare da son sanin yaya yake ciki dasu ba can ? Duk da yan tsegumin da nakan tsunta nasu abakunan dangin miji cikin zance hakan ban yarda na sakawa zuciyana damuwa akansu ba. Bazance bamu haduwa ba mukan hadu can ba a rasa ba don ina zuwa ganin yar uwata a gidan kuma saiba bata daina kawo muna hari ba da sunan kishi. Balle yadda na dauki lokaci ban samu ciki ba shima wanan din ya zamo kamar abin gorine a wajenta don takan sakar min magana a kansa wani lokaci. Yau,ma daga school nan na nufo don in duba yar uwata dake fama da laulayin ciki a cikin yan kwanakin wanda hakan ya zamo mata dabi,an da zaran ta samu ciki babu zaman lafiya a rayuwanta ke nan. Don ko yanzu likita yace dole sai tayi zaman asibiti irin wancan din da tayi a baya donshine nazo gidan muyi shawara da ita don ni ta fara nema da zancen hankali tashe. Yunwar dake cina yasa ina shiga na fara neman abinda zan aikawa cikina agaji dashi tace na duba fridge dinsu ko zan samu abinda zanci a ciki . Yoghout din Rufaida na dauko da cake na dawo saman kujera na zauna na bude ke nan yaran su saiba din suka shigo part din. Sun biyo dan wajen Yanda suna wasa ba zance yaran basu sanni ba saidai babu sabone yanzu sosai tsakanina dasu kamar da amma don sani sun sanni ai. Haka kuma kowa yasan yaro da daukan ido idan yaga wani abinci a hannun wani hakan yasa na rasa yadda zanyi saboda idon da suka zuba min din ga Rufaidan dake hannuna ina sha. Banda kyakyamin yara donshi nake diba ina basu a baki wanda hakan yayi daidai da shigowan Saratu part din tazo amsan hairdryer a wajen yar uwata din. Haka kuma bata sanda na shigo gidan ba sai a lokacin don banshiga wajensu ba tukunna na nufo wajen yar uwata din. Har ta karba zata fita sai kuma ta dawo baya tana fadin jimun yan iskan yara da saka idon tsiya me kuka rasa a wajenku da zaku dawo nan ku rufawa wanan abin ido haka ? Tsawa tayiwa yaran suka fice a cikin kuka nace da kin barsu ai munsha tare aini na basu bata ko tsaya kallona ba ta fita a fusace ta tasa yaran gaba. Sai bayan sun fita naji maria tana fadin yanzu wanan abin ya isa uwayensu jidali bansan meyasa saratu take halin nan ba ko shigowa yaran nan sukayi sai tayi masu jan ido akan su fita zakice ina masu wani mugun abune a nan. Kyaleta kawai neman maganane irin nata idan da sabo ai yaci ki saba da halinta bata so a zauna lafiya ita ko kadan dama. Na mikawa Abbanta roban gaba daya na gyara zama ina fadin yanzu yanda dolene sai asibiti zaki zauna ? Ba zaki zauna gida a dauko maki wace zata kula dake ba ninaga kamar hakan zaifi sauki da zaman asibitin nan tunda kinga dole wancan karon ummah ta zauna dake yanzu ko ummah tana da aure. Idan ance tazo ta zauna akwai takura acikin hakan yana da wuya mijin nan nata ya yarda da hakan gaskiya. Tace Ramaah abinda nake tunane ke nan mama dai yanzu kinsa ba dadi a tsakanin mu don tunda ta kula da cikina samu nake wanan wahala naji tana fadin. Ai hakan ya zama takura ace duk ciki sai an wahala dama abinda akewa yaran nan gudu kenan kaje ka daukowa kanka wahala yanzu gashi abu ya zamo fitina wa zai iya wanan wahala ace duk ciki sai mace taje tayi kwance ta mike kafa asibiti. Dama ai kinsan zata fadi har abinda yafi hakan ai tunda ba yan sonta bane sukayi hakan kofan da aka turo a fusace yasa duk muka juya lokaci guda. Ita kanta a yadda ta shigo din ta samemu saida ta raina kanta don jikinta saye yake da wani dogon riga na atamfa baki daya kode. Roban youghot din dake hannun Abba yana sha ta kalla ta soma fadin ai dama nasani akan wanan tarkacen kwadayin zaki mayar muna da yara kamar marasa galihu ? Haba dai anty Saiba meya kawo wanan maganan kuma anty Maria ta fada cikin tsawa take fadin don Allah rufa min baki kinji malama. Shi Rufaida din inba abin yaro ba nawa suka sha da zasuzo nan ana yan masu a hannu kamar wasu almajirai dasu ? Ku ya zamawa bakon abu har kuke kwadayinsa koda yake ba abin mamaki bane don ba asaba ganin hakan ba sai a nan din ake samu kuma dai kudin ubansune dai ake ci ko saukin abin ke nan dai daga yau bance wata ta kula yata ba balle a bata wani mugun abinda za a sabauta min ya in rasa gane kanta yadda akaiwa ubansu. Wanan kuma ke kika sansa ai don bamu gaji mugun abuba balle muyiwa yarki don baki tsarewa kowa komai ba balle yarki To mara kunya nasan idan ita bata tanka ba dama ke zaki tanka ai nace kwarai tunda ba tsoronki nakeji ba kuwa baki da wuta baki da aljannan sakani akan me zanji tsoronki Saiba ? Kazan uba nice ma Saiba haka gatsau a bakinki nace kina da wani suna da yafi hakan ne a bakin mutane Nusaiba. Na fahinci sanyin da yar uwata keyi masu ya jawo raini a tsakaninsu tun ina gidan wanan yasa a yanzuma nake son in kakabe hakan a tsakanin mu tun a yanzu din. Idonta ya fifito na masifa ta soma jefa muna zagi na wullakanci ina rama abinda take fada min din cikin hikima da nasa mata bakin ciki a rayuwanta dama ance magana zaran bunu. Nasam karshe tace zata dora min hannu a jikina don haka takewa kishiyarta a baya nasani kuma hakan yasa tunda naga tana nufoni na mike tsaye cikin masifa nima ina jiran karasowanta a kaina. Sai fadi take yau zan murji rashin kunyar nan taki da kyau dana jima ina jiran wanan ranan zan gwada maki nafiki iskanci ke karamar yarinyace wallahi . Yariya ai tana bayan uwarta kin sani nikan ai daidai nake dake saiba kafin hannunta ya sauka jikina don yanda data shiga tsakanin mu hakan yaban daman samun shammatarta nakai mata wawan mari a tsakiyar fuska tauuuu. Saida ta duka kasa kokarin kare yar uwata don kada mu illantata nayi nakai gareta muka hade ana gwadawa yar filo mai kiwo a daji kokawa ? Ai kunya garemu badai tsoro ba sai gashi Allah yaban sa,a na dagata sama na zuba saman kujera nabi na danneta ina aikawa fuskanta naushi a iya karfina da bansan na saura dashi ba har lokacin . Ihun yanda ya fito da mutanen gidan mama a rude babu kallani akanta tana rige rige da yayanta suka nufo part din cikin tashin hankali. Salimace ta soma fadin ayya girma ya fadi ke Rahama daga mata hakana don Allah garin yaya haka ya faru kuma yaushe kika shigo gidan nan ma inji mama ? Jin abinda suke fadi din yasa na daga akanta ga idanuwanta sun firfito waje tana haki ta soma fadin wallahi ba zan yarda ba yau gidan nan za ayi bala,in da ba a taba yiba kuwa kun tarar min ke nan ? Da keda yar uwarki ko nace kunji munafuka har me za a tarwa anan mace haka kamar faifai ba nauyin komai nidai din da kikace zaki murza na murjeki son raina yau din. Tayi kukan kura akaina tana fadin wallahi baki isa ba kizo har gidan nan kice zakiyi min haka karyane wallahi na tattare bujena zuwa gwiwa don kada ya takura min nako here hannuna nakai mata wani naushi sai a gefen fuska duk suka jaye baya dama salima da Asmauce ke rikeni mu din don sunfi kusa damu. Na kara samun sa,anta na taushe a kasa amma wanan ai zaluncine ku dagata mana tunda kunga bata in mata kun tsaya kuna lallonsu kuma tana dukanta ? Saarece ke fadan hakan cikin hasala tayi kaina wai zata dagani jinta kasa yasa ta kai min duka nako juyo na aza mata duka iya karfina saida ta saka ihu tana fadin kika dukeni Rahama ? Keda kika dukeni fa ina can ina bata amsa ta samu sa,ana ta kai min cizo a hannu tana dagowa na koma na kaimata shaka a makogoranta ta soma kakarin kamar zata shude. Haka na zama masu yar daban gaske a gidan inkaiwa saratu duka inkaiwa saiba maria ta dora hannu akai tana kuka duk da suma suna dukan nawa amma Allah bai basu sa,ata ba yadda suke so don na fitarwa kowa da jini . Saida kyat mama da su salima suka samu rabamu fadan salima ke fadin an daiji kunya yau tunda har kuka tararwa mutum daya ke Saare meya kaiki shiga fadan su don Allah ? Ke rufa mana baki mama ta fada a cikin tsawa tana fadin mara zuciya kawai da iya fadan tsiya ki tsaya kina kallo kin kasa rabasu daga rabon fada zata hau yar uwarki da duka haka kina tsaye ? To mama so kike mu zama daya meyasa takai mata duka haka ake raba fada kakaiwa mutum duka muko muna can muna aikawa juna zagi na tashin hankali ido a rufe duk a gabab mama din data kasa komai
Chapter 173 · 0% Book details