← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 306

Sashe 72

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anyi tsegumi sosai ga irin hidiman da Ya J yayiwa matar dan uwansa tsegumin kuma tsakanin can babban gida da wajen matan yaya sin yafi karfi. Ita mama kan dadin hakan taji a zuciyar ta harma da fili wanan kuma shawaran Kawu daudane hakan don kara samuwar hadin kan zuri,an tasu. Basu kara tsegumin ba saiga labarin zuwana school ya fito inda a take suka soma tsegumin hakan kuma ya za ayi in samu karatu a gurbin jami,a. Wanan kuma yaya Habune yayi min kokarinsa ya kuma tsaya saida yaga na soma karatun don let addimition dana samu karatu yayi nisa a lokacin ga kuma takardana sunyi kyau sosai ya baza kudi ya samo min a boye saiji akayi na soma karatu ai a nan jami,a. Anyi tashin hankali sosai a boye duk mu bamu sani ba inda yakai wani zuwa da akayi har akayi zama a falon Iya da kawu dasu yaya da matansu har Saratu dake gidan. Bayan an bude taro da addu,a mama data kirasu ta soma magana kamar haka na taraku nan don gano dalilin dayasa kai Jafaru ka nemawa yarinyar nan makarata haka irin wanan Jami,an ta garin nan ? Alhalin ga yan uwanka sunso karatu a nan haka kuma matan ka suma suna so gasu da yan uwa duk baka nema masu ba sai yarinyar nan Rahama ? Budan bakinshi yace ita Rahama ta fara karatune mama aini ban ma sani ba don ba a fada min ba dama ina da niyar ta soma ai tunda tana tare damu kuma kowa yana karatun nan kada tace mun mata banbamci ? Uwar tace yaya zaka tambayeni bayan kaika samo mata abu kowa a nan ya sani yanzu zaka nuna baka sani ba kuma ? Saiba ta gyara zama irin wanda ke nuna a to din nan kasan komai barkado kakewa mutane kawai. Yace wallahi Allah mama bansan ta soma karatu ba don bani na samo mata ba amma kuma ina da niyar hakan a ina ta soma karatun ? Kallon juna sukayi shima kallon Habu yayi yana son sanin wani abu akai da kyat Habu din ya hade wasu yawu don ransa ya gama baci a lokacin. Yace a A,B U ne yaya J Awar nasa ya samo mata don takardunta sunyi kyau sosai zata iya zuwa karatu ko ina a fadin kasan nan dama ina son hakan Anwar ya jima yana cewa nakawo mashi takardun wanda yai kyau a bashi gurbi a wajensu shine na kai masa nata takardun. Hakan yayi kyau sosai Allah ya bada sa,a yasa taci amfanin abinta ita da sauran al,umman Annabi sallalahu alaihim wasallam. To ke nan Jafaru bakai bane don ka nuna baka da masaniya akan hakan ya sake kallon uwar yana fadin wallahi mama ban sani ba amma ina da niyar hakan a gareta. To ku kunji shiyasa Allah da manzonsa suka horemu da munana zato a tsakanin mu wai tsaya mama don Allah ba katseki bayi ba a nan shike nan yanzu ba a da halin a taimakawa iyalina kome haka yake nufi ? Kai Habu dakata ai anbar magana baya kawu ya fada yana gyara zama yace toni Habu bai yi hakan ba saida ya sameni ya fada min kyakyawan niyarsa na son taimakawa yaran nan na kuma bashi goyon baya akan ya nemi shawaran mahaifiyarta da yar uwarta ko zasu yarda da hakan. Ka fada min yaya saidai a yadda suka hau din nan ba yarda zasuyi da hakan ba don zasu dauka na rufe masune amma ni Habu yazo nan da takardun ya nuna min haka kuma da zata tafi tunda dare ya sanar dani hakan. Mama kawu don Allah ku gafarce ya J ina son barin gidan nan don Allah ka tafi ina mama din ta katseshi da tambaya yace ko haya zan kama kafin na karasa gina nawa mama . Tir tir wallahi akan wa yan nan habu basu isa su raba mu da uwarmu ba muddin mama tana raye a doron kasan nan saidai su subar muna gidan tunda zama dasu ba dole bane. Ko akwai wace aka haifeni da ita a cikin ku kona fada maku cewa ni din ba dan dangi bane ke Asmau kin sani tun bude idon ki kinsan koni waye har iyayyen kunsan yadda gidan mu yake kika yarda kika aureni a hakan kona boye maki wani a cikin rayuwana wanda baki sani ba ? Kasa tayi da kanta tana fadin toni me kaji nace a nan munafukan banza da wofi kawai mama zatayi maki karyane ? Kyale ta dukkansu nan suka sameni da kukan su harda wanan sauniyar shakatafin wai kana son ka fifita yarinyar nan basu san meyasa haka ba ? Saboda ba kudin gidan ku nake amfani dashi ba yasa ban fada maku damuwata wanan maganan idan bakuyi hankali ba wallahi karshen zamana daku yazo ke nan a gidan nan. Kai haba meya kawo wanan maganan a yanzu ana sulhu kuma bari mama halin matan nan ya dameni ko alheri nayiwa dan uwana suka sani sai wanan shedaniyar tayi min korafin hakan me yasa zanyi ya nuna Saiba. Ni ai ba kace ni kadai ke hakan ba idan kuma kaji nayi maganan abu itace tagani ta fada min sai nayi magana tunda muna tare da kai. Nasan Asmau munafukace ta karshe macijiyar soshiyace yar sari ki noke kawai nasan halin kowa a cikinsu ke gaki mara kunya kece ke iya gaba da gaba dani don baki da kunya. To ai bamu muka soma magana ba Saarece ta samemu da zancen ita da Amina suke fada mana kaine kakai ta wanan school din. Suyi rikici a wajen sosai don Habu ya kafe da abarshi ya bar gidan don su din makiyansane sai da kyat aka samu ya lafa don Jafar bai ragawa matan nasa ba harda zancen sunan Abbati saida sukayi yace da yana da halinda yafi haka abinda zaiyi saiya fi wanan don baida wanda yafi mai dan uwansa a duniya. Jin hakan yasa dole habu din ya sasauta zuciyar shi har anci an sude yar uwata bata san abinda ke faruwa ba tana part dinta sai nice dana fara jin zancen wajen iya nake tambayan anty Nafisa ta fada min komai . Nayi mamaki tare da tunane abinda mukai masu don wanan kiyayyan yayi yawa haka a tsakanin mu dasu Allah ya taimaka ban faye fadawa yar uwata abinda ke faruwa a gidan ba. Nakan barwa kaina in shaye duk wani abinda za a fada game damu don ta zauna lafiya da mijinta wanda kowa hakan zai mata fata a zamansu din. Jin abinda ya faru din yasa na kara kama kaina sosai da yan gidan namu har anty Nafisa da muke dan shiri da ita a yanzu ba komai take sani game da mu ba. Karatuna nasawa gaba sai kuma lalurar yar uwata indai mun hadu zamu gaisa dasu idan bamu haduba kuma a zauna lafiya. Wanan halin ya karune a ranan wata jumma,a dana saka wasu kayan da anty salma tabani sawa daya tayiwa kayan ta kwabe ta mika min wai dinkin bai mata ba. Sai gashini kayan sun matukar karbuwana suna saka don girmama jumma,ata na ranan da wuri na dawo don haka na samesu a wajen gida inda suka tsiri zama yanzu suna shan iska. Gaba dayansu daga can inda suke zaune suka zubo min ido tun bude get dina shigowa gidan ban nuna nasan suna zaune ba na bude part din yar uwata na shiga da sallamata kukan Abbati nakeji nake tambaya meya faru kuma yake kuka Yanda ? Bansan meya sameshi ba tun dazun yake wanan kukan daukan yaron nayi na kwabe masa kayan jikinsa don yasha iska ko zaiyi shiru saidai a banza daukansa nayi na daurayeshi har na shafa mashi mai na sauya mai kaya na kaishi wajen uwar don ya dan rage kukan da yakeyi. Yaron ya kama nono sai kuma ya sake yana challara ihu yana kwandare kafa da shure shure hakan yasa na daukeshi zuwa part din iya ina jijigashi. Yaron a yanzu yayi wayau sosai dan kimanin wata bakwai ke nan da haihuwa anan na sake wucesu ban tsaya duban wajen ba nashiga iya tana zaine ita kadai a falo nasameta dashi nake gaisheta. Bata samu amsa min ba take tambayana kome ya samu yaron saidana zauna nake fada mata haka kawai yake kuka tundazun. Karban yaron tayi tana fadin na dauko mata jar kanwa ta hausa shina dauko mata tajika taba yaron yasha. Ta miko min shi nacigaba da jijigashi a hakan ya shigo ya samemu yaron yana dan sauke ajiyan zuciya gaidashi na soma naji iya na fadin. Ka dawo kenan Jafaru ko baka samu zuwa bane naje iya dawowan mu ke nan yanzu duban mu yayi yana fadin wanan kuma meya sameshi haka ? Iya tace ina ganin cikinsa ke ciwo kasan yaran yanzu ba kula suka iya ba sun dauka kukan banzane haka kawai mutum zai dinga kuka da gangan ya fada ? A daidai lokacin Saiba ta shigo part din itama yana fadin in miko mashi dan na banye na mika mashi ya karbeshi yana fadin yanzu me aka bashi ? Kanwa na jika na bashi yasha iya ta fada da sauri yace iya kanwa kuma ina maganinsa yake da aka bashi kanwa bari a kaishi asibiti dai a dubashi. Ai yasha kanwa ya fada mashi Saiba ta fada ke dauko mayafin ki mu kaishi asibiti kome ya tuna kuma yace kira min Saare mukashi asibiti . Batayi niyar fita ba yasa ya dubeta yana fadin badake nake ba ta juya cikin bacin rai ta fita sai naji iya tace kayi dabara don gara zuwa da Saratu din. Nasan halinsu da sheri ko yanzu abinda ya kawota ke nan ai ta dauka nasan wanan tana part din nan bar yan iska zanyi maganinsu ne. Kyalesu Allah ya dora masu kishine haka barsu sunyi ta haukansu akan hakan su girman su ke zubewa gareta ina fama da yaron ba jinsu nakeyi ba don na koma wajen kitchen dinsu ina jijigashi. Saida suka tafine naji iya tana fada na dan fahinci abinda ke nan ni kaina gaskiya da nasan yana gari ba zan ko shigo part din iya ba a lokacin don nasan wajen zuwansane bansa
Chapter 72 · 0% Book details