← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 306

Sashe 66

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Satina biyu Abuja na dawo a cikin mutunci tare da goma hataran arziki da mama da anty salma suka hadoni dashi. Nida naje da jakka daya karami sai gashi na dawo da jakkuna maya har biyu makil da kaya na mutunci da alfarma ire iren kayan anty Salma da sakawa daya wasuma ko sakawa batayi ba wai angama yayinsu a wajenta. A part din Iya na sauka don part din mu yana rufe sun nuna farin cikinsu da dawowana musan,man iya daketa fadin yar nan muji kewanki sosai a gidan nan . Gamu gida ya koma muna wani iri sai kace taron tsofi ba don zuwan Iyatu gidan nan ba aida bola ya rufemu tas don babu wanda yake iya gyaran gidan nan yanzu. Iyatu na samu tazo ta wuni min idan zata koma na hadata da abinci da kudin mota a raina nace yanzu ko ga boyanku ta dawo bako zan hana iyatun nan cin abincinta ba gaskiya. Saare ce tana shigowa ta ganin zaune gaban mama sai tarin kayana dake tsakiyan falon turus taja ta tsaya tana mamakina budan bakinta sai cewa tayi wai Ramaah ce haka ? Wanan da kinkai wata daya aiba zamu ganeki ba ke nan kin koma wata wise haka lokaci guda haba dai kamar wace aka saka ga injin . Gaida ita nayi ta amsa tana zama lokacin kuma naji mama dana hango damuwa a fuskanta tana tambaya yaya ya samu harci kuwa ? Wallahi mama baiyi barci ba yana nan dai kwance nasan ciwon ya lafa mashine amma ba barci a indonsa fuskan kowan mu tausayi ya nuna mukai mashi fatan samun sauki. Dagawa nayi na fara jidan kayana ina kaiwa dakin kwanan mu lokacin naji saaratu na fadin wai mu hudu kenan zamu zauna daki guda yanzu ? Ta sauka a dakina kafin yar uwarta ta dawo mana iya ta fadi hakan ba karin digo Saare ke fadan waiki kai kayan ki dakin iya mu ukune yanzu a dakin anty nafisa tana nan tare damu. Jin hakan yasa na juyo cikin mamaki tace dakin iya zaki kai wanan shirgin naki da kika kwaso ku kara cikin nata naji mama ta dan dubeta cikin damuwa tana fadin banson iya shege Saare. Kikai kayan naki dakin iya ku zauna tare dakin kunyi yawa yanzu nafisa na nan tare damu saboda ciwon yayan ku. Dakin iyan na nufa da kayan nawa ba laifi dakon don a gyare yake tas nasan wanan iyatun dake zuwa yanzu ke gyaranshi amma dai akwai shirgi a cikinsa yadda saare ta fada a gefe daya na tara kayan ban fito ba nashiga bayi donyin alwala saida na tsaya na tsabtace shi na samu nayi amfani dashi nafito na tayar da sallah. Kodana gama na fito ban samu su mama da iyan ba suna wajen dan nasu dake fama da jikinshi a lokacin. Tare da Salima da Nafisa muka shiga part din don gaida dan uwan nasu a can muka samu iya tare dashi suna magana matansa duk suna zaune da yaransu daga mai waya sai wace ke shan wani abu acup. Gaidasu nayi na isa wurinshi ina gaidashi tare da mai sannu da jiki ya dago ya kalleni cikin karfin hali ya soma fadin kin dawo ke nan ya kika barsu can ? Lafiya kalau yaya ya karfin jiki kuma gabana saida ya fadi don yadda ya dago kai mukayi arba dashi wurin ramin idonsa yayi wani iri na ban tsoro. Bansan lokacin dana kai gurfane ba gabana yana faduwa a yadda ya kalloni ya rame wajen idanunsa sunyi wani baki saboda azaban wahalan da yake sha a lokacin. Ba zakice yaya jafar bane wanan dan gayen dana tafi na bari a cikin lafiyan shi ko ince wanda ya kaini abuja sati biyu da suka wuce da kafansa ba. Sai ki rantse da Allah wanan din ya jima yana ciwo a kwance ba Jafar bane ya koma haka a cikin sati biyun sannu yaya ashe jiki kuma ba dadi haka ? Hannunsa yakai a kai yana dafe goshin tare da fadin da sauki a wahalce bansan hawaye suna zubo min ba saida naji Salima na fadin aiki bar kuka Ramaah jikin da sauki sosai yanzu ai Ramaah. Nidai zance har muka bar part din bawan Allah nan baya cikin hankalinshi saidai idan an mashi sannu ya amsa da kai koda hannu baiko iya magana. Gashi kuma suna fadin wai ai hakan da sauki sosai don dai shi musulmi da dangana aka,sanshi ko wani lokacin bayan hakan baga ta inda saukin yake ba. Allah sarki kallo daya zakiwa Mama da yaya Habu kiga tashin hankali karara a fuskokinsu yanayin gaba daya nasu ba dadi a yadda salima ke fada min yaya Habu da kawu dauda suna hanya ko yaushe cikin tashin hankali wajen malamai. Kai duniya ina zaki damu mutum kamar yaya J mai alheri da mutunci ga duk wanda ya sani yau kuma shine aka jeraba da wanan lamarin . Sunce anje asibiti har angaji ana cewa ba aga komai ba amma za,aje sakoto ko ibadan a aunashi don suna zargi a kwakwalwanshi abin yake inji likitawa. Ranan monday zasu tafi talata ake awon yasa zasu isa tun monday din don suje ayi booking kamar yadda aka shawarcesu. Nisawa nayi daga inda nake zaune a hankali na furta wanan ba juttoro bane a yarenmu ban zata wani zai jini ba lokacin. Sai naji Nafisa tana fadim meye juma juttoro Ramaah ? Nace a,a magauta nake nufi da hausa magauta kuma ni ai kin kara jefani a kwana Ramaah ? Kukan dai yaran yanzu baku san hausa ba magauta masu bin duduniyar ka take nufi koda ance hakan ne ai ba a mussawa iya ta fada. Iya idan hakane nima dai bance a,a ba don ko a cikin gidan mu kullum a cikin hassadan su yaya ake duk da alherin da suke aikowa ana karbewa kuma ayi lalura dashi. Amma da an bada baya zagine ba godiya ba yake biyo baya a zagi mama a zagesu ana binsu da sheri ni yanzu na hana inna shiga tare fadan suje suyi tayi donsu ke komawa baya a kullum Nafisa ke fadan hakan. Abinda nake fadawa dubu ke nan kullum amma tasa kada ta toshe kunnen yaran da suka taso tun suna kananu ake binsu da sheri meye ba za a iya yanzu akansu ba Allah dai ya kyauta kawai za ace. Kin dauka don dadi ake shan tsamiya akwai dafa,in sanmu a cikinsa idan kana amfani dashi lokaci lokaci yana da wuya wani abu ya samu jikinka. Hirana da Dage dan baffa da nake tambayansa a wurin kiwo maiye amfanin tsamiyane wai da mutane suke ta dibansa suna kaiwa birni ? Washegari ganin yadda mama tayi laushi da yawa yasa na shiga kitchen don na dama mata kunun tsamiya a hautsane na samu kitchen din komai ya barkace a cikinsa saida kyat na gano ledan tsamiyan na dauko na wanke na jika. Har na gama damawa suna zaune da kawu dauda suna magana na hado cups biyu na fito falon dashi na aje gabanta ina fadin mama kunun tsamiyane na dama ko zaki iya shansa. Allah dai yai maki albarka Rahama yau kusan kwana nawa ina son in tsaya indama na kasa samun sukunin hakan. Naji kawu shima yana fadin a zaba min na dansha don Allah ai abin marmarine saidai kunun da zafi hakan yasa tace don Allah in biyota dashi part din Jafar kila shima a samu yasha kunun. Ban fita ba saida na zubawa iya na dauraye kayan na fita na hango wanan matar iyatu tana faman sharan tsakar gidan ga girma ga shekaru ina zata iya tsayawa tayi yadda nake masa tsab. Nikan na fito na nufi wajen ya J da kunun don bata kusa dani balle in gaida ita ina saka kafa ina jin muryan saiba na fadin don ina kin rigani shigowa zaisa aje dake idan na shiga motar gobe kisa in fito. Saiba na fada maki idan banje ba kema babu inda zaki gidan mu zauna gaba dayan mu a gida don ba fina kikayi ba da za a tafi dake a barni. Wai menene haka don Allah har mijin ku yana kwance ba zakuyi ladab ku natsu ku komawa Allah ba sai yaushe zaku girmane wai don Allah ? Mamace ta leko daga dakin ita da kawu jin hayaniyan da sukeyi falo wai ashe cewa kawu yayi mutum daya daga cikinsu ta shirya gobe aje sokoto da ita sai Asmau tace ita zata wanan yakawo masu hayaniyar a tsakaninsu. Ni dai ina tsaye saida kawu yace shigo muna dashi nan kinji yar nan wanan ne kuma karo na farko dana taka zuwa dakin part din shi maigidan nasu. Yana kwance shida wani abokinsa dake zaune saman kujera na gaidashi ya amsa ba tare daya dago kai ba na aje kawu ke fadin a dan zubama kunun tsamiyane ta damawa dubu ko zata gyara bakinta a zubane kasha Jafar ? Sai lokacin ya sauke hannunsa daya dafe kai yana fadin a zubo kadan kawu kawu ya dan kalloni yana fadin zuba masa ko Allah zaisa ya yasha din. Yana da zafi kunun don haka na tsaya na dan huhuta masa na mike zuwa wajensa ina fadin yaya ga kunun da kyat ya sauke hannunsa yana kokarin karban kofin faga hannuna. Abokin nasa ya taso da sauri ya karba yana bashi yake kurba a hankali yayin da nida kawu muka zuba masu idanu sai ya shanye tas ikon Allah Allah dai yasa ya zaunama a ciki. Amin amin abokin ya fada na fito da cup din na dauraye wanda aka kwana dashi cikin wani hali sai gashi ya fara karyo zufa a jikinsa. Mama dake shigowa ita da iya da suka gama rabon fada take fadin ikon Allah meya faru yake zufa hakane ? Kunun nan da yarinyar nan ta dama aka zubaf mashi shine yasha yake wanan zufan haka Allah dai yasa ya zauna mai a cikinsa. Na dawo da kofin dana daurayo yayi yunkurin amai suna fadin subbahanallahi aman dai yana nan ke nan sai ya koma ya kwanta ya daina yunkurin da yakeyi da farkon na aman. Sannu a hankali yayi lamo a yadda ya dan kwanta din ganin haka nikan na
Chapter 66 · 0% Book details