Sashe 195
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dan uwa murfin jallo inji manya wasu sukace rabin jiki kuma don hakan ne ya kasance ga habu lokaci guda don ganin kwaryan da ake nufi ta jafar taki motsi yasa ya dinga karanto addua da sunayen Allah mai girma sai gashi a fusace ya daga kwaryan ya tura ya fara tafiya saman ruwa cikin yardan ubangiji. Abin mamaki suke kallo daga iyayyen har mai maganin sun zubawa ikon Allah ido suna bi da kallo tun wanan kwaryan yana kokarin turjewa ya tsaya a waje daya har yakai ya fara dan tafiya da sauri sauri yana bin igiyar ruwan kamar yadda dayan kwaryan ya mike tsaye yabi ruwa suna kallo. Lai habu kakai shu,umin yaro iya ta fada daga gefenshi hakan yasa ya dan kallo iyan yana fadin komai zanyi akan dan uwana iya. Amma baka ganin kayi kasada da shiga hurumin daba naka ba habu iyan ta kara fada a hankali yayinda duk hankalinsu yake kan kwaren dake saman ruwan suna tafiya . Kaga wanan abin kamar rayuwace malam habu haka ruyuwan bawa yake a wajen ubangijin mu shi ciwo ba mutuwa bane wani lokaci. Wahala kawai bawa yake gudu da fitinar ciwo don sai kaga mai lafiya ya tafi ya bar mai jinya a kwance inda rabon mikewa sai majinyacin ya mike shi wanda yake tsaye yakai kwance. Kallonta iya tayi kallo dake nuna akwai magana ke nan ga wanan zancen nata bata kula ba tana surkullensu na yan bori har zuwa lokacin da ta dago garesu tana fadin da alama dai sadaka ya karbu ke nan sai dai ayi fatan Allah ya tsare. Akwai abubuwa da ya kamata ace kun sani tun wajen amsan maganin nan wanda nake ganin kai malam dauda ya sani a lokacin. Kawu dauda yana jin hakan ya gyara tsayuwanshi yana dan kame kame ta karbe da fadin baida matsala tun lokacin da abin ya damu maman mu ta sanar dani komai akan haka har zuwan da matarka tayi daga baya tana neman a bata aikin a mayar dashi wani nau,in sai daga bayane hakan ya damu maman mu kuma bayan tayi aikin abin ya koma yana damunta wanan yasa na fita neman ku don kwantacen da matarka tayi muna a lokacin . shi nayi amfani wajen nemanku nazo har zaria din a wajenta naji komai a cikin hikima don yadda najata a jikina sosai a lokacin. Naso ace kunzo lokacin da mahaifiyar mu take raye saidai hakan bai samu ba don kaddara ya riga fata a cikin lamarin. Kai yanzu ga yar uwarka bata san abinda kai da matarka kuke shiryawa akanta ba duk dadewan nan ya kamata ace ka fito fili a yanzu ka sanar da ita manufarka a kanka dakai da matarka. Me zai fada a yanzu ai gara kawai yayi shiru don hakan ma ai maganace don jin baida amfani a wajen mu yanzu tunda ko yanzu Allah ya baiyana muna nufinsu a kanmu. Ban taba zaton hakan ba yaya ko mutuwa nayi na taso akace kaine kayi min hakan akan zuri,ata zance kazafi akai maka don a shiga tsakanina dakai. Wai sai gashi da raina da lafiyata hakan ya faru yau a gabana yaya ka kasa mussa wanan zancen da aka dade ana fada min ina fadin karyane zalla zumuncine kawai a tsakanin mu. Ashe abin ba haka bane yadda na dauka kai a wajenka da wani manufa ka ke nuna min zumuncinka a kaina don kawai,,,, Kukane yaci karfin ta wanda yasa habu ya taso daga inda yake yazo ya rike mahaifiyar tasu da komai yake iya faruwa da ita a lokacin don yadda yanayinta ya nuna a lokacin kamar bata cikin hankalinta. Shima kawu dauda din sai fadi yake na dade da nadaman haka Dubu tun bayan dana fahinci cewa kamar yaran nan sun gano irin abinda Hafsatu ke izani inayi akansu din. Tundai ma shi Habu da har ya fara fitowa fili yana fada min magana a fakaice wanan yasa na fara neman mafita daga kaidin ita hafsatu na yanke shawaran in kara aure,,,, Daga baya ke nan dai dauda kaji kunya wallahi ka rasa wanda zaka zallunta sai yar uwarka akan abin duniya me yaran nan suka rageka dashi a matsayin ka na kawunsu ? Malam dauda kadai fadane amma hakan bashine nadamarka ba ko in fada a nan gaban kowa wanan abinda ka fada bashi bane nadamarka mai magani ta fada. Kinga idan abinda ya kawomu har an gama a barmu mu tafi don dan uwana dake can kwance ba lafiya munzo nan da sunan wunine don bamuzo da niyar kwana ba nan da zaria akwai nisa sosai don haka zamu koma yanzu . Ya fada yana kokarin mikewa tsaye don duk wanan bashine a gabanshi ba zancen dan uwansa shine ke zuciyarsa din yana ganin kamar wani abu zai iya samun jafar din kafin su dawo zaria a yadda suka barshi din. Ba yanzu ya shirya daukan mataki a gun kawu ba sai bayan komai ya lafa yake son su tunkari dan uwan mahaifiyarsu din da matarshi. Don tunda sukai waya da yaya Isah ya sanar mai halin da suke ciki asibiti da jafar din hankalinshi ya tashi yake ganin ai kamar baida rayuwane sun boye mashine kawai. Sai bayan sunyi nisa yake sanar dasu irin halin da akace Jafar din ya shiga bayansu wanan ya kara daga masu hankali sosai. ZARIA Tun bayan faruwan hakan muna dakin zaune nida mama da inna don ita umma ta koma gida don basu watsewa su bar gidan ba kowa sukace. Inda yaya isa ya gargada yan uwa yace su koma gida ayi masa addua tunda likitoci sunce ba zasu bar kowa ya shiga ba kuma dakin da yake kwance din. Bayan na idar da sallah magaribane inda nake zaune makure a cikin damuwa wayata dake cikin yar jakata ta dauki kara na dauko ina dubawa abin mamaki dan uwana Dagene ke kirana a lokacin. Na dauka murya ba dadi ina amsawa yake fadin yaya yaji muryata haka kamar banda lafiya ? Ban iya bashi amsa ba sai kukan dana fashe dashi lokaci guda a cikin harshen fulatanci nake masa bayanin halinda mijin nawa yake ciki. Wai tsaya Anini ko dai zancen mijinkine naji hardo da nayi da baffa dazun nan yake fada min yaji hardo ya bugowa baffa waya suna zancen don ya bashi wani makari da zai masa amfani dashi. Asalin maganin baffa ya dauke daga kakansu shi kadai kedashi a hannunsa yanzu nan dai yake fada min a ranan idan baffa ya fita yawon darensa zai shiga ya dauko min tun da safe zai shigo mota yazo zaria dashi . Naji dadin hakan sosai don nasan tunda yayi alkawari har in ya samu daman daukowa zai kawo din naja bakina nayi shiru don ba abinda zan fadawa wani bane zancen daya shafeni ni kadaine wanan saiko yar uwata. Karfe goma yaya Auwal yace na fito mu tafi su saukeni gida don zai mayar dasu mama da inna gida a lokacin ba zan iya rokonsa ya barni ba . Saidai furucin mamane yasa naji sanyi don ita ke fadin Auwal kubar yarinyar nan ta zauna kusa dashi don ko dazun daya rikice badon itaba bamu san yadda zamuyi ba. Taje dai ta shirya ta dawo nima zan tsaya a nan din tare da ita ya kasance ta samu mace a kusa da ita sai yaya Isah yace amma mama kinga,,,,,,, Abinda na fada ke nan isah kubar yarinyar nan a kusa da mijinta har in kuna skn ganin cigaban lamarin nan ga dan uwanku. Hakan da mama ta fada shine yayi sanadin zamana da ita a kusa da yaya din ko wani lokaci don mama irin matan nan ne masu tsare gida ga bada umurni ga iyalinsu wanan yasa take jan girmanta akoda yaushe. A can gidan su Jafar din kuma tun bayan barin su asibiti da suka isa gida Nusaiba ke ta kuka tana waya da yan uwanta tana fadin cewa an kita ana son hada mata kai yan uwan jafar sun tsaneta suna kinta. Da korafin yayi yawa uwar tace taba Asmau waya zasuyi magana shine Asmaun ke fada masu abinda ya faru uwar tayi masu fada dukkansu kamar yadda ta saba tace ai dole zasuce hakan tunda kuna nuna kamar baku damu da halinda yake ciki ba a yanzu. Ta yaya zaku tsaya karamar yarinyar har tazo ta fiku iya fallako ta karbe maku miji kuna gani ai ba sunce bane inda suke ganin kauna suke jin taushi tunda rayuwansa ake nema a yanzu koma meye ku bari gobe zamu shigo ai. Da haka suka samu ta hakkura don cewa tayi da zata dawo gida tunda an nuna mata kiyayya a nuna bata da amfani ga jafar din. Ranan sunyi shirin da suka jima basuyi ba a tsakanin su don sunyi zama na shawaran kan abinda zai fitar dasu daga kallon tuhuman da yan uwa suke masu din. Su mama basu dawo Zaria ba sai karfe biyu saura na dare ina zaune a dakin da hasken wayata ina karatu mama tana kwance a gefena suka shigo don basu nufi gida ba asibitin suka nufo kai tsaye . Jin an turo kofa yasa na dago kai ina duban kofan dakin sune dasu yaya suke shigowa hakan yasa na dan taba mama da barcin ba nisa yayi ba a lokacin ta tashi muna masu sannu da zuwa. Suka amsa da tambayan ya mai jikin aka basu amsa da saukin tun dai dazun din barci yakeyi a hakan yadda yake bai kara wani abuba kuma har wanan lokacin. Iya ta karaso tana fadin Allah ya baka lafiya jafaru ubangiji ya tada kafadan ka a cikin mu suna amsawa da amin kafin ta juya gun mu tana fadin Salamatu ashe kina nan mama ta amsa da ehh iya zuwa gidan ai baida amfani gara na tsaya a nan din tare dasu. Rahamatu kina zaune baki barci ba ke nan ta juyo kaina tana fadan hakan cikin nuna kulawa nan mama ta karba da fadin . Ina ai yar nan akwai kokari ko dazun din daya rikece itace tayi namijin kokari akansa kafin likitocin su iso tayi dubaran datse hakoran nasa da cokali daya taune harshen nasa ai duka don ba mai dabaran hakan acikin