← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 184 OF 306

Sashe 184

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani kallo tayi mai ta juya ta fita daga dakin bata tsaya ba ta nufi hanyar fita daga asibitin kai tsaye Saarece ta hangonta ta nufeta tana kiran sunanta. Ta juyo a hasale tana fadin akan me za ace bamu shiga wajen miji mu ko Rahama ta fimu ne don kawai tana kanwar matarsa zai dinga nuna muna bambamci da ita ko me ? Haba dai kinga haka yana yuyuwa ita kadaine halan da za ai hakan wananma ai maganam bamzane watafi a cikin halan da zaice hakan ? Idan bata fimu ba aiba zai fadi hakan ba zaman me zan zauna nayi tunda ba rako mata nayi duniya ba zo muje ga mama can kada ki tafi idan kin tafi ai taci bulus ke nan a kanku ? Jin hakan yasa ta biyo saare din zuwa wajensu mama din inda suke zaune saman tabarma da abokan zamanta suna tattaunawa kan jikin jafar din. Mama kinji wai ya Habu kada su saiba su shiga dakin da ya J yake sai Rahama kadai aka yarda ta shiga wajensa amma banda su ? Wai meke damun habune haka mama dubu ta fada kafin ta rufe baki mama tace haba dai dubu tunda kikaji yace hakan ai dole akwai dalili tunda ciwon yaron nan baison damuwa ko dogon motsi a kusa dashi. Amma sai ace matansa ba a yarda suje kusa dashi ba sai wace aka so taje din zata tafi wanan wani irin danyen hukuncine haka yaya ? Habu din ne ya fito daga dakin da saurinsa hankalinsu ya koma kanshi ya karaso yana fadin ya isah fa lafiya dai suka tambaya don yadda suka ganshi a hargitse. Baba Tanimu ne yayi waya akan wani yaje ya karobo wani abu azo dashi banda lokacin zuwa yanzuni don tafiya zamuyi dasu mama zuwa wajen wani mai magani kuma. Aiga Auwal can ya dawo ina ganin gida suka danje zai tafi mama ke fadin kai habu meye hujjanka nacewa yaran nan kada suje kusa da mijinsu sai wace zuciyar ka ya yarda da ita ? Ni kuma mama yaushe nace hakan aina fada dole akwai dalili yanzun nan saratu tazo da wanan tana nuna Nusaiba tace wai kace kada su shiga mama uwargidan su mama dubu ke fadan hakan. Mama yaya za a bari suna shiga haka barkatai wajen mutumin dake son natsuwa a yanzu tashigo tana fada wai ko don me zansa likita su kira Rahama ? Nace don itace kadai ke zuwa kusa dashi ya gane tazo hakan laifine ko tsoronta akeji da zata dinga zuwa tana tayarwa mutane da hankali bayan wanda muke ciki saboda bakin kishi irin nata ? Bako za a bari ba tunda haka dama jinya ya gada ba kowa bane zai shiga haka kai tsaye aiko lokacin da Alh ke jinya ke dubu daga ke sai nice muke bayayyan shiga gurinsa a lokacin. Jinya abune fa da yake son natsuwa da maida hankali illa iyaka a bishi da addua Allah ya bashi lafiya ya mike shine abinda yake bukata garemu yanzu. Ke kenan da kika san hakan ai kin fada iya ta tsoma baki daga gefen da suke zaune suna saurarensu . To umma tsoronta za aji tunda ga gaskiya aki fada saboda ana gudun kada zuciyarta ya baci ita idan tana da tunane ai wanan abin yanzu na kowane bana mutum daya ba. Ke Nusaiba ki natsu kada ki tayarwa mutane da hankula a nan muna fama da kan mu da abinda ya damemu ke inkina da kunya ya kama aji hakan a wajen ki yanzu ? Ina wanda kike fadan kansa shine a kwance rai a hannun Allah idan kina da tunane har aji wani zance haka a bakinki yanzu kuma ? Meke faruwane mama ya Auwal yake tambaya bar yariyar nan tana son dagawa mutane hankali bayan wanda muke cikinsa a yanzu don ance su fito aba majiyanci waje ya huta take fada da Habu. Dama naso cewa a rage wanan shigowan da akeyi abar wa yanda zasu tsaya kawai tunda ba ganinsa akeyi ba zama kawai ake zuwa ayi ta hira a zauna gida abishi da addua zaifi. Wanan yarinyar amaryan shi ita damu zamu iya kulawa dashi tunda zuwanta yana da ma,ana a wajen nan ko dazun ya gane tazo don ya amsa mata adduanta da take mashi . Kunga gara din tana zama a kusa dashi ko yaushe zaifi mama ta katseshi da fadin abinda likitocin da habu suka fada ke nan ya zama matsala a gareta. Ai ba ance kada ku shiga bane hayaniyace ba a so a wajensa yasa aka fadi hakan amma ku da mijin ku a hana ku shiga ku ganshi. Dole dai me jinyar tasa idan tana da tunane ai ta bada wuri kuma ku zauna dashi din tunda jinya shina kowane bana mutum daya ba . Saiba tana gefe tsaye tana sauraren mama din don a gaskiya zatace wanan matar tana yawan shige ma lamarinta ko wani lokaci ta gaji da irin halin da mama ke nuna mata ko yaushe idan magana irin haka ya taso zata nuna itace mara gaskiya a cikin zancen. Wani bangare na zuciyarta ya gargade da kada ta yarda ta soma yiwa mama rasgin kunya duba ga yadda gaba daya family din suke ba mama girma. Yin hakan zai iya haifar mata da wani matsalan da zai jawo barin ta gidan kai tsaye donshi tayi shiru kamar tana daukan nasihan da mama din ke mata a lokacin. Saiga mama din ta koma magana kamar na lalashi a gareta tana fadin kuyi hakkuri wanan aiba komai bane idan anyi hakkuri duk hakan mai wucewane fatan mu dai Allah ya tayar da kafadan yaron nan ya samu lafiya ku koma zaman ku yadda kuke shine fatan mu kinji a dinga hakkuri da kuma saka basira cikin lamari. Hakan yasa ta danji sanyi a zuciyarta har ta nemi waje ta zauna daga gefe tana sauraren kowa a wajen . Har zuwa lokacin dasu mama har iya suka mike suka bar cikin asibitin tare da habu suka tafi inda ba wanda yasan inda zasu din sai su kadai. A cikin rashin sanin hakan na fito da wanan kayan nasa da aka cire mashi da niyar zuwa in wanke su a bakin famfo saidai kada in barshi shi kadai yasa dana fito na nufo inda suke zaune na dan duka a tsakaninsu ina fadin. Zanje in wanke kayan nan daya bata ko wata a cikinku zata shiga ta zauna dashi mama din ke fadin ke nusaiba ki shiga tunda yar uwarki nada goyo. Kamar ba zata mike ba ni dai na bar wajen na nufi wajen famfo don wanke kayan a can Maria da salima suka sameni mun jima tare dasu a wajen don dana gama zama mukayi muna hira dasu duk akan ciwon yaya din. Maman tudun wadace ta mike ta shiga dakin inda ita da umma inda suka sami saiban zaune tana waya sundan jima tsaye a kansa suna kare mashi kallo kafin mama din ta fara magana tana fadin. Gyara mashi hannun can daya taushe ta dakatar da wayan tana kallon hannun nasa tace haka na sameshi na zata ko hakan yake jin dadin kwanciya din suka barshi. Suwa ke nan fa ke yar nan ki iya kanki don Allah abinda ake fadi ke nan kuke ganin kamar an barku baya shi jinya kula yake so kaba maishi kinga ko wayan nan bai dace ace kina daga murya haka ba gabanshi. Wani irin kallon rashin kunya ta jefawa mama din kafin ta mike tsaye ta nufi wajen hannun da suke magana din tana kokarin dagawa a cikin karfi. Haba dai yi mashi a hankali mana kinsan jikin ba karfi sai a sannu dole za ai mashi komai yanzu umma ke fadin hakan a gefen mama din. Ganin ta kasa dabaran yadda zata dagoshi yasa ita umma din mikewa suka kama mashi daga shin da zasuyine suka gane yayi lalura a lokacin . Umma din ke magana tace yanzu yaya za ayi don sai an dagashi gaskiya daga inda mama take zaune take fadin sai takira yar uwata su dagashi a sauya mashi kayan tunda ya bata wa yan nan. Gabatane ya fadi ta yaya zata iya hakan amma bari ta nemo Asmau tagani suma su nuna tasu bajintan da ake ganin basu iya din. Fita tayi ta nemo Asmau din ta shigo take fada mata abinda zasuyi abinda Asmau ta fada shine ta yaya zamu iya daga shi har mu cire mashi wanan kayan Saiba ? To ya zamuyi su mama sunce mu canza mashi in bamuce haka za a barshi cikin lalura tunda mazan basu kusa a yanzu kune dai dole a yanzu zaku sauya mashi ai. Kayan da ya habu din yasa nazo dashi suka dauko sai nan suka tsaya dabara fita su mama sukayi suka barsu dashi a dakin saidai sun rasa yadda zasu fara tsarkakeshi balle su sauya mashi kayan jikinsa din. Ita saiban ce ta fito nemana dole nice nazo a cikin karfin hali na tare da taimakonsu muka samu aka sauya kayan na goge mashi jiki muka saka mai wasu tufafin a ranan na kara sheda cewa dan Adam ba a bakin komai yake ba a wajen Allah. Iya kar dan adam a lokacin da yake a raye shine yake cikin koshin lafiyansa yake jin kansa dashi wanine ashe da zaran ka rasa lafiyan ka ka rasa komai ke nan a rayuwanka. Yau yayane haka ake dagashi kamar dan jaririn da bai taba sanin duniya ba balle abinda ke cikinsa shine yau yake lalura a kwance har ake kyamar tabashi haka ? Komawa nayi still na wanke kayan daya bata din na nado wa yan nan din dana wanke da farko saidana dawo na zauna mama ke fadin waiko kinci abinci yar nan ? Maria ta kalleni take fadin bansa taci komai ba mama don tunda safe tazo wajen nan gara dai kici wani abin a cikinki kada ke ma ki kwanta ciwo . Shi jinya saika daure kana kula da kanka kaima in ba haka ba sai anyi haihuwar guzuma da kwance uwa kwance. Ki duba ko zuwan nan yan uwanki naga sunsha su lemo da kayan sanyi kada ki yarda ki bari ciwo ya
Chapter 184 · 0% Book details