← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 306

Sashe 142

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kawu daudane zaune a gaban iya data kura mai ido cikin mamaki don jin zancen dayake koro mata a lokacin na karin aurensa dayayi. Saida ta nisa ta sake fadin dauda kace ka kara aure ma,ana har kayi auren ke nan ma ? Wallahi an daura auren yau kimanin sati biyu ke nan don dana tura su baffa neman aure shine iyayyenta sukai karamci tunda ba budurwa bace a daura auren gabadaya lokaci guda. Kwarai kuwa to me za a tsaya jira kace ka fasa hakan ai yayi sosai gara da aka daura din ma yafi sauki yana washe baki yace wallahi iya nima haka nagani. Ehh lalai abu yayi kyau tunda duniya sabuwa fil a yanzu gidan ka dauda ni ba zance kada kayi aure ba don Allah ubangiji ya yardan maka da hakan kaga kuwa ban isa ince don me ba dauda to amma ina fatan ba dukiyan yaran nan kake facaka dashi ba dauda ? Assha iya assha haba ina sane budi daine ubangiji yayi min a yanzu amma dama ina da niyar hakan a raina sai yanzu Allah ya nufa ayi. Wananfa shine damuwata da auren ka a yanzu karka samu dukiyan mutane kana facaka a cikinsa don amana da cancantan hakan yasa suka mika maka. Kaga ko amanace mai nauyi ya hau kanka dauda amana ko wuyan sha,ani ke garesa musan irin wanan amanan dukiyan marayu ba kowane ke yarda ya rika ba. Ina zan yarda iya asalima dukiyan nan basu hannu don ban yarda na ajesu a wajena ba don haka karki ko kawo wanan tunanen a zuciyarki iya. Ai Dubu mutumce samun mai irin halin dubu akan zumunci sai antona gaskiya donshine nake taka tsantsan da komai nasu dake hannuna. Ni dai Ka daiji abinda na fada kayi hankali a samu a rabu lafiya ni tun farko da kunji maganata da ba,a karbi kudin nan hannun yaron nan ba da an barshi dasu ya dinga juyawa a wajensa yafi kwanciyan hankali amma kunce a,a kai da yar uwarka Allah ya sauwaka ya amsa da amin. Sun gama hira zai tafi ya fito da goro manya farare ya aje mata a gabanta yana fadin iya ga wanan na biya na sayo maki da zanzo. Tayi godiya tare da fadin to a dai kula don Allah kuma a hada da hakkuri da iyali baki daya hafsatu dai kasan irin hakkurin da tayi dakai na tsawon shekaru a gidan ka don haka ayi adalci don Allah. Kitchen nake ina hada breakfast don ina son shiga school muna da test amma sai zuwa rana don haka na tashi da wuri ina yan aiyukan gida. Anty Nafisa ta fito ta sameni muka gaisa take fadin ashe har kin fito yanzu nace bari na fito na dora abin karyawa duk da bansan abinda zaki dafawa yaya din ba yau. Murmushi nayi ina fadin ai har na hada anty nagode yanzu ma miya nake son hadawa anjima dana dawo abinci kawai zan dafa. Banjin zankai rana a gidan nan da nace ki barshi amma da wuri nake son zuwa na gyaro dakin mama dan kila yau din nan zasu dawo. Allah ya dawo dasu lafiya na fada ta amsa da amin tace sai kuma zancen salima na jiya don Allah Rahama banson kina damuwa da irin maganganun su don su basu dauki hakan wani abu ba. Da mai mata da mara mata dukkansu biyun zaman lafiya akajawa ba wani abuba don haka kiyi zamanki a dakinki lafiya da mijinki Rahama. Itama Salim din nayi mata fadan irin wanan magana tace wallahi bata san zai bata maki rai ba don haka kiyi hakkuri don Allah dai. Abin tsaman dana dauka na juya dankali na aje ina fadin la anry wallahi ban dauki wanan maganan nata wani abuba sam wallahi. Ita ta tayani karasa aikin har na samu naje nayi wanka da wuri na samu na fito a daidai lokacin da yaya Habu yayo sammakon zuwa gidan. Na gaisa dashi kana na nufi dakin yaya don in fada mashi zuwan yaya Habu din kwance na sameshi yana barci dama yace min barci yake son ya samu ya danyi don ya gaji da yawa. Gashi kuma ya hana kanshi hutu da dare saida na yabawa aya zaki duk wani gajiyansa ya rage saukewa a kaina cikin daren. Na rasa yadda zanyi na tayar dashi hakan yasa na kai zaune a gefen shi a hankali nakai hannuna saman wuyanshi na shafa kana na mayar da hannun akan kirjinsa. Firgigit ya bude idonsa ya sauke a kaina ya dan motsa yana mika yake fadin wallahi nagaji Rahama banda time din hutu a can koda da darene balle da rana. Yaya habu ne yazo yana falo na fada tare da kura mai ido naga ya danyi tsuki yana fadin karfe nawa yanzu na bashi amsa da almost to nine fa ? Kai ya fada sai ya mayar da idonsa ya lumshe zakai wankane kafin ka fita yaya na tambayesa ? Ya bude idonsa yana fadin naso hakan amma bari na ganshi tukun in dawo ya kara kallona yana fadin har kinyi wanka ke nan ? Nayi ina shirin tafiya school ne yanzu abinci na falo na hadama ko bari na hada ruwan wankan kadin ka dawo don nasan fita zakuyi kila ? Na fada ina mikewa ya miko min hannu wai in dagashi dan murmushi nayi din nasan ina ni ina iya daga mutum kamarsa amma banki ba na mika mashi hannun nawa ya jawoni da karfi na fada mashi a jiki ya rungumeni. Bai sakeni ba saida ya dan jahagulani ta hanyar kiss na samu dai ya sakeni yana fadin barin je naganshi tunda korata akayi jiya aka nuna min ba a maraba dani nan . Na samu na mike tsaye ina fadin ba hakana bane yaya tsoron shiga hakkin da ba nawa ba nakeyi ga hakan baidai yi magana ba ya mike shima. Nakai kofan bayin naji yace nasan abinda nakeyi sarai Rahama duk abinda kikaga nayi ina da dalilin yin hakan so ki barni kawai na fiki tsoron hakan a zuciyana. Ni dai banyi maganan ba na shige bayin na fara gyarawa don amfanin da mukayi dashi da safe na wanko na fesa kamshi na hada mashi ruwan dumi na fice zuwa dakin shima na gyara shi fes kafin na fito daga dakin. Tsabta da yake so a zuciyarsa yakai karshe don haka nima nake ban son kazanta ko kadan abu kadan na kazanta yanzune zai tayar min da hankali har tsikan jikina sai ya dinga tashi kan hakan. Tare na samesu suna karyawa dasu don harda Nura ya shigo ashe nasan Nuran tun ban auresa ba don yana da wuya idan yana gari bai tare da Nuran abokinsane sosai shakikinsa. Hakan yasa na tsaya gaida Nura zan shige naji yaya din ba fadin Rahama karfe nawa zaki shiga school ne ina son yin amfani da motarki idan ibrahim ya saukeki ya dawo zan fita da ita don nawa ba zasu shiga ba yanzu sai an wanke min su. Yanzun nan zan shirya in tafi don test zamu rubuta yau Ok ya fada idan ya saukeki sai ya dawo ya daukeni ni dai na shige daki abina. Na karasa shiri daidai yaya Ibrahim yazo don bai saba time gaskiya inba lokacin da yakai mama kaduna dauko Saiba ba shine na biyo motan su Nuratu na dawo gida don basu dawo garin ba sai bayan isha,i a ranan. Nayi tuya na manta da albasa don da ta buga zata kaduna yaya Habu yace yayi tafiya shine mama tace zatabi motar haya yaya habu din yace ta kira ibrahim yazo ya kaita. A hanyarsu ta dawowane mamake tambaya dama makulin motar tana hannun ka ke nan ibrahim yace ehh mama kinsan Amaryan yaya ke amfani dashi ita ake kawai school da motan . Nan saiba taji wani sabon malolo ya tokareta a makoshi har suka kawo zaria bata kara magana ba sai ajiyan zuciya da take saukewa lokacin. Haka shima yaya daya shiga motar ya tayar yake tambayab ibrahim din da zai sauke ya akayi yaji motar a haka don indai iyaka school da yake kaini ai baci ace tana wanan karan ba ? Ya ibrahim din yace ranan da nakai mama kaduna da zata dawo da Saiba shine naji tana wanan kara na so nakaita wajen gyara naji kuma tabar kara yasa ban kai ba gashi kuma yau tanayi again. Da wanan motar kaisu kaduna ina motar dana aje donsu a can yace to ban sani ba nidai mama dince ta kirani inzo da mota in kaisu kaduna ita da saratu shine na dauki wanan na kaisu. Baiyi magana ba ya saukeshi shida Nafisa ya wuce da salima gida sai ganinsa sukayi kwatsam don ba wanda yasan da dawowan shi a gidan. Part din iya ya nufa tana zaune ta gashi tare da salima hannu ta fara tafawa tana fadin lale lale da Jafaru yaushe garin inji maki bako saukan yaushe jafaru da safen nan haka ? Iya jiya na dawo ta amsa da to sannu da zuwa yaya can ta dai shiga tambayansa irin na al,ada yana amsawa da alhamdullahi. Ga uwar taku ko yau zasu dawo sun tafi sokoto duba yar nan da take aure can tun shekaran jiya ko yau zasu dawone oho ? To sun tafi duba hauwa ke nan don yar wajen mamace ke aure a sokoto din akaiwa aiki wajen haihuwa shine suka tafi dubanta sai suka samu tana jin jiki suka kara kwana. Nan dai iyan tayi mai bayani ya mike yana fadin barin leka wa yancan ingansu ai ba gidan nan ka kwana ke nan ba ? Yace a,a iya wancan gidan na sauka yanzu shigowata kenan nan din a daidai lokacin Saratu ta fito daga daki tana fadin sannu da dawowa yaya. Au ke kina ciki ke nan jelar mama aina dauka tare kuka tafi dasu mama din ta amsa da ehh na dan kwantane naji muryan ka nafito. Kaji makira tana daki tun safe bata lekoni ba da badon yar nan matar habu ba wana shashashan data kasheni da yunwa a gidan nan tunda ba iya girkawa zanyi ba ba kafa kasani ta fada tana nuna mashi kafan nata. Saratu din ya kalla yana
Chapter 142 · 0% Book details