← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 306

Sashe 18

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da Ya J ya fitar da nasa tsaraban kai tsaye part din Iya yace Abubakar ya kai mashi a can wanan yana daga cikin sallon horon da yake son yi masu a mumuke . Bai tsaya ya karya kamar yadda Asmau ta bukataba gareshi wanka yashiga har yafito duk a cikin kyankyami yake haka ya shirya a cikin wani yadi fari na maza dayasha dinki kayan sun matukar karban jikinshi sosai ga ogogonsa daka kalla kasan bana ranke ranke bane. Haka takalman kafansa baki masu dan igiya daga baya amma ya taushe igiyan da dudugenshi ma,ana bai kaunan saka belt din takalman ke nan a lokacin. Turarensa ya dauko ya fesa a jiki abinka ga farin mutum nan kyauwonsa na asali dake rudin jama,a ga kuma jin dadin da jikin nasa ya nuna tare da wayewa sai hakan ya taru ya karawa jikin nasa ma,ana sosai. Duk cikin yaran mama Dubu ya jafar yafisu haske sosai duk da kaf diyanta fararene masu matukar kyau sosai sun biyo sashen mahaifinsu da yake shima farin bufulatanine daya bar gida tunda karanta don mutumin yolane zama ya kawosu Zaria shida iyayyensa amma komai nasu yanzu a cikin zaria suke rayuwansu da komai don yan bayama basu san gida ba. Part din Iya ya nufa inda ya samu mama tana kwashe dan abincin ranan data dafa masu yayi sallama ya shigo yana gaidasu da aiki nan yake fada mata zai fita yakai wankin mota ya kuma leka kawu dauda don sun shaku sosai da kawun nasa. Kusan duk wani motsin Jafar kawu dauda yasanshi shiya rike a matsayin mahaifi tun ma mahaifinsu yana raye kafin ya rasu. Cikin jin dadi mama take fadin ashe bari a bada tsarabansu saika mika masu daga can yace yayi mama yana zama yake fadin akawo nasu umma na mika masu don har can nake son shiga in gaidasu. Ka kyauta malam abinda zance ke nan ka rigani Allah yai maku albarka ta juya don taje dauko mashi sakon kafin ta juyo tana fadin ina ai matan naka sun gama abinci wajensu ko ? Sam baiji dadin zancen ba amma haka ya daure yace cikin bata fuska mama su ai basu gaj gama abinci da wuri ba banma jin sun dora yanzu gaskiya. Ikon Allah wanan waani irin sakacine da yaran nan miji da ake murnan zuwanshi amma su sam ba hankalin gane haka ai wanan shine kishi na asali ba wanan haukan da sukeyi ba. Yanzu sai ka dawo kaci ke nan yace ko karyawa banyi ba mama saidai idan na fita zan tsaya wani shago nan gaba kadan in karya. Sam malam ba mutuncika bane kana da mata biyu ka koma cin abincin layi wanan zubar da kimar namijine da matansa bari dai inzaka iya cin namu na zubo ma ka dan hada da ruwa. Murmushi ya sake a fuskansa daidai lokacin Habu zai shigo part din don shima fita zaiyi to ga sadauki nan sai in diba maku kuci gaba dayan ku ta wuce zuwa kitchen din kai tsaye. Abunci ta zubo masu plate biyu shimkafa da miya da ganyen kabeji yaji hadi sosai sai nama yanka bibiyu a cikin ko wani plate ta direwa kowa a gabansa. Yaso ya basar amma aiya muda ya busar da iska yana fadin yaya naga plate biyu mama matansa fa basu ciyar dashi bane halan ? Yayi kamar baiji mai dan uwan nasa ke fadi ba sai wayan shi dayake faman dakila cikin basarwa kafin ya aje yana jawo plate din abincin zuwa gabanshi. Mama Dubu data dawo dauke da goran kunun ayya sai ledan pure water ta aje Habu ya dago yana fadin is not right mama yana da mata a cikin gidan nan yazo nan kuma yana ci muna abincin mu. Murmushi mama din tayi kafin takai zaune tana fadin Habu dole ya kama in bashi son da yafita yana tonawa kansa asiri yaje saye shago gara kawai in diba mashi yaci a nan din. Duk zancen da sukeyi Jafar sai aika abincinsa yake a cikinsa Abubakar din ya dan kalleshi ya jawo plate dinsa shima ya soma ci kafin can ya dago yace. Cikin gari kayi ina son nima zan fita ka saukeni saiga iya ta fito daga daki tayi wanka ta sauya tufafi yadda takeyi idan mama tana gidan tare dasu ka,idace wanka a rana gareta . Habu ai gara ka bari yaci abincinsa a nan kada yunwa ya illantashi nima tsohuwa ba iya cin abincin yaran nan nakeyi ba balleshi matashi haka da harshensa yake da kaifi a yanzu. Amma iya gaskiya ba zasuji dadi hakan ba idan sungani shiya kamata ya tsawata masu koma meye su gyara amma haka gaskiya bai dace ba karshema zasu iya dora laifinne ga mama. Kamar yadda kace din ya kara tsawata masu dai hakan yana da kyau amma wa yan nan shedanun ba kan gadone dasu ba balle su gyara din. Tsuki Abubakar da takaici ya kumshi yaja goran kunnun ayya Jafar ya mika hannunsa ya dauko ya kafa baki ya korawa cikinsa kaf ya aje yana gyara zama yace. Ita Asmau ki barta da kazanta da saurin fushi yanzu haka dakinta wallahi iya baya shakuwa don kazanta kayane ako ina watse a dakin kamar wata wace ta tara yara goma. Itako Nusaiba aikinma bata san kansa ba barta kawai da in za a fita sai kice zakizo gidanta ki samu abin kwarai duk babu mai tsaba a cikinsu ga rashin kunya kamar tashin tasha bakinta ko yaushe baya gajiya. Nayi mamakin hada kawancesu da Asmau don ita ba yawan son maganane da ita ba amma ta iya zama da ita haka da wanan rayuwan na banza. Sam ban taba zaton haka rayuwanta yake ba harna yarda na fada tarkonta dariya sosai Abubakar ya kwashe dashi jin abinda dan uwan nasa ya fada inda sabo ya saba da halin Abubukar na kyata don a haka suka taso dashi. Daga can kusurwan kitchen mama ke fadin ina aika diban ma matanka nasu tsaraban ko kada azo a kwshe a nan ? Kafin yai magana Iya tace zai shigo dashi baikai masu nasu bane ai baya kawo nan baki daya yakan fitar masu da nasu tuncan hakan yasa taci gaba da fitarwa kawu dauda da abokan zamanta indai ankai can su raba a tsakaninsu . Saida ya mike yake fadin gari iya na sawowa shi don kune masu son jan garin kwaki da manja aina gani malam saida nayi tunanen hakan Allah yayi albarka amma wanan ai yayiwa Iya yawa bari a dibawa mutane suma susa albarka. Baiyi magana ba don ko yayi tunda mama tayi niyar hakan saita diba din donshine basu tsaya bata bakinsu ba ta fitar da wanda zaikai gidansu dana gidan kawu din Abubakar ya tayashi kwasa zuwa cikon mota saida suka cika mota fam suka tafi. Gidansu ya fara tsayawa aka sauke kayan zuwa cikin gida kafin su shiga don gaida mutanen gidan shigansu Abubakar ya kalli part din mahaifiyarsu dan kwana biyun da tayi wajen yai kura an rasa wanda zai share mata shi don mugun hali irin na dan Adam. Da ace mama mutuwa tayi ashe gidan ma ba zai basu sha,awan shigowa bake nan kilama wanine zai gaje wajen ya zauna aci albarkacinsu. A gurguje aka gaisa suna masu sannu da hanya tare da godiya kan tsaraban da aka kawo din agaida mama da dai sauransu. Basu tsaya ba sukai sallama suka fice daga gidan kai tsaye suna fita inna ta kalli yar uwar zamanta tace mena fada maku yaya indai yayan Jushuce sai ta aiko muna dako kwarane a gidan nan yanzu ji wanan kaya don Allah haka. Tsuki mama taja tana fadin meye a cikin ledojin nan sabira bude muga abinda ke ciki inda kowa na gidan ya fito ya tsaya ganin abin arzikin da aka shigo dashi din don basu yarda a shiga ciki dashi don gudun rage masu kwantiti dinsa da suka san za a iya hakan don an sabayi masu hakan kuma ba daman suyi magana a kai. Mama duba wanan abin ta fada bayan ta bude ledan inna takai ido ta kalla tace nasan wanan sai yayan jushu ita kadai takai can a gidan nan. Kaico waike karima baki kishin kankine wanan katobara haka da nuna zalama a filin Allah kamar wata mayunwaciya dake ? Nidana nuna a fili za,acewa hakan ba amma kowa anan ai yana so don ban taba ganin wanda akabawa ya marya ba a cikin mu. Nidai don Allah ku bari sabira ta fada cikin dan hasala ga iyayyen nata dake son nuna halinsu fadane akulum sai anyisa kuma a shirya haka ake zaune a gidan tsakaninsu. Mama Dubuce yana da wuya kaji harshenta a cikinsu tunko mijin nasu yana a raye kafin ya kwanta dama haka halinta yake ita bata son yawan hayaniya . Sunyi mamaki kwarai da irin abinda mama Dubu ta aiko masu dashi nan gidansu su raba ke nan yana can gidansu baja baja ke nan tunda har ta iya basu haka ? Kai tsaye ya Jafar motarsa yabada wanki a nan kasan unguwarsu ya hau mashin zuwa gidan kawu Dauda da sakon tsarabanshi cikin buhu. Ya samu baba din ya fito zai fita ganinsa hakan ya dakata yana fadin malam kaine tafe yaushe garin ? Yace jiya da dare kawu yana fada yana kokarin dauko buhun da mama ta bashi ya shiga masu dashi cikin gida kai tsaye nan suka tsaya gaisawa da matarshi tana mashi yaushe gari ? Sai bayab sun gama gaisawa yake fadin mama tace a shigo da wanan au ka biya ta gidanta ke nan kawu ya tambaya yace tana wajen iya ai. Kace tayi tataki zuwa kwasan lada nimafa yau nake zancen naje nagonasu na kwana biyu ban lakasu ba kawu ya fada ya kara da yaya wajen iyalin naka suna lafiya Jafar ya bashi amsa. Fita sukayi tare da kawu din dake tambayanshi baizo da mota bane wanan karon yace nazo da ita kawu tana wajen waki nakaita can tudun wanda. Ai hakanma na dakyau wuri suka samu suka tsaya daga kofa kawu din ke fadin naga kamar kazo da magana a bakinka ? Yadan kara rankwafawa kafin ya fuskaci kawu yana fadin nazo dashi kawu shawara nazo nema
Chapter 18 · 0% Book details