← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 306

Sashe 76

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

din mu mama ta kira waya da inzo mu kula mata da Jafar zasu tafi wani waje ita da kawu. Don a lokacin ita Saare tana school ita kuma Salima ta wuce bautan kasa saini da Nafisa ne a gidan muka shiga part din nasa tsit don matan gidan da basa nan kwana biyu. An dawo da Asmau mama tace taje ta huta kawai haka ba yana nufin zata raba mata aure da mijinta bane bata dai son ganin su gidan a yanzune. Lalai ankai hali dubu makura mace mai hakkuri ta iya yanke wanan hukunci don haka kawu yace suje din kamar yadda tace har ta huce. Anty Nafisa tashi mu shiga dakin yaya ayi komai a gabanki don Allah akwai taimakon da nake son yi ban samu daman hakan ba a gidan nan . Kallona tayi a tsorace tana fadin me zakiyi Ramaah nace zo muje anty Allah ya gani taimako zamuyi da zuciya daya. Dakin muka shiga da sallama ya kwance gwanin ban tausayi muka gaidashi ya amsa muna da kai dakin ya danyi shiru gabana sai faduwa yake ina kuma kare mai kallo nace yaya don Allah ka fahinceni. Akwai wani magani da aka bamu a gida nake son in jaraba mu gani amma ina tsoron hakan bansan me zan fada ba yasa yanzu na sameka ga anty Nafisa don Allah yaya ka daure ka dinga sha koda ban kusa anty Nafisa zata baka zamu fadawa iya kuma. Maimakon ya amsa min sai hawayene ke zuba a idonshi na fito da kullin maganin muka zuba mai a kunnu bai ki ba yasha muka kara kwantar dashi. Mun jima a wajen zaune sai sha biyu su mama suka dawo gidan kawu ya sauketa ta samemu a dakin wajensa zaune bamuyi barci ba. Mu muka taimaka mata tayi mashi komai a ranan daman dana samu kuma weekend ne don haka yasha maganin kusan na kwana uku ina bashi a boye. Mu gyara dakin mama tayi mai wanka kafin ta fito na kwashe zanin gadon na shimfida wani na feshe dakin da kamshi. Zakiga ya sauke ajiyan zuciya idan ya zauna na hada mai kunu ina bashi mama tashigo tana saka min albarka tare da fatan alheri a gareni. Take fadin Rahama indai ba karya nakeyi ba kamar jikin jafar yana saba (salinta ) alaman hakan kuma meye ? Mama duk ta rude daka ganta bata cikin hankalinta nace mama kila hakan wani sallon ciwon ya canza kuma ? Naji sauki sosai ya bamu amsa da fadan hakan yana gyara kwanciyarsa ya habu ya shigo dakin nayi saurin gaidashi yana tambaya ina Nafisa mama ke fadin yanzu take nan tace iya tace tayi mata shayi . Ya karasa bakin gadon yana fadib J ya karfin jikin naka ya bude ido ya dubi dan uwan yayi dan murmushi kadan hakan yasa ya Habu din yakai zaune. Mama bari naje na gaidasu iya na fada ina fita tace kima huta tunda ga Habu ai kafin kawun ku yazo ya kama min nima na dan jena huta. Bayan fitana yake fadin yarinyar nan habu yace wa Ramaah ya gyada kai alaman eeh saiya lumshe ido yace me tayi yaya yace kirki don bai dogon magana. Sai Habu din ya danyi murmushi mama daga gefe tace meyace wai Rahama yake fadin tana da kirki aini har tausayi ta koma bani yarinyar arzikice sosai wallahi. Barci nayi sosai don kwana mukeyi gadinsa a gidan daya motsa dayan mu dake falke zai tambayeshi me yake so ? Hakan yasa har zuwa school na dan dauke don maganin da muke gwadawa wanda dagani sai anty Nafisa dashi muka sani haka kuma yana sha sosai idan mun bashi din kuma yana shan wanda su mama keyi mashi. Hadari aka hada sosai a garin hakan yasa mama cikin damuwa ga yaya Habu ya tafi kaduna tare da kawu gashi ance kada a dage rana ga karbo maganin fita nayi kamar zan shiga cikin gida na fice bakin get ban samu abin hawa ba haka nayi ta sauri saida na kusa isa na samu mai keke ya karasa dani gidan mutumin. Na karbo haka na biyo ruwa da iska na iso tsamo tsamo da maganin gidan nakaiwa mama mamaki tayi sosai ta shiga yi min fada yadda na iya fita a cikin hadarin nan. Nace mama gani nayi lokaci zai wuce bai sha ba kuma ga ruwan nan ba a san lokacin da zai tsagaita ba. Maza kije ki kwabe tufafin nan kada sanyi ya kara kamaki mura ya sauka maki kin daiyi kasada wallahi bin hanya haka a cikin ruwan nan . Dakin ta shiga tana fada yake tambayan meye mama din tace yar nan Rahama ashe ta fita a cikin ruwan nan ta tafi karbo maganin nan dana damu akansa. Baiyi magana ba sai zuwa can yace mama yaran nan suna matukar kokari sosai wallahi a raye suke kwana gidan nan. Aini ban iya cewa komai a yanzu saboda ko yaran nan su saratu ba zasuyi min wanan dawainiya haka ba wallahi. Bayan kamar kwana biyu jikin nasa yayi sauki sosai a lokacin ya dan harda tafiya ba tare da an rikeshi haka kuma kumburin kafanshi ya fara sucewa kafan yana fadawa don yayi kamar turmi a lokacin ba dadin gani sai walkiya da yakeyi kamar zai fashe. A takaice bawan Allah nan yasha wuya fiye da tsamani sai zantuka akeyi marasa dadi game da ciwon nashi kowa da abinda yake fada. Shi kanshi mijin yar uwata duk ya fita cikin hayacinsa saboda jinyar dan uwasa din hankalisa duk a tashe yake haka kuma shike gudanar da komai na kasuwancin dan uwan a yanzu. Zuwan ummah biyu daga kaduna suna wuni a nab su duba jikin nasa ita da maigidanta sai ya ajeta ya shiga gari wurin yan uwansa. Ba wani rashin jin dadi ko takura a jikinta tayi fes da ita dama gwanar tsabtace ita don haka gyara a yanzu ya samu waje. A kullum ummah tazo takan min korafin yaushe zanzo naga mazaininta saidai inyi dariya kawai banyin magana. Ni damuwana yan uwan mu da muka baro a gida duk yadda birni ya lalace yafi kyau mu muna nan muna jin dadi su kuma suna can bamu san halin da suke ciki ba . Don ni a nawa ganin banga abinda zaisa ummah ta barsu a can hannun hardo ba tunda ita dai ba haihuwa take nema a yanzu ba. Har yakai na kasa magana da zata tafine nake fada mata damuwana akan yan uwan namu maza tunda ba wasu manya bane dai. Shine take fadin mijinta ya soma maganan hakan yana son su dawo wajenta don suci gaba da karatunsu itace bata bada goyon bayan hakan ba kada yan uwansa suce tana son mamaye masa gida. Ummah ai yasan kina da yara ya yarda ya aureki don haka a taimaka masu su samu suyi karatun nan suma bata dai ban amsa ba har ta tafi gashi ko wayansu muka kira ba,a samun su wasan dadi suna daji inda ba service.
Chapter 76 · 0% Book details