← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 306

Sashe 25

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

min wata kila a part din iyace kamshin ke tashi. Baki saiba ta tabe ta gyara zama tana fadin kamshi kamar wani girkin kwarai ina bafulatana ta iya girki banda tatsan nonon shanu. Badai gyaran gyaran ba tayi mai wanan da gani daban take a cikin fulani don tayi kama da wace ta zauna a birni ba a cikin daji ba. Bayan magariba Ramaah tayi sallama part din Iya ta sauke kayan abincin data dauko niki niki tana gaidasu inda suke zaune. Abincine Yanda tace na kawo cikin murmushi mama tace a,a abincin hardamu aka sakawa angode aida tayi iya bakinku sai mijinta. Sare ce ta mike ta karba suna fadin sun gode har Ramah din ta juya taji muryan mama na fadin. Nace ba idan kun karasa aikin a can anan wajen Iya zaki dawo da kwana idan kin karasa saiki dawo nan din ki kwanta kinji. Ta amsa a ladabce ta fita na part din ya J ta dauka ta mika masu inda ta samesu zaune a falo duk da hiran nasu ba wani hiran arziki bane mai tsawo. Amma ya zama dole garesu don dokan da maigida ya kafa a kansu yanzu kuma kowa na tsoron yayi abinda zai bantale masa auren a lokacin da suke jin dadinsa. Gaidasu ta fara a falon ta dire abincin acikin wani kula mai kyau tana fadin abincine daga wajen amarya a gyatsine Saiba ke fadin ta aje a saman table din. Babu wace tace angode a cikinsu ko a gaidasu da mai girki ba wace ta iya fadan hakan a cikinsu haka yarinyar ta fita tana mamakin hali irin nasu. Part din yar uwan ta koma taci abinci saida ta gama ta mike take fada mata abinda mama dubu tace dan shiru yar uwar tayi indai son samune taso a barta da yar uwanta da take amana a wajenta yanzu ta zauna a wajenta din. Saidai ba yadda zatayine don umurnin mama dubu ne hakan tayi mata saida safe ta fita zuwa part din tsofin don ta fahinci ana son ta bar ango da amaryansane lokacin. A bangaren yaya Jafar kuma Ramaah ta fita bada dadewa ba saiga maigidan ya shigo suna mai sannu da zuwa ya amsa tare da bin kulolin da kallo ya kai zaune yana fadin wanan abincin fa ? Daga bangaren amaryan Habu aka kawosa Saiba ta fada tana mikewa donta dauko mashi abincinshi da suka girka a part din. Saidai taja ta tsaya tana bin maigidan da kallo wanda ta sama ya bude abincin yana zubawa tare da yaba yadda aka tsara komai cikin nuna wayewa da zallah gwaninta tare da iya tsabta da kuma sanin darajan dan adam. Bai jira wani cewa ba ya mika hannu ya fara serving din kanshi saiga Saiba ta fito da only warmer din data zuba mai ja,loop din taliyan da tayi na manja. Tunkan ta karaso ta soma magana tana fadin wanan abincin yarincan ne fa ga abincin ka nan na dauko maka ? Bai kullata ba yacigaba da zuba abincin a cikin plate iya yadda zai iya tare da fara zuba miyar yana jin wani irin tukuki a da zafin matan nasa na yadda basu iya tsayawa suyi girki haka irin da malam bahaushe ya sani saidai shiririta irin na shirmey din nan da matan yanzu keyi saboda sakaci. Mikewa yayi ya wanko hannunsa ya dawo ya zauna yana shirin zamane ta kara fadin J fa bafa nina girka ba wacan yarinyar ce matar Habu ta aiko muna dashi. Bissimillah taji yayi yana yankan tuwon ya fara kaiwa a bakinshi tare da lumshe ido don jin yadda tuwon ya hadu tsab rabo da yaji tuwo haka tun suna gida mahaifinsu yana raye mama na girki ta saka masu. Komai yaji acan acan kayan yaji na gargajiya sai dandanon daddawa ga kuma kamshin man shanu dake tashi gwanin ban sha,awa. Daidai Asmau data gama shirya danta ta fito dashi rugume a hannunta itama tabishi da kallo tare da mamaki ta zauna a saman kujera. Wai ikon Allah yanzu girkin nata zakaci J ya dago yana kai loma a bakinsa ya hade yake fadin wai wanan din sunansa me kin isheni da wanan abin da kike dafa da sunan abinci. Wanan din shine muka sani da abinci a gidan nan ba wanan shirmen da kukeyi ba ku diba yarinya karama tasan ta girka wanan abincin hakawa mutane ? Ku me yaci karfinku da ba zaku iya ba ya dauko gutsuren nama ya kai abakinsa ya lumshe ido kallon Asmau saiba tayi cikin mamaki itama ta lumshe idanunta. Tana fadin wai bari dai nima naci naji hannun ta da akewa yabo haka ta fara serving din kanta itama saida ta loda taja plate din gefenta ta fara ci. Loma biyu taci ta dago tana fadin kici kiji abincin ya hadu gaskiya ba laifi kici don Allah murmushi tayi cikin takaici tana kallon kulan dake hannunta ta dangware tana fadin wanan ai baiyi ba. Ta fara jan plate din ta bude ta zuba kadan don ta gano matsalan abincin ta fada ta soki wanan girkin da taga suna santinsa. Saidai ta cinye wanda ta zuba din ba tare da tasan tayi hakan ba shiko maigidan ya tashi da duk abincin ya koma cin naman da bai jin zai gaji da cin wanan naman da kamshin sanadarin girki ke tashi a cikinsa. Da sallama ya shigo tana zaune tana addu,a saman sallaya ta juyo tana amsa mashi sallaman babban rigan sa daya ishe,shi a jikinsa ya debe ya sagalo a hannunsa ya dora saman kujera yana zama. Shafa addu,an tayi ta mike tana fadin sannu da dawowa yaya Habu kai ya dago ya kalleta jin yadda ta kirashi a ranan sabanin yadda ta saba kiransa da dan zaria. Murmushi yayi yasan wanan sunan a bakin su Sare tajishi kallamane da kannesa ke kiranshi dashi dole a wajensu taji wanan sunan. A cikin muryanshi mai natsuwa yake fadin amaryata ya zaman kadaici ina Ramaah ya dan fara dube dube yana neman yarinyar a zatonshi tana daki zaunene. Rigan daya aje ta dauka tana fadin tana wajen su mama tun dazun au ke kadai ta bari nan ke nan ya fada yana kallonta cikin so da kauna tare da godiya ga ubangiji Allah daya nufeshi da samun wanan tsatsiyar yarinyar a matsayin mata a gareshi. Wanka zakayi ko sai kaci abinci muryanta ya katse mashi tunanensa ya dago ya sauke mata kallo yana fadin bari muci abincin sai na shiga gaba daya. Ta juya ta shige ciki ta aje rigan ta fito ta sameshi ya lumshe ido yana godewa Allah indai Yanda tacigaba da hakan a rayuwanta zaifi kowa murna da aure a rayuwanshi. Ga abincin can na jera a dinning ta fada ya kalli daning din ya hango kuloli a jere gwanin ban sha,awa ya lumshe ido yana mikewa tare da kamo hannunta . Idonta tayi saurin lumshewa lokaci guda tana maijin wani iri a zuciyarta basu nufi dining din ba sai ji tayi yakai mata runguma yana sauke ajiyan zuciya da itama shita sauke lokaci guda tana hawaye.
Chapter 25 · 0% Book details