← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 167 OF 306

Sashe 167

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

da zaman lafiyan da sukeyi ashe ? Ga dan uwankinan inba ya zama munafuki ba da bai iya fada maki gaskiya sai akasin hakan ko yaushe shi yanzu daya samu wata da take dadada masa ai gashi da tsufansa yana sabari a kanta da yayan angolan datazo mashi dasu gidansa. Kiyiwa kanki karatun ta natsu tun kafin yaran na su gane nufinki a kansu dubu su fara mayar maki da martani don dai yayanki ba rabuwa zasuyi dasu ba kin sani. Ba kansu ai aka fara irin wanan hadin ba tunda Allah bai hana ba har uba yakan auri kanwa da ya auri ya duk bai zama illa ba sai a gidan ki dubu kina kokari kija da ayar Allah da Annabinsa a nan kinki kwantar da hankalinki kiki bari na yaro ya kwanta kuma ? Yazidu kuma kinsanshi kinsan halinsa to ki matsa dubu kikai ga abinda ba aso akai din har yan uwanki su samu shiga kina kallo ke kikajawa kanki hakan kuma ba wani ba ? Nina rasa gane matsalan ki idan na tariyo sai inga duk laifin na daudane don ke kamar kanki a burge yake yanzu tun mutuwan mijiku kuwa nake hango hakan dama shine katangan daya tare duk wasu matsalolin da za a fahinci hakan a gareki. Yanzu dai shawaran da zan bayar a nan shine ita mama tayi hakkuri har yazid din yazo da matar nasa aga mata wace irin rayuwa ke gareta don Allah a fanci juna shine zaifi tunda ya riga yayi wanan kuskuren ko ? Banso dubu ta matsa akan zancen nan ba amma tace sai mu taso a san yadda za ayi ya baro matarsa ya dawo nan shi kadai kawu ke fadan hakan . Iya tace kaji shirme ko na fada maku dubu ta canza a yanzu ina kuka kwana da zancen da nayi maku zuwa biyan bashin dake kankune dauda ? Wanan ya kamata ace kunyi ba wanan shirme ba dakukeyi a yanzu auren da aka samu zuria a tsakani ina ke ina shiga tsakaninsa kuma yanzu ? Zamuje iya wajen ne yake da wahalan zuwa amma za aje din tace sai yaushe zaku tafi ko sai kunga sun fara zaran yaran daya bayan daya zaku maida hankali ga tafiyan ? Goben nan ko jibi nake son duk abinda kukeyi ku maida hankali a tafi wajen nan don naji jafaru yana zancen komawa wajen sana,anshi cikin kwanakin nan. Zubur kawu yayi yana fadin gobe iya iya tace kwarai kai harni zamu tafi ba wai ku kadai ba idan baku shirya ba kuyi kwatance mu tafi nida yaran nan . Ku diba yaron nan ko bai fada ba ansan da abinda ke damunsa don yana namijin tsayene baku gane hakan sai ya fadi kasa kuji dadin hakan ?
Chapter 167 · 0% Book details