← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 221 OF 306

Sashe 221

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nayi kuka har nagodewa Allah a wanan ranan daya zamo min kamar na tonon asiri a wajena ranan da nake jin kamar kasa ya bude inshiga saboda kunya daya lulubeni a lokacin don hakan ya zamo kamar wani bakon lamari a society ake gani. Yayin da miji yake kwance a lokacin ni kuma Allah ya nufeni da samun karuwa dashi karuwan da nake jin tankar i hadiye raina a lokacin . Wanda bake jin tsanar mijin fiye da kowa don ina ganin shine ya kaini ga wanan abin kunyan a yanzu wanda a sanadin haka har ya barni da nauyi da kunyar iyayyena. Wanda ko kafin su daddy su wuce a ranan saida su kai ta zolayata a bakin mota ina hawaye badai kamar anty Salma dole ganin yadda nake kuka yasa takai ga rikeni a lokacin. Haka suka tafi suka barmu a cikin tausayin mu don sun fahinci muna zaman hakkuri a wanan gidan gidane da baida alkibla baida tsayayyen babba da zai tsawata akai yaran maza sune tsaye da gidan kuma su din dai tunda akwai uwa da kaka dole komai zasuyi akwai taka burki da tauyewa ga irin zaman nan. Zamane da wasu iyayye ke zabawa iyalinsu don gashin kan zuciyarsu su wanda akasari ya sabawa al,ada da shari,an mallam bahaushe. Zakiga iyayye masu irin halin nan suna nisanta iyalen su da yan uwa suna kamesu daga shiga dangi ko wani harka na zununci wanda uwace zata zauna ta dinga shimfida doka iya son ranta ga zurianta. Irin wanan rayuwa muka tsunci kan mu a cikin gidan nan matukar ba naku yazo daya ba da irin matan nan mata da yawa suna fuskanta bacin rai a zaman aurensu koda ya kasance kuwa miji na aon matarshi uwa ba zata bari a zauna lafiya ba irin haka aji dadi. Abin mamaki na zata maria zata dan zauna dani ta kara min shawara ina tsaye wajen bayan wucewan su daddy saiga Habu ya fito yana cewa da ita muje ko tsayuwan nan kada yai maki yawa. Haka suka shiga mota suka tafi suka barni ina kallonsu a cikin mamaki har suka bacewa ganina naja kafata zuwa ciki inda na samu mama da iya zaune a falo suke fadin Allah sarki mutanen kirki sun tafi Allah ya saukesu lafiya. Amin kawai na iya fada na shiga dakin yana kwance shi kadai a dakin yayi shiru yana kallon saman dakin yanayin kwanciyarsa zai nuna maka cewa ya shiga zurfin tunane a lokacin . Kwanciya nayi ba tare dana kallo inda yake kwance din ba nima na fada nawa tunanen muna wajen a haka har aka kira sallah magariba. Na mike zuwa bandaki na hado komai da nake mashi alwala na fito saida nayi mai ya tayar da sallah nashiga na dauro alwalata nima na fito. Falo na koma ranan nayi sallah haka kawai nake jin tsanarshi na karuwa a zuciyna ina zaune ina addua wayata ta dauki kara bayan na duba naga ummah ce a layin lokacin na dauka take fadi bayan mun gaisa. Ramaah yaya na batku dazun kiyi hakkuri kinji kowa da tasa kaddaran kar kiyi mamaki duk sanadin wanan cikin Allah ya kwantar da mijinku jinya irin haka saboda hakan kawai ya faru a tsakani ku. Wani dan, taurine dashi kafin yazo duniya sai uwa da uba duk sun girgiza wani lokacin ubane kan fara laulayi da jinyar ciki kafin a sakawa uwa ta karasa saukin haka manya suka fada. Ance sai uba yayi jinyan fitar da kwansa kafin ya samu ya fito daga jikinsa kamar yadda mace kanyi wahalan haihuwa suma maza din suna da tasu jinyar kalan fitar da kwai a jikinsu. Don haka nake ganin duk wanan jinyar kamar ta wanan halittan dan da a yanzu kuka samune dashi sai kiga in har hakan gaskiyane a cikin yan kwanakin nan insha Allahu mijin ku ya samu lafiya ya mike kamar bashi ba. Ta jima tana rarashina kafin mukai sallama ina aje wayan kiran mummy yana shigo min a wayan na daga itama din dai hakkuri ta bani kamar yadda duk wani masoyina iya hakkuri zai iya ban a yanzu kawai don dama shi muka gada tun kakanin a arewa. Na dai idar da sallah ina zaune naga shigowan mahaifiyarshi hakan yasa ban damu dana koma ciki ba na zauna a falon abina ta jima a ciki zaune kafin ta fito da bacin rai ta fice daga part din. Ikon Allah naji maman tudu ta fada daga bayana don iya bata falon namu lokacin zuwan Yazid da family shi yanzu bata faye zama damu ba ko yaushe. Amma akwai aiki a wanan rayuwan kice komai yaro keyi da iyalinsa idon ki yana kai a wanan zamanin ka kawar da idonka ma yaya aka kare dakai balle kace saka ido zakayi. Dubu tana da wahala a rayuwanta zancen nan da mutumin nan ya fada shine yanzu take faman hasala akai duk da yaron nan yana kwance bata duban hakan ita. Saida ta sameshi da wanan zancen bata duban zancen nan bana yau bane balle ta duba halin da dan nan yake ciki ta tausaya mashi ga hakan. Amma wai haka dubu ta rutsa yaron nan yanzu akan zancen nan dubu sam bata kaunar diyanta suna alheri wayema me alherin ciki banda shi jafar din ? Jafar din dai mijinku shine ya buwayeta yake alherinsa ba tare daya fada mata ba kada ki dada ki kara a wanan tsanar da tayi maki a yanzu kan rilon yar nan diyan baby da kikeyi yana daga cikon abinda yasa ta tsaneki haka ? Ta dauka ban sani bane har mutunci taci masa daya dauko maki yarinyar nan ta manta Nafisa na gidan take fadin ta rabasu hurda da duk wani dan uba nasu amma baya jin hakan . Tunda mutumin nan yayi zancen gida a gabanta nasan ya bambarowa yarshi magana har su kuwa indai dubune ki zuba ido kiga yadda zasu kwashe da ita a gidan nan yanzu. Ai tunda ta gane inda take hasashen yana narka kudinsa ba a nan abin yake ba yar nan a yanzu nata ya sameta kuma da dubu a gidan nan zakice na fada maki wanan zance kuwa indai itace . Sai lokacin na dan murmusa ina gyara kwanciya tace aiki barsu zakice na fada maki don sai ta zazzagewa yarinyar nan fushinta tas zataji saukin hakan a ranta yamzu. Sukan ba zakice tsohuwar nan iya ta haifesu ba son sam basu dauko halin iya ba ta ko ina sai jikokin ne suka dauko iyan a wajen sanyin hali sam iya baka rashin gaskiya ita a gabanta. Ni dai har barci ya daukeni ban sani ba a wajen sai dare sosai naji mama din tana tayar dani inshiga daki na koma daki na kwanta sai safe. Kamar yadda na saba a kullum hakane ya faru a wanan karon nayi sallah ban zauna ba na shiga aiyukan cikin daki saida na kawo wirin gada kamar a mafarki naji ya rikeni da hannusa da bai iya dagawa lokacin sai gashi ya rikeni dasu gam. Na dago ido ina kallonshi shima ni yake kallo idonsa a cikin damuwa yake magana fushi kike danine Rahama da nayi maki laifin me kike wanan fushi haka dani ? Ni ka sakeni ba fushi nakeyi ba na fada ina kokarin kwace hannu na daga rikon dayayi min din sai naji ya sasauta rikon yana murmushi yace. Da kina da wayau Rahama da baki fushi dani ba a wanan abin ko kinyi fushi dani ni bana fushi dake saidai ina son ki sasauta fushin nan naki don bake daya ke rayuwa a yanzu ba. Hakan daya fada yasa na kalleshi a lokacin ya daina kallona hakan yasa na kyaleshi na share dakin ruwa na hado nazo nayi mashi wanka dasu yadda na saba nagama na goge dakin na saka kamshi kafin na hado magani na zauna nayi mai addua na bashi ya sha na kuma hada mashi tea mai kauri kamar yadda na saba yi mashi kafin duk su kawo abinci sai na tabbatar da yaci wani abin a cikinsa kafin na bude kofa a kullum. Bugun kofan da akeyine yasa na nufi kofan don in bude saidai kafin na bude din naji muryan maman tudu tana fadin haba wanan dukan ai sunji dole a bude indai Rahamace yanzu haka ita ta tashi tunima tana aiyukanta ai. Ina budewa Saiba ta kutso kai a cikin dakin kamar zata bankeni naja gefe daya ta kutsa kai ciki tana fadin munafuncin banza da wofi kawai. A labe da sunan yaudara ana ha,intan mutane ga hakan Allah dai ya tona maki asiri ai kowa ya gama ganin ki da abin kunyar da kikayi . Abin kunya ai yana a gindin kowa don gara da nawa bada katon waje nayi ba da mijina nayi wasu kuma zarginsu akeyi da mazan waje ai ? Allah yafiki yafi sherinki nusaiba don ya kwatoni daga sherin da kikaso ki kulla min shigowan mama ya hanata ban amsa don mama ta shigo cikin daga murya tana fadin . Yarinyar nan kina da hankali kuwa ina zancen nan an kasheshi tun jiya yanzu kuma kizo da farar safiyan nan ki tayar da mutane da fitina haka ? Aina fada maku yar nan bata da mutunci dama nasan ba zata bar zancen nan ba ai kishin mahaukata kawai ta iya ita. Niba fitina nazo yi ba nazone a raba kwana abawa kowa hakkinsa tunda ba ita kadai bane kuma bata fi kowa da za a barta tana abinda taga dama haka ba ? Kanki daya kuwa to anki a raba kwanan yadda aka saba din haka za ayi ai dama ba wanda ya hanaku halinku shine ya koreku ba wani ba ko kun tsaya din me zakuyi mashi? Ki duba ki gani yadda yarinyar nan ta tsaya ta gyarashi ta gyara mashi muhalinsa a cikin ku wa zai iya wanan din ? Keko Amina tace hakan mana sai an raba kwana a yanzu mana tabi dare tayi mai fyade tace sai yayi mata cikin dole yadda yayiwa yar uwarta tunda ba Allah ta sani ba ita ? Saida na daga kai na dubi iya dake wanan maganan lokacin kafin na mayar da kallona gareshi yana kurum ya zuba ido yana saurarensu
Chapter 221 · 0% Book details