Sashe 165
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nagama shiri zan kwanta kiranshi ya shigo min nayi mamakin ganin kiranshi na daga tare da sallama a bakina ya amsa yana fadin baki barci ba ke nan har yanzu ? Na amsa mai da fadin yanzu dai zan kwanta ina wajen iya muna hira yace keda kike da exam gabanki zaki tsaya hira da iya ? Murmushi kawai na iya yi ba tare da furta mai komai ba sai naji yace nima gani nan ina kewarki yau duk sai naji dakin nawa daban kamar ban saba kwana a cikinsa ba. Na miji ke nan wanda keda mata biyu a kusa dashi ya fake da fadin hakan don dadin baki irin na maza don kawai ya faranta min rai nasan ya fadi hakan. Ban karasa mamakinsa ba na sake jin yana fadin kilama zan dawo nan in kwanta abina don kewanki a kusa dani da banji ba duk ya kashe min jikina yau. Ni dai yaya saida safe don Allah kada kasa mai girki tace ko a can kana tare dani manne a waya ina fadan hakan naji yana fadin . Baki yarda da abinda na fadaba ke nan kashe wayan nayi ina jan tsuki na wurgata gefen filo waini yaya ya mayar karamar yarinya ya faki odon matansa yazo yana min dadin baki . Nasan zai kira yaji wayan a kashe kamar yadda na saba tofe dakina da addua haka nayi don tunkan inshigo na rufe ko ina na gidan biba kuma zata kwana da iya don tare suke kwana a dakin dama da ita. Haka na kwana ina juyi washegari na tashi kamar kullum karfe bakwai duk nagama komai har na shirya don tafiya karyawa ne ya rage muyi nida Biba . Ina saka hijab naji muryanshi a falo nayi mamakin hakan sosai yadda ya baro can gidan a wanan lokacin haka ? Ya leko dakin yana waya na dake ina mashi ina kwana ya amsa ya kashe wayan yana fadin meyasa kika kashe min waya jiya Rahama nazo kuma na samu kun rufe gida ? Kazo fa yaya haba dai kadai fada ina zakazo karfe goma fa da yan mintuna lokacin ai Oh kina zaton karyane banzo ba din to ki tambayi maigadi idan kin fita. Banso ina waya da mutum ya kashe min waya hakan yana bata min rai sosai wallahi ba wani gargada nace dashi iam sorry gani nayi zamu shiga hakkin wace ke tare dakai lokacin. Ni hakkina da sukeci fa ya fada yana nufoni sai muryan iya mukaji tana fasin wai Jafarune da safe haka ince dai lafiya ka fito gida wanan lokacin kuma ? Iya nine ya fada yana kutawa ya fita ina jinshi yana fadin nazo nakaisu makarantane kada su makara don da motarsu na tafi can jiya din. Allah sarki nikan nace to lafiya ka fito a yanzu da safe haka to ya kwanan mutanen gidan ya amsa yana zama falon yace lafiya kowa yake sai yaron nan Abba dan wajen Habu shine dai jikinshi ba dadi har yanzu wallahi. Yo ina zaiyi lafiya dama yasha allurai da kwayoyi tun a cikin uwarshi dole sai an zuba mashi ai yayi lafiya ai illan asibitin ke nan dama irin hakan baku ganewa ne dai . Banji dadin jin Abba ba lafiya ba don mijin yar uwata bai gari shi yanzu habu sam baya zama gida ko kadan ko yaushe yana wajen aikinsa ni har takan ban tausayi wani lokaci saidai ita sam bata damu da hakan ba. Naji kamar in tokesa ya kaini idan mun fita saidai kuma zan iya makara idan nace hakan muka karya a gurguje muka fito munawa iya sai mun dawo. Tun a gabana yake fadin zan biya gida in dauko maki salima tazo ta tayaki zama kada a barki ke kadai . Amma sai naji iyan tace ka barta zanyi ibadana idan nagaji kuma sai in dan kwanta kafin su dawo tunda ba har dare suke kaiwa ba a can. Muna gaba zaune biba tana bayan mota zaune yaja motan muka fice a gidan saida muka sauke biba yaja mota banyi aune ba naji hannusa cikin nawa yana tuki da hannu daya kallonsa nayi na dan sauke murmushi naji yace dani. I love you with all my heart yana lumshe idonshi naso ki rubuta exam ina garin nan gashi zan koma next week don kayan mu ya kammalu. Yanzu mutane su fara gane harkan donshine bamu tsayawa bata lokaci da zaran kayan ya kammalu nake mikashi can wajen masaya. Zan barki da iya don zamanta a nan tare daku hankalina yafi kwanciya da hakan nasan babu wani wanda zaiyi ganganci zo maki gida da izgili tunda tana tare dake yanzu duk da nasan mama ba zata yarda da hakan ba amma zan fara zama da iya din inji ra,ayinta. Nasan ba zataki ba ai saidai idan taki kada ka matsa har ayi tashin hankali Allah yana tare damu ai ba abinda zai samemu in sha Allahu. Tafiyan da yakeyi da motan a lokacin ba wani gudu yakeyi ba har muka kai muna zance guda ya saukeni nayi mai godiya yaja mota ya tafi. Kwananshi hudu can gidan tare da iyalinshi inda nayi kokarin danne zuciyana ban yarda na nuna hakan ya dameni ba a fili amma kasan raina akwai kishin hakan sosai da nake ji. Don idan yazo yana dan kame kameshi sai na dinga jin haushin hakan bayan ya gama masu abinda kilama yafi wanda yake min nan zai dawo yana nuna min irin damuwan da yakeyi dani din. Ranan da zai dawo gidana duk shawaran da anty salma taban shinayi na kuma ga farin cikin hakan a tare dashi sosai don ga iya a falon amma duk inda nabi idonsa yana kaina tunda yazo kuma bai fita zuwa can gidan ba kamar yadda yakan muna zai dawo yakai goma ya koma gida sai kuma da safe idan ya dawo. Niko nasan nayi shiri din don ni aka bari da tsamin jiki a karshe inda Allah ya taimakeni ranan ba school donshi na dan kai wani lokaci kwance ban fito ba sai takwas da rabi. Inda nafito na samu Biba har ta dafa ruwan zafi tana fere dankali donshi a rayuwanshi nafahinci yafi son dankali irish da safe wanan yasa nake kokarin soyawa wajen karyawan mu. Nakan sarrafa masashi nau,i nau,i wani lokaci haka kuma duk yadda na sarrafa din zai zauna yacishi sosai da safen . Faten dankalin da kayan cikin da nasa biba ta yanka kanana nayi muna inda na dan sakewa dankali ruwa sai kuma muka hada ferfesu kai shanu da ya kwana saman wuta a hade. Sai ruwan shayi mai kauri da yaji kayan kamshi wanda mukeyi a gidan maman Abuja mun kammala na jera a dinning din don ko iya ban dibar mata nata daban ba a ranan saboda ina son mu zauna a karya gaba daya yau a gidan. Wanka na shiga na tsala kwaliya a cikin atamfa da akai min dinkin buje da riga kayan yayi matukar karban jikina sosai dan takalma flat na zaman gida na fito dashi zuwa dakinsa. Barcinsa na samu yanayi hankali kwance na kai zaune a gefenshi yadda zaiji motsina a lokacin. Hakanne ya faru don ko second banyi da zama ba naga ya dan bude idonsa dake cikin nauyin barci yana kallona murmshi na sakar mashi ina fadin barcin ya isa haka yayan mu ka tashi ka watsa ruwa iya tana jiran ka mu karya don tare zamu karya yau da ita. Ido naga ya lumshe yana jawoni zuwa jikinsa na dan fada ya sauke nufashi yana fadin bason haka ba sai ince ki bari in biyaki kudin wanan kwaliyan naki don Allah ? Ba saika biya ba tunda ka yaba ka tashi dai a karya kada iya taga nawana wajen bata abin karyawa yau ta dauka ban damu da ita bane. Yau ba school ke nan nace ehh ina mikewa ban faye shiga ba irin yau don lecture gudane gareni malamin ma kuma ance baya gari yayi tafiya. Ok ya fada yana miko min hannayesa biyu da alaman wai in dagashi daga kwancen banki ba na mika mashi hannayena din ya mike zaune bandaki ya shiga na mike na wce wajen iya. Tana zaune tana dan hira da biba nashigo ina gaida ita da kwana na samu biba tayi wanka tana shafa mai nace kiyi ki shirya ga uncle nan zai fito muje falo mu karya a can yau. Bidiri yau da mai gidan za a karya ke nan nayi murmushi nace iya ai hakan sunnane a musulunci zama tare da iyali a danji korafin kowa hakan yana kuma kawo shakuwa a tsakani akace . Don sammakon da mukeyine muna fita yasa ba a samun yin hakan wani lokaci don yadda muke karyawa a gurguje kadin mu fita. Dolene miji ya kulaka ai yar nan duk sauri da abinda ke gabanki baki gaza bashi kulawanki haka nima nan da yar nan me zai hana mace ta sace zuciyat mijinta tana hakan. Abinda suka gaza ganewa ke nan ba asiri bane ke sa miji karkata sai tsaban kulawan mace wata mace bata dogara ga asiri ko wani siri ba akan miji sai zalla tsaban kyautatawa da take masa yake sa miji ya ahagala a kanta haka . Dan zaman na fahinci komai game da zamantakewan ku gidan nan akwai banbanci sosai a gidan nan da can gidanmu . Wa zai zauna ya baka kulawansa irin hakan da kikeyi mace tasan muhinmancin da darajan namiji haka ace miji ba zai bata kulawansa ba wanan ai karyane. Barsu can su zauna suna kishin hauka da bai fishesu ga abinda ya dace suyi amma haka zasu barshi har sha daya wani lokacin wai ba a gama abin karyawa ba. Toke iya waya tambayeki muryan Biba ya katse mata maganan ta mika mata dakuwa da hannu daga inda take zaune tana fadin ungo naki nan yan nema idan zaki mai da hankali ki koya a wajen yarinyar nan gara ki koya ki tashi da wanan halin duk da naga kina da kwazon kima kinayin komai yadda ya dace. Ni dai ina gefe zaune bakin gado ina murmushi nace iya kinsan taji kina zancen iyayyenta shine ranta ya baci. Kai anty ni da nake shan harara wajen