Sashe 161
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Barci nasamu nayi sosai washegari don babu kowa gidan har biba a can ta kwana wajen su anty Salima dagani sai shine a gidan shi kuma ya fita tunda safe . Ina kyautata zaton yan uwan saiba ce zasu koma gida a washegarin suna din don haka na samu nayi barcin gajiya mai isata da yake ina fashin sallah donshi na samu har karfe hudu ina kwance saidai fitsari ya tayar dani kawai. Karfe hudu na samu na mike na shiga wanka na fito na shirya na fada kitchen don girka muna abinci ina gab da kammalawane naji tsayawan motanshi alaman ya dawo ke nan lokacin. Ko ina na gidan fes yake sai kamshi ke tashi ga kuma na girki dayake dan shigowa ciki lokacin muryanshi naji yana shigowa a zatona na dauka waya yakeyi ashe shida iyace da habiba suka shigo. Ina tsaye daga kofan kitchen da niyar gaidashi da dawowa sai ganin iya a bayanshi nayi habiba na biye da ita da dan jakar kayanta . Cikin murna na hada ina masu sannu da zuwa na dauka ganin idon iya din zai hanashi yadda yake min idan ya dawo saidai hakan bai hanashi ba don saida yazo ya rugumeni yana fadin how are you ? Fine na fada ina dan nokewa ya gane me nake nokemawa din don iyace sai naji yace wai iya ai zataji dadin ganin yadda kike ban kulawa don itama hakan take son na kasance. Ni dai na wuceshi ina murmushi zuwa wajen iya din ina kara mata sannu da zuwa na nuna mata kujera ta zauna a sama tana fadin masha Allah abu yayi kyau sosai wallahi haka ake so a rayuwa dama cigaba aiba wanda yakishi. Zonan mu gaisa da kyau tana nuna min gefen da take zaune na zauna kamar yadda ta bukata din ina fadin iya yaya gida ya taro kuma ? Taro Alhamdullahi ke dai anyi lafiya an kuma watse lafiya sai abinda ba a rasa ba dai wanan kuma ai an saba dashi kuma ko ? Habibace ke gaidani na juya ina fadin biba yan suna nayi ta zuba ido jiya inga dawowanki shiru ta danyi murmushi tana fadin ban samu wanda zai dawo dani bane har dare yayi na kwanta a can. To bagashi yau kin dawo ba bata da sabo kin ganta nan taki sakin jiki da kowa amma yanzu kinga tana zuba kamar ruwan sama. Mukai dariya na mike kayan da Biba ta aje gefe na dauka zuwa dakin da iya zata zauna wanda a nan Biba take gyara dakin nayi sosai tare da Biba din na shimfida sabin zanin gado dana dauko daga dakina na wanke bayin tas duk da dama baida datti sosai amma na kara gyarawa nasa kamshi. Falo na dawo na sameshi tare da iya yake fadin ina kika shigane haka nace ina gyarawa iya dakine sai naji tace kaji arziki ba a inda aka santa Allah dai yayi maki albarka kinji. Kitchen nakoma na kwashe abinci na hada miya ina tsaye biba ta shigo ta sameni zata kama nace jeki huta aina kammala tun dazun kafin ku iso. Ke kuma ai da gajiya a jikin ki tace banyi komai ba a can wai anty ai gara da bakije ba wallahi ana ta fada dasu anty salima da matan uncle wai ta aiko a dibi abinci mummy salima ta hana shine tashigo tana ta zaginsu harda ke da bakije ba din. Maman tudun wada kuma ta farwa mummy salima din da fada har ta kira uncle shima tace wai an kawo abincin mai kyau gidanki andafa ba akai can ba gashi kuma yanzu abincin ya hada fada. Ikon Allah nafada cikin mama sai tace ai uncle yace duk abinda ya sawo nan gidan shiya saya a can kuma na can din yafi yawa tace dai ya dinga adalci. Bayan haka kuma aka zauna da yan uwanta akaita fada da uncle din tana ta kuka shine mama tudun wada tace wai in tashi in fita na koma part dinsu Abba na zauna. Biba irin hakan dama dole zaki gani tunda kina tare dani ko kingani kibar damuwa saivyarinyar tace Allah mama tudun wanda bata sonkine anty haka shima uncle ya fada yace me kikai masu meye matsalansu dake ne wai ? Muryanshi naji yana kirana nazo yake fadin to bakuwanki zaki kai daki zatayi alwala na amsa da to iya muje dakin kiyi ko ? Tafiyan nata daine yasa dole nima na taka a hankali muka shiga har dakin sai fadi take masha Allah kinga arziki dole ai yarinyar nan tayi hauka sunzo jiya da yan uwanta sai koke koke suke muna wai Jafaru ya fita batunta ya maida ita bora a gida. Uwarku kuma kamar sun gama da ita sai wani noke noke takeyi makin ta fada masu gaskiya ta tsaya marawa karya gindi ita da yar nan saratu mara hankali. Duk abinda dubu keyi da zugin saratu takeyinsa ni yaushe zan zauna yaro karami yana min wanan shegantaka in dauka yarinyar dako auren fari batayi ba. Kinga ki daure kibi mijinki yadda yake yabon nan naki karki yarda ki canza halinki ko gaba haka nake fadawa yar uwarki wanan zancen don yadda suke hattaranta a yanzu gidan. Dan dama wanan Asmau din naga kamar ta fita wanan shirmen nasu tunda tasan Allah dayane taba da kai bori ya hau har abin suna naga ta hado akawo maki amma uwarku ta rabewa mutane duka. Naman daine na suna nayiwa Jafar magana tasa a debo maku har muka fito bata bayar ba nace iya nagode ba komai wallahi Allah dai yabashi lafiya tace amin kafin kuma tace dani. Wai har yanzu dai jikin nasane kome ni naga yana rama a tsaye nake tambayanshi yace min damuwane kawai da abubuwa da sukai mai yawa kuma. Haka yake fada iya idan anyi magana baidai fada maki gaskiya bane amma da abinda ke damunsa gaskiya sai kin zauna dashi kila zai sanar dake damuwansa din . Jam jam Allah kaza gata a garemu shiko abu na cinsa bai fada tun abu bai baci ba ni yaron nan tausayi yake ban don da kurciyarsa nauyi ya hau kansa haka ? Na dai nuna mata ban daki ta shiga tana mita na fito na samu biba ta kammala komai a kitchen din dakina nanufa na zauna ina azzakar na yamma. Ban fito ba saida akai isha,i na fito na dauki abincin nakaiwa iya din har ruwan sha dana wanke hannu duk na aje mata a nan inda take sallah din. Na koma gefe muka zauna da biba muna hira ta gama addu,a ta shafa ta juyo tana fadin shi dai mutunci gadarsa akeyi haka yar uwarki take faman dawainiya dani kullum gashi na fito ban samu sallama da ita ba. Ayya bari na kira maki ita kuyi sallama din tace hakan shiyafi kada taga rashin hankalina nasan yanzu ta shigo bata sameni ba. Itama uwar naku naji tana fadin gobe zata gida ai saigashi Jafar yazo yace dani ai in shirya muzo nan in kwana biyu daku in huta hakan yai min dadi sosai wallahi. Kwana biyu kuma iya nida nasha kinzo ke nan baki komawa a nan zamu zauna dake tace haba ina haka zai yuyu ai sai a zageni nazo nan na tare don kwadayi kamar yadda ake zagin yar nan salima tunda na saratun nan ba mai ido a tsakar kai. Na fadawa dubu ai tayi mata aure ta huta da ita yafi zaman ta sai gulma tsakanin yayyun ta da hadin hasumi da takeyi a gida. Aure lokacine iya idan yazo koba shiri sai anyi nata harda ruwan ido kinji aiba maneman ne ta rasa ba ruwan idone kawai ta dafewa yaron nan da akace baida kirki sai karya yake masi ko yaushe gashi turo magabatanshi ayi zancen aure. Ina ji masu tsoron irin na barakha ta fada hannun baragurbi azo ana dana sani daga baya ido ya raina fata shine ya dawo yasa namike zan fito sai gashi ya shigo yana fadin kina nan ashe ? Na amsa da ehh yake miko min goran ruwan dake cike da ruwa nabi goran da kallo kafin na karba don ruwan ciki bai min kama da ruwan goran ba. Ganin na karba da mamaki yake dan wuceni yace ruwan da akace a samo na hadin maganine ai nace au ruwan doki ko ? Ya amsa shine Auwal ya samo min a gidan makwabcin su yanzu ya kawo minshi daga inda iya ke zaune take fadin ruwan doki kuma ? Yace iya banjin dadin jikin nan nawa wallahi shine wani yace mu samo ruwan a hada magani dashi ina jin kamar wancan ciwon yake son ya dawo min kuma a yanzu. Muna ga rasulu ni yar mutum biyu kaga abinda nake fadawa uwarku ko amma ta kasa fahintana sai shirme ta tsaya yi ita da wanan shashan dan uwan nata. Wai yanzu ace kamar dauda zai kara aure don jaraba mace tazo ma da goyo har da yayyu a gida ka wani haukace kana sabari kamar karamin yaro ? Jiya nan hafsatun take ai tana muna kuka wai dauda ya juya mata baya kan ya kara mata da yaya ko yaushe yana rugume da dan da akazo mai agolanci dashi. Har yana batun sabawa Hafsatun da yaranta kaji min abin kunya waya saura wanan auren kazantan yanzu banda shi mara hankali ? Ba rashin hankali bane iya abinda yake ra,ayine kinsan mu maza idan muka hangi abinda muke so sai aga rashin hankalin mu kan abin da zuciyarmu ya zaba. Kaiya ba irin haka bane wanan yarunyar daya kwaso yar duniyace kaji banda duniyanci da samun waje zakizo aure da yaya ukku ? Sai kace wani attajiri dashi a zamanin nan da kowa keta kansa ina dai dan dukiyan nan daya kwamsa na uwarku da yan uwakane ya ke rudansa har yake ganin shiya isa a yanzu baijin has ? Kawu aiya canza gaba daya iya ni har abin nasa yana ban mamaki wallahi zai baka kuwa kaida kasan kanka amma dama ai haka dauda yake kune baku ganesa ba dai sai yanzu. Kaga matar nan nasa hansatu to makiran matace tun aurensu gaba daya lamarinsa ya canza bari naga abu zama da wanan yarinyar. Don