← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 293 OF 306

Sashe 293

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ba. Da bakin ki nan gaban mutane gaban kowa kikace saidai ya bar gidashi amma ba sarakuwarki ba yar so a gareki yace ya yarda yanzu zakice kuma bai isa ba ? To iya ana son a nuna min iyakata ke nan da ban isa dasu ba yanzu tunda sun girma suna ganin sun kai iyan tace na dai fada maki kar inji kar in gani duk kika tofa wani kalma akan zance irinsa zai biyo bayan ki dubu. Tabbas idan naji kona gani kinsan zancen kema don haihuwa baifi haihuwa ba dubu kin tauye yaran nan dayawa dubu tun suna maki biyayya yadda akeso har yanzu yakai sun daina suna ra,ayin kansu tunda sunkai mutane suma ? Kuka sosai mama keyi saida iya tace tashi kaje Allah yasa ku shiga a sa,a nina taba ganin haka danka ya samu karuwa irin haka ke mahaifiya kice ba a isa ba ? Yau ko kango mutum yana son ace ga nasa balle ke da Allah ubangiji ya yayi maki Rahama ya fida diyan ki cikin yan uba kece kuma da kanki kike son ki bata abinki yanzu da hannun ki ? Iya ba hakana bane koda nace su zauna nan don hadin kansune ba don komai ba amma tunda hakane ai shike nan suje Allah ya bada sa,a . Ya daga yana fadin mama kiyi hakkuri ni dama ina da niyar hakan wallahi ba don zancen nan nayi haka ba tsawa iya tayi mai tana fadin jeka nace ubangiji Allah ya tsare mun koma godewa Allah daya nuna muna hakan gareku tun muna raye. Yau idan mahaifinku yana rayene akwai wanda ya isa yayi maku wanan rayuwan tauyewan da ake maku yanzu komai yaro zaiyi naci gaba sai a hanasu ? Haka ya mike yabar part din ya samu samari nata daukan kaya suna fita dashi yace ke banda tarkace ba zan yarda yadda kuka bata nan ku bata can ba yanzu iya kayan amfaninki dana yara kadai zaku dauka wanan tarkacen duk ku barsu nan. Yayi mamakin rashin ganin Saiba da baiyi ba ashe ta fita zuwa unguwa har aka gama bata dawo ba sai bayan tafiyansu kadan ta shigo gidan tun a waje take ganin tarkace hakan ya bata mamaki ta karasa ciki da mamaki a fuskanta zuwa cikin gidan. Ba kowa a waje nan ma tayi mamakin ganin falin a hargitse haka tadai shiga ta aje kayanta ta fito tana kiran Asmau shiru da taji ta koma kiran yara shima shiru hannun yarta ta kama zuwa part din mama. Mace kadai a lokacin gidan Salima tana gidan mu iya kuma tana nata wajen taki fitowa tunda ta gama magananta a lokacin. Mama lafiya ina Asmau na dawo na samu waje a hargitse haka wani abu akayine bayana kuma ban sani ba ? Da kyat mama ta iya bude baki tace Nisaiba ni Jafar zai nunawa iyakata da nace ya bar gidan ba zaki bari ba shine yau ya dauki Asmau wai ashe ya gina gida tun tuni ban sani ba ? Kam uban nan ya dauke tafa mama wallahi sunyi kadan dagashi har ita sunyi kadan wallahi duk inda suka koma nima zan samesu yau din nan me jafar yake nufi dani . Harta juya zata tafi sai kuma ta juyo tana fadin koma meye mama laifinkine na nuna maku so da kauna an hada kai dake an cuce yan uwana basu fadi karya ba kece ke amfani dani bani ba ? Nisaiba kanki daya kuwa tace kwarai kuwa nagane kinyi amfani danine don wata manufa taki ta daban mudfin aure na ya mutu mu zuba auren kowa ma zai mutu wallahi. Ta juya zata fita suka hade da kawu kamar zata bangajeshi ya kauce gefe daya ya bata waje ta shige shi ya bita da kallo yana mamakinta. Kawu ya karasa falon yana fadin wai gidan nan lafiya meke faruwa naga duk gidan a hargitse yaya iso dolene kaga gidan haka hargitse yaran nan sun gama dani kuma iya ta hanani daukan mataki ? Meya faru ni baki fada min kina kawo min zancen iya to zance iya mana wai Jafarne ya dauki matarsa uwargidan suka bargidan nan kamar yadda habu yayi a baya ? Suka bargida ya koma ina gidan haya ko can inda ya aje wanan yarinyar ya kaisu aida canne ban mamaki haka yaya ? Gidafa jafar ya gina ban sani ba kamar yadda Habu yayi min sai daukan matarshi su tare kawai naji zanyi magana iya tace ban isa ba ina na fito yanzu yaya abinda iya keyi min kan yaran nan yayi daidai ke nan don Allah ? Zaudowa yayi zuwa bakin kujera ya dubi yar uwar tashi yace yanzu shi jafar yana da kudin gina gida shine ya bari dan uwansa mara mutunci na kokarin daureni gidan yari ! Haba yaya kasan bakinsu daya na yarda bakin su daya shike nan ni Dauda yaran nab duk sun bata min shiri kaiya bukata bai biya tako ina je nan ? Bukatan me kuma yaya kedai bari Dubu bar zancen kawai shike nan ai komai ya tafi yanzu bar wanan zancen kuma yanzu ina jafar yake ? Sun kwashe ta fada a sayayye cikin bacin rai sun kwashe fa to ita wanan data fita yanzu kamar zata bangajeni fa ? Ai kasan ya furta saki a tsakaninsu nace ta zauna shine yabar min ita nan baije da ita ba yanzu ta dawo take masifa kasan bata da kwanciyar hankalin fahinta. Naso ince ki rabu da ita ki kama wacan yar fulanin muyi makami da ita a gareshi yanzu tunda wanan din ta koma bata da fada wajenshi a yanzu bata da sauran amfani a garemu. Muryan wa nakeji kamar na dauda muryan iya ya katse masu magana iya nine shigowana ke nan yanzu nake zance naje na gaida ke ai. A,a ina zaka gaidani kana nan kuna kulla shu,umancin naku da bansan sai yaushe zakuyi hankali ku daina bibiyan yaran nan ba tunda ita uwarsu ka gama da ita dakai da matarka. Iya mungama da ita kwarai kuwa ko kana zaton ban sani ba ita din yar uwarkace dauda duk surukullen da kaiwa dubu ya hau kanta yar uwarkace dai kanka kayiwa. Godiyana ga Allah dana yaran nan baiyi tasiri ba kun halakata kun koma kuna neman halaka mata diya koka dauka duk dadewan nan ban sani bane ? Nasan komai dauda ina kuma kai kukana ga Allah ganin na yaran baiyi tasiri ba yasa kaga na sakama ido kuna ta bace nasan mai hansatu takewa kuka lokacin daka kara mata kishiya ai ? Shiru yayi iya ta zuba ta zuba yana zaune baice komai ta kare da fadin dauda na dade da kumsan bakin cikin ka a zuciyana sai ince ni banga amfanin haihuwan da namiji a rayuwata ba don hansatu ta shiga ta fita ta rabaka da kowa naka a duniyan nan. Ni kuma na dade ina kai kukana ga ubangiji Allah ina fada mashi damuwata akanku har gashi yau kana fada da bakinka komai yana da iyaka banda ikon Allah da manzonsa. Tana fadan hakan ta juya ta fice takai kofa take fadin Allah yasa yaron nan yazidu ya daureka a kotun nan dan makulin ya bace ka mutu can dan banza mara imani ka halaka kanka ka halaka yar uwarka saboda macen macen ma figgaga kamar hansatu wai daba gaba ba baya. Kun gani ai dakai da ita kaso diyan yar uwarka su tabade kamarka da Allah yafiku sai yabaku tambadadun diyan ku ya shirya mata nata. Tasa kai ta fita ta barshi yana hawaye sai mace da bata san kaiba take fadin ni iya fadan ta yakan ban mamaki wani lokaci bata barin mutane suji da abindake damunsu a rayuwa.
Chapter 293 · 0% Book details