Sashe 228
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
tana masa karatun kur,ani tana sallolinta tana bashi magani tana tofeshi ko yaushe ka falko kana iskata a kan shi tana mashi addu,a. Tau ku sani idan jinyar yaron nan ya koma kasa kada kuyi kuka da kowa kuyi kuka da kanku wallahi don daku aka hada kai aka koreta a gidan nan yau. Dama makiran kishiya tafi mai fitina hatsari don gara mai fitina tana fitowa fili ka fahinceta amma wace ke sari ka noke itace guba mai cutarwa farat daya. To yanzu fissabillahi yaya daga dan maganan fatar baki saita kwasa tayi fushi tana fadin magana haka dama dai ai sallon ta samu hanyar kubucewace tayi don ta nuna ta gaji hakana ? Yanzu idan bata zo ba sin yadda tace ai zai nade ya bita can din inda ta saba cin karanta babu babbaka ana kallonta can ko sai abinda taga dama tayi. Itama yar kauye tasan tayi wanan shirin ga mutane balle muna da aka haifa a cikin gari taje wa zuwanta ya dama a gidan nan koda ita ko ba ita in Allah ya bashi lafiya sai ya mike da yardan Allah. Kaico iya dake tafe tana gyara daurin dan kwalinta take fadin haka badai da abokiyar zaman naki ba kuma kike wanan abin kunyan haka ? Aa,ha iya badani bace da dai sarakuwartace da yaranta tunda su ba ai masu fada nikan ai kafin nima su koreni din yau zan koma dakina insha Allahu kar abin ya juyo kaina yanzu kuma ? Yaya sai kinso saka kanki cikin zancen nan gaskiya don wallahi dai bada ke akeyi ba kin sani yaran nan kuma kin dai san dan yau banice zan turasu sunawa matan dan uwansu haka ba ? Wai sai meyasa matan jafar ne ko kafin yarinyar nan ta auri Jafar ai yar uwarta habu ya fara aurowa gidan nan da zaku dauki karan tsana ku sakawa yarinya guda duk kokarinta ga dan uwanku. Aike Amina baki sani bane dan uwanne nasu basa so shiya kawo haka kiyayyan jafar dasune ya shafi amaryansa . Haba iya in antashi magana kiyi ta hadawa dani don Allah ni yanzu mena cewa Rahama anan daga muna maida maganan zagin da Nusaiba tayiwa Asmau shike nan fa tayi fushi inma maganane ai ita Asmau itace ke fadin magana da har ya shafeta ni meye nawa a cikin zancensu. Tun bayan fitana daga gida kuka baizo min ba asalima taxi na tare zuwa gidan saidai inata faman sakawa da kwancewa a kasan raina. Ina shawaran barin garin a ranan in nufi abuja ko adamawan cameroom gun yan uwan mu zaifi min sauki a rayuwata sam ban taba nasa cewa zanwa wani shige shige a wajen boka ko malami da sunan in kuntatawa wani. Amma sai gashi ban tsira wajen sherin abokan zama ba kullum duba sukeyi ina da asirin da nakewa mijin namu yasa bai yarda yaga laifina. Duk magana idan zai taso nice wai za a bawa gaskiya na sani ai na kuma san irin azaban da Allah zaiwa mutum. Nagama komai na shiri kwance na dawo falo don in danci wani abu duk da bakin nawa ba dadi a lokacin amma haka nake daurewa kamar yadda manyana suka fada min. Ance in daure ko bakina ba dadi in dinga cin abincin ya kasance ina da kuzarina dan kada na lalace abin cikin cikina kuma zai wahala . Fruits din dana sayo a hanya da zan dawo na yanka nake sha naji bugun kofa don munyi da Biba saida safe zata dawo ranan don haka ni kadai ke nan zan kwana a ranan sai megadin gidan dake waje. Daga ciki nake tambayan ko waye muryan ya Yazid naji yana fadin bude mune da iya hakan yasa na dauki gyalena dake gefe na yafa akaina na bude kofan. Shida iyace sai matarshi da yaransu sukazo na danyi murmushin dole a fuskana ina fadin kune a gidan yau ? Ba doleba ance amarya mu tayi fushi harda rantsuwa ba zata sake taka gidan muba murmushi yake na komayi ban daiyi magana har lokacin. Muka samu waje muka zauna dukkan mu a falo na mike na dauki sauran fruit din a cikin fridge din na kawo masu sai bin ko ina na fidan sukeyi da kallo. Iya ke fadin kagani ko na fadama ko acan din tauye take don laluran nan ne kawai yake kaita amma yaran nan yau saida suka kure hakkurin yatinyar nan. Ai tunda nadon su takeyi ba iya ba zatabi ta nasu ba tace bata kara zuwa ganinsa yanzu gashi can kun barshi ya rikice bayan tafiyan ku ita mama tayi fushi ta wuce gida ke kuma kin dawo nan ke kadai ina yarinyar da kuke zama da ita din ? Saidana hade wani malolon bakin ciki nake fadin tana gida yau yar uwarta ta haihu suna suna sam banyi tunanen zaki bari suci galaba akanki ba ai tunda kinsan da gaiya suke abinsu. Kowa yasan meyasa Saratu take hakan ni dai na dauka ba banza take hakan ba don ban taga ganin inda mutum yaki dan uwasa ba haka ? Amina tun bata kai gida ba nasa aka dawo da ita kema munzone da safe idan Allah ya kaimu ki shirya yadda kika saba kizo ki duba mijinki kinji na amsa masu tare da godiya. Sun dan jima a zaune iya ta matsa akan su tafi dare yayi don sam ita bata fitan dare wanan fitowan ma ya kanane haka. Nayi masu rakiya akan washegarin zan shigo suka tafi matarshi sai bina da kallo takeyi kawai don hausan a lokacin take koyonsa. Bayan sun wuce ina shiga daki na jawo dan jakkata na hada kayan bukatana a cikinsa nayi ready komai na saka a jakar safiya kawai nake jira a lokacin. Barci sama sama nayishi a ranan don abinda na yanke a raina gidan ga baki daya ya fice min a rai abin cikin cikina kuma yana ban tausayi. Don nasan haka zai taso da kalubali idan ban dauki matakin hakan ba tun yanzu don haka dole in kauce in samu a daukar min mataki akan saratun nan da kowa ma don har mama gaskiya. Washegari sallah kawai nayi na zauna addua na jira gari ya dan haska na fito inacewa maigadi zani can gidan kila in kwana biyu a can din waman zuwan. Yana ta min adawo lafiya yana gaida maigida shiya tare min keke na hau ina sauke ajiyan zuwa dana bar wajen muna fita titi nacewa mai keken kaini tasha in shiga motan kaduna. Ya dauki hanya sai tasha din muna zuwa ga mota saura mutum biyu zuwa kaduna na sallameshi na biya kudin mota na fada. Saiga cikon na karshen yazo muka daga na sauke ajiyan zuciya ina jan hijjab dina zuwa hancina saida muka bar zaria na sake gyara zama ina lumshe idona. Mai karatu abinda yasa banje abuja ba son zuwan dasu daddy sukayi na nuna masu zan daure da duk wani abinda zan gani amma yanzu na kasa hakan . Gara inje wurin ummah zaifi min duk da banson zuwa gidan nasu don yadda mijin nata yake like da ita kamar wasu yara hakan kan ban haushi idan na tuna da mahaifin mu da basuyi irin wanan rayuwan barikin dashi ba haka har ya tafi kullum shi yana kofan gida yana tsaro wajen aikinshi ko in daddy yana gari su fita tare dashi din. Amma shi wanan ya samu wanan daman da mahaifin mu bai samu ba Allah ya gani ina taya mahaifin mu kishi a kansa gaskiya. Ashe yazid ya biyoni zuwa gidan ya daukeni ya samu ban gidan maigadi ke fada mashi ai tun safe na fita da jakata nace can gidan zani a lokacin. Gidan mu tace dakai zata ni yanzu daga gidan nake ai fitowana ke nan nazo nan don jikin mijin nata ya dan tashi subbahanallahi maigadi ya fada ya dora da fadin har da jakar kaya ta fita ai nina saka mata a mota don tace wanan karon zata kwana biyu a can din. Waya ya daga ya kira yana tambaya ake ce mai to ban iso ba ya juya ya fita sun kira wayana a kashe yasa suka kira Maria ta dauka cikin sanyin muryan nan nata suka gaisa bai tsaya ba yace ko amaryan J tana wajenkine sister ki ? Rahama ta fada cikin mamaki ta dora da fadin wallahi bata zo nan ba ai mun kwana biyu gaskiya yake fadin habu bai dawo bane ? Ta amsa maida yace sai jibi zai dawo bai tsaya ba ya kashe wayan ya karasa gida sun ta maganan maman tudu ke dadin dama nasan zatayi gaba tamayi kokari tunda har takai war hakan. Bafulacene zai tsaya ana gardaman abinda yake da gaskiya a kansa tayi kokari dama ta zauna ai tunda tana son mijinta yanzu dai kubar zancen nan kada yaji don Allah mama ta fada. Basu sameni ba sai zuwa yamma nayi barci na tashine suka sameni kira ukku na dauka da sallama muryan yazid ne yake fadin Amaryan J kina ina don Allah ? Hanyar garin mu na bashi amsa na kashe wayan ban tsaya saurara mashi ba don ban son yawan magana tunda mun kwasa da ummah tun isowana.