Sashe 170
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dama da shirinsa ya fito ke nan ? Sai biyu saura muka bar gidan bayan ya cikasu da alheri muka dauki hanyar gidan wani wajen gida ukku muka je a ranan sai bayan karfe hudu muka dawo gida. A hanya yake cewa dani bayan ya sauke ajiyan zuciya sai naji yace wallahi sai naji kamar an cire min kaya da naje gidajen nan. Nan ya fara min bayanin yadda alakansu yake nagane zumuncine ya koma kamar yan uwantaka wanda a yanzu mafiyawan sun yarda wanan akidan ta zumuncin haduwa da mutanen da keyi a baya. Bai kai ga ida tunane ba naji yana fadin yanzu sauran mu kaduna kuma in sha Allahu idan na dawo zamuje muyiwa ummah nata wunin acan mu zaga wasu yan uwa a can din don yan uwan mama akasarinsu suna zaune ne a kaduna su. Murmushi nayi don nima hakan yana cikin raina ga mijinta da kokarin kirana mu gaisa kwana bibiyu zai kira waya ya tambayeni muna dai lafiya ko idan mun gama gaisawa kuma yaba umma waya itama mu gaisa. Ganin haka yasa nima yanzu nake kokarin kiransu akai akai tunkan su kirani din mu gaisa don kada ya fahinci ban ra,ayin shi da mahaifiyar mu. Shiko gashi yana kamanta muna din har yaransa mata ya tayar da aka kwana biyu akan suzo su dubani suga yaya zaman mu yake ? Inda wata daga cikinsu take fada min ai tasan Saiba da Asmau a school daya sukayi nan Queen Amina zaria. Take fada min cewa abokaine fa sosai don har provition dinsu a lokacin tare yake saidai kazamaine na gaske kowa yasan su da kazanta ko yanzu sun barine take tambayana hakan ? Nayi murmushi ina fadin wallahi ban sani ba don ba shiga wajensu nakeyi bani koda na zauna gidan kowa da part dinsa saitace ki daiyi hankali dasu don ba karamar yar shige shige bace Nusaiban nan. Don abinda tayi ke nan ta kwacewa kawarta miji ance kuma zaman nasu ba dadi a tsakaninsu itace ke juya kan gidan sun mayar da Asmaun kamar shasha ita da mijin ku. Nan ma dai dariya nayi ina fadin ba gaskiya bane anty kowa dai da irin tasa ai sai yar uwarta da suke kira da Laraba tace nikan dai haka zance kina nufin in bata gane komai zata kai hakane a gidan ai da ta bar gidan don cin fuskan yayi yawa ai ? Gaskiya kowa da irin nasa suna dai rigima sosai amma kuma ba wai yadda ake nufi suke zaune ba don naga yana kokari da kowansu sai yamma ranan suka bar zaria. Murmushi nayi don tuna hakan nasan mutane akwai fadin abinda bai shafesu ba nasan ko yanzu nima da akwai abinda ake fada a kaina zama tare dasu din. Muna shiga gida iya ke fadin haba dai har ina batun soma cigiyar ku a gari haka shiru daga fadin bari muje mu dawo yanzu sai kuma shiru ? Yakai zaune yana fadin iya wanan mai kukan banza dince na fita da ita taga dangi dangina su ganta kada in barta gida ta cika muna kunnuwa da kuka haka . Kuka kuma jam da akai mata me yayi dariya yana daukan ruwan da Biba ta aje muna yana balle gora yace kinsan duk abinda mama suka fada dazun ai tana ji nasan shine yasata kuka kila ? Ehh banga laifinta ba don ko nice hakan zanyi tunda nasan banyi komai ba don na auri danki kawai zaki dauki karan tsana ki saka min ? Ba laifin kowa bane kaifin Daudane shike zugota anzo nan sai ya noke zai jini ai don bashi na basu dama so nake mu kebe dasu in masu iyaka da hakan . Ta bari daga yau idan ka taka kafa wajenta ta fadama duk abinda tayi niyar fada amma a gaban yarinyar nan haka kiri kiri ? Tajuyo gareni tana fadin kinga mutumiyata irin hakan ba kuka akeyi ba nasan akwai cin rai amma ki daure kada ki kara yarda ki nuna abin yanaci maki rai don in kin yarda tasan hakan ba zata daina ba tunda halintane hakan ai. Abunda na dauka shine harda son da Dubu keyiwa yaranta shine yake sakata hakan a yanzu tana ganin auren yaran nan da kukayi yana son yasa kan yayan ta ya juye ta kasa gane masu. Wanan shine kawai abinda tunanena yake bani akan halin nan nata don ko zama kayi da ita a yanzu kace mai yaran nan sukai mata ba zatace ga laifinsu ba amma zan zauna din inji inda matsalan yake don a gyara. Iya da kin barta don kada ta dauka kuma anyi wani abune yasa kike tambayanta idan anyi hakkuri ai abin mai wucewane in sha Allahu. Matsala dai a yanzu shine na farko kan auren yaran nan Saratu da Salima ya kamata suyi aure hakana zaman nasu ya fara damuna har ita Nafisa nake son a hadasu lokaci guda in hakan zai samu. Wanan shine daidai don matukar wanan saratun na gaban mahaifiyar ku a kullum zancen bai karewa tunda itace mai kai mata tsegumi akan matanka saidai taki yarda itace matsalan rayuwan nata. Nan na mike na barsu suna zancen sun jima don bai fita ba sai kusan magariba nasan daga masalaci can gidan ya nufa wajen matanshi yakai goma na dare bai dawo ba. Koda ya dawo din muna falo zaune ana hira ya shigo da ledoji a hannunsa a gaban iya ya aje ya mika mata daya yana zama yake fadin na rasa irin sakaci na Asmau iya ? Wai ace mace na jego bata iya kula da kanta balle yaron nan koda naje gidan gashi tace baida lafiya amma ta sake fanka har karshe ko rigan kirki bata sakawa yaron nan ba iya ? Asmau ai halinta sai Allah na rasa meye matsalan yarinyar nan ko wanan babban ai Allah ne ya raya mata ita don komai safiya haka zaka ganta da dan pant a jiki in anyi magana tace zafi. Yaja tsuki na kalleshi a gajiye ina fadin abinci fa ya dago yana fadin bar abincin nan Rahama wanan dai zan danci in kwanta tunda naje muka fita zuwa asibiti sai bayan isha,i muka dawo. Yanzu dai likita ya fada mata ai idan kasheshi take sonyi ai sai ta matsa kada ta kula dashi din na rasa meye matsalan Asmau wallahi ? Bata da matsalan komai sakacine kawai yake damun ta inka duba kamar ai haka yan gidansu suke a watse kowa abinda yaga dama yakeyi a gidansu. Rayuwane na zaman kishin matan yanzu ya haifar masu da hakan tunda kowa dansa ya sani a gidan ba mai tsayawa yayiwa dan wani fada kan abinda ya dace yayi makyau in bashi ba ko ita wanan ma,aikaciyar matan mahaifin nasu ai naga zata iya basu tarbiyan daya dace ai amma ina sun yafawa kansu zama na cin kai a tsakaninsu kowa na jiran wani sheri ya fito daga dan uwansa. To irin abinda akewa gudu ke nan ga wanan zaman ko kuna abinku kada ku yarda ku hada da yaran ku kuyi kishin ku ku kadai su kuma yara ku barsu suyi zumuncin su tunda Allah ya hada zama a tare. Na mike a kasalace zuwa kitchen na kwaso plate na kawo masu na iyan na fara budewa sai kamshi ke tashi na zube mata namane na rago da aka gadashi da zafinsa da yaji sai abinsha. Haka sauran ledan kuma suma suke ina kokarin zube masa nasane wayanshi ya dauki kara ya duba naga ya dauka a yanayin yadda yake magana don jin da nayi yana fadin ni gani gida ai. Ba nashiga sallama dake kina ganina kikaki aje wayarki ba na juya nikan wajen biba ina fadin hjy habiba ko kin koshine sai gobe zakici ? Da sauri take fadin haba anty saida idan zan aje naci na iya gobe naci nawa na fita dashi zuwa school ko ? Kaji yar wayau nice bansan dadi ba miko min nata in karama dashi nan kinji iyan ke fada muna dariya muryanshi ya katsemu don tsawan da yayi yana fadin. Wai kina da hankali kuwa Saiba in dawo in maki me tun dazun da nake gidan meyasa baki fada min ba sai yanzu wai meye matsalanki daine dani haka ? Look Nusaiba duk abinda kike nema dani fa zaki sameshi ina jin ta kashe wayartsne shine yasa yaja tsuki yana aje wayan a saman table din gabanshi. Matarkace ko iya ta fada yaja tsuki yana fadin itace don rainin wayau wai sai in dawo in sayo masu magani ita da laila yanzu wai ai suma basu da lafiya na kyalesu. Murmushi iya tayi tana fadin karma ranka ya baci halintane hakan kayi hakkur da abinka wasu mata basu da hakkurin saka ido akan abinda akaiwa yan uwa sai sun maganta wanda hakan ke jawo bacin rai a karshe. To iya haka zan zauna da ita kullum a cikin matsala ban isa inyiwa wata abuba sai tace don me ni wanan abin ya isheni wallahi kullum ita dai ban mata daidai ba a rayuwanta. Shiru falon yayi na dan lokaci ya karaci fadanshi shima yayi shiru din don ba wanda ya tanka masa kuma dama kuma ai iyance daidai ta tanka ta kuma bashi amsa ai. A raina nake fadin ke nan har yanzu badani kadai take kishinta ba ashe dukkan mu ta tasa a gaba tana yaka da kishi tunda naji ya fadi hakan. Wanan ke nan yasa anty salma fada min cewa zamana kishi irin namu zamane na kowa tasa ta fusheshi a gurin miji don ba zancen hadin kai a nan don ko an hadadin wata rana sai anji kanku da wace kuka hada kai din. Bai jima ba ya mike zuwa daki sai lokacin iya ke fadin ninasan wanan yarinyar ba zata canza ba ai don kishinta na haukane . Kinzo kin samu yarinyar nan da mijinta kince ba zaman lafiya ankawo wata daga baya kuma kince dai ina miji ya fito irinsu saidai a zauna dasu kawai da halinsu. Aida agida daya kuke zaune na tabbatar da yanzu dole dayanku tabar gidan saboda fitinan wanan yarinyar da kowa baida daraja a wajenta. Tsugul naji muryan biba tana fadin iya ai shiyasa maman mu