← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 306

Sashe 103

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune suka samu mama Dubu da Saare a kasan kafet din falon suna cin shikafa da miya da aka zuba salad a gefe daya sai goran zobo a gefen kowansu da ruwa na leda. Mama ruwan ya kare ke nan ko kun koma shan na gora kuma Habu ya fada yana zama mama dake kokarin kawar da goran gabansa don ya zauna da kyau tace. To Habu a zauna ba abinyi sai shan ruwa a gora wanan ma ai samunsa gatane wasu na can suna neman irinsa basu samu ba ba kuma lafiya muka fisu dashi ba. Sanabene kawai irin na zamani da wani ruwa iyayyen mu samu kanmu muka sha muka rayuwa cikin sallaman ubangiji kuma. To ai yanayi yana saka ayi taka tsantsan mama Jafar ya fada daga gefe daya sun zauna aka gaisa take fadin saiga Rakiya hankali tashe wai kawunku yai tafiya bataji duriyansa ba ? Ai har nan tazo ashe Habu ya tambaya mama take fadin har nan take ai hankali tashe bataga mijinta ba ni abin na Rakiya har yana ban kunya kuma wallahi ?. Koda yake shiya saba mata ai dole ta damu don daya dawo baya numfasawa sai ya zube mata kaf abinda ya nemo ta lissafe itace mai tsara yadda za a kashe a tsakanin su. Ita har yanzu tana wanan halin natane wai Jafar ya tambaya tome zata fasa haline fa kuma ya daukar mata hakan ai kaga bata da laifi ke nan. Wayan mama din dake saman kujera a gefenta yayi kara ta dauka tana fadin kaga yar halak itace ma ke kirana ashe yanzu kuma . Habu ya dubi dan uwansa yana fadin Isah bai san halina amma zamu hadu wanan karon dashi rainin wayyon da sukeyi a gidan nan yayi yawa sai kace su kadaine yaya baba ? No saka masu ido duk abinda zasuyi suyi gida dai a yanzu kafi karfin tsayawa kana fada a kansa Habu suda suka tsaya jiran gado sai suyi ta zaman cinsa mu dai mun gode Allah munfi karfin hakan a yanzu. Lokacin mama ke fadin ai gasu gabana yanzun nan suka shigo amma basu fada min har can suke ba ai sai kuma tayi shiru tana sauraren bayanin da Rakiya keyi kafinta tace wai wani Jafar kike nufi dai ? Jafar yayi aure haka kowa bai sanda zancen ba jin hakan yasa su zubawa mama din ido lokaci guda suna saurarensu . Don Allah Rakiya ki bar zancen nan mana Jafar fa yai aure har yaushe ya taso daga ciwo da za a kakaba mashi aure a yanzu haba dai don Allah nawa Jafar yake da zai zauna da mata ukku biyun nan ma yaushe ya iya dasu balle yaje karo wani auren kuma ? Saare ta kafe mama da ido don bata fahinci takamaiman zancen mama din ba akwai mamaki ace yayanta J yayi aure haka basu da masaniya a kai. Mama wani masaniya zakiyi a zancen banda ki saka masu Albarka tunda Allah ya nufa dai matarsace daga zuwa nema aka sauwaka muna komai don nisa aka daura auren lokaci guda ai kinga anyi muna halarci a nan. Kai dakata min da wanan zancen banza don Allah ban haifi dana don wasu ba don haka babu wata gaiyan tsiya da za,a sake kwaso min kuma wanan aure bai dauru ba a wajena. Haba mama wani irin zance kikeyi hakane aure kan an riga da an daura yarinya na zamasa a yanzu saidai kiyi hakkuri da fatan alheri a garesu kuma. Habu wai meya hau kankane haka ina fada kana fada zan gani idan kaine ka haifa min jafar din waima wayaje har wanan gari ya auro banda labarin komai ? Shiru sukayi gaba dayansu sun kasa bata amsa don yadda ta birkice a lokaci daya a hankali habu dake mikewa yake fadin you have to be strong for dis issue if not ,,,,, Ai da ka zageni da hausa habu abin zaifi maka sauki da wanan yaren nasaran da kakeyi a yanzu ko bamu son jafar zamu so lafiyanshi ba tashin hankali a kansa ba. Tsam ta mike zata shige daki cikin wani tsaya yayi magana yana fadin ke dawo munafuka kawai ina zaki ana magana zaki daukan rahoto ki samu na yadawa ko ? Ai ka barta ta yada din duk uban da zata kira ta fadawa taje ta kira idan wani ya aura min matar mama ba kowa na aura ba sai Rahama dai da kika sani kanwar marian habu itace na aura zargi ya kare. Anty Nafisa dake shigowa don ta gaidasu taja ta tsaya a cikin mamaki tana bin yan uwan nata da kallo tace yaya J ka auri Rahama ? Tabbas Rahama ce na aura don wanke zargin da aka soma min iya matakin da zan dauka ke nan tunda ance dama farkatace ita dole in mata gatan hakan a idon kowa. Yanzu na gaskanta zancen da ake fadin fillo kakan sheri yau sherin nasu a kaina kuma ya dawo ke nan an fada masu ni na haifa masu diyana donsu ne ? Haba mama bai kamata aji hakan daga bakinki ba ai na dauka wanan abin da nayi albarka zaki saka min kan yadda nayi din ba irin maganganun nan ba ? Rahama dai kowa yasanta yasan halinta balle ta zama bakuwa a cikin mu ni kuma na ganta nace ina so ba wanda ya tilasta min yin hakan. Ni dai naga dacewan hakan da nayi duk da yarinyar bata sona ga hakan asalima daga ita har maria har kawo yanzu basu sanda zancen auren ba. Don bata ban hadin kai yadda naso ba hakama wa yanda take wajensu can basu bani goyon baya akan nufina ba yasa na dauki kawu da Habu da Nasir muka tafi tare dasu aka kumayi mai gaba daya. Kiran wayansa da akayi ya katse masu zancen ya mike yana fadin yana zuwa ya barsu a zaune zugun zugun kafin yasawa Habu kira ya mike shima ya fito daga dakin. Fada mama dubu ta soma tana fadin yau za ayita ta kare ba sai gobe ba wanan ai tada zaune tsayene yaushe aka taba yin hakan kagani. Kanin ka yana auren ya kai kuma kaje ka daura aure da kanwa don shashanci kana babba a garesa ka koma ka auri kanwa kuma ? wanan wani irin komawa bayane wai ? Ba kowa bane maria ce keda kisisinan nan mama tunda tana ganin ta samu waje bari ta cusa yar uwarta itama da hadin bakinta hakan ya faru . A,a Saratu ki kama bakinki wanan zancen manyace bata yara bace kin dai san halin yaya habu yanzune yaji abinda kike fada akan matarshi zai latsa ki wajen nan. Ai sai yazo gata tunda hauka yayi ya kara dukan mi ya kan matarshi wanan karon ba zan raga mashi ba . Mama ta daiyi shiru shine alheri ta kama bakinta tunda ba zancen ta bane gashi kuma sun fada daga maria har Rahaman basu sanda zancen ba ? Dazun nan muka gama waya da Rahama da safe a dakin nan mamakinji metace ai danace hutunsu ya kare tace saita kara lokaci zata dawo . Nafisa rabu da yaudara inda kika gansu sunsan komai maganan saratuce da gamin bakin maria akai hakan don haka ko ita ba zan kyaleta ba gidan nan yanzu. Ya jima a unguwar saidai bai yadda ya kara shiga cikin gidan nasu ba don habu ya fita tun bayan fitowansu ya nufi kaduna. A lokacin ya kira anty Salma yayi mata bayanin komai tare da rokonta zai turo mata kudi ta hado mashi laife. Hakan akayi ina daki kwance duk da ba barci nakeyi balokacin don haka kawai nake jin raina ba dadi aranan. Kafana taja tana fadin lazy tashi ki rakani outing wani ya ban aiki daga maiduguri haka na tashi na shiri muka fito ganin harda Samuel driver da yunusa zamu fita yasa nasan babban abu zamu fitayi kfaruwa lokacin. Bayanin da takewa yunusa yasa na fahinci meke faruwa a takaice dai wani ya sakata hada lefe na gagawa wanan sana,an mamace mahaifiyarsu anty salma. Donshi banyi mamaki ko kawo wani abu kasan zuciyata ba nakance alfahari da neman suna yake sa wasu fita waje don banjinta da daukakansuna. Amma komai da zaka sayo waje akwaishi a nan gida Nageria dan bambanci kudi kuma kadanne a tsakani don muda kan mu muke raina arzikin kasan mu da kan mu amma gaskiya matasan masu kudin Nageria suna iya kokarinsu wajen cigaban kasan nan saidai mu yan kasan ne bamu bada goyon bayan cigabansu. Don munfi ganewa alfahari da bajinta a koda yaushe wanan na kara durkusar damu a cigaban kasa da zamu samu. Tayani zaba Ramaah kada ki damu da kudin kayan ki duba qualities dinsu kawai ki dauka duk abinda yai maki kyau a zuciya. Nasan wanan akidar tasu tun muna kananuwa mama kanzo damu mu tayata zaben kayan da take hadawa din da gyaran wajen event dinsu da suke bada haya. Jin hakan yasa na zage na tayata zaben abinda nake ganin na fita kunya saboda furcinta sosai muka hada kusan akwati ukku da kaya na gani na fada a ko ina a fadin kasan nan a wanan shagon na el,samad kafin mu fito zuwa Sahad. Bamu shigo gida ba sai bayan ish,i akan washe gari za a koma a karasa sayan kayan tunda na shige nayiwa wanka da alwala nayi sallah na kwanta. Bandamu da neman abinci ba a ranan saboda gajiya dana debo har nake dariyan kaina ashe ko wani jiki yana son hutu a duniya ? Dan kwana biyun da nayi ina samun hutu a yanzu dan abu kadan yake wahal dani da gajiya kamar bani bace nake yawan aiyuka a yan watanin baya ba. Zaune suke dukansu a falin iya din da mama ta daga masu hankali saidai shi Jafar bai wajen don ya wuce a ranan ya bar gari zuwa kano zaibi jirgi da zai kaishi lagos . Sai habu da ya tsaya shima yace da safe zaibar gari zai tafi maiduguri mama ta nisa tana fadin na dai gane kuna son mayar dani mutumiyar banza habu ? Na fada maku hakan ba zai yuyu ba dole Jafaru yasan yadda ya walwale auren nan dayaje aka daura masa
Chapter 103 · 0% Book details