Sashe 52
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idan suna gida bamu da hutu sai sun bar garin zamu dan dafa abu mai sauki da zamu bude baki dashi a irin hakan na fahinci abubuwa da dama a rayuwa. Na farko komai arzikin ka a waje idan akwai wanda ya daraka naka sai ya zamo babu mai ganinsa saidai wa yanda suka zama dolen ka su gane maka hakan. Don yanzu da mai lokaci ake zamani harda wasu uwayen suna nuna irin wanan bambanci a cikjn iyalansu da suka duka suka haifa. Zakiga uwa kamar tana shakkar danta don kawai yana da hali shike daukan dawainiyar ahalinsu sai a koma jin tsoronsa shiya zama kamar bakece kika haifishi ba. Da yawa a yanzu ana samun hakan ga iyayye saidai akwai jijirtattun iyayye da har gobe suna a maysayinsu na iyayye din komai mutum ya zama kuwa. Zaki suma sauran diya suna nasu kokarin amma ba a ganin hakan da sukeyi hankali sai ya koma a waje daya anfi ba bangaren dake da maiko muhinmancin. Saidai gaskiya a nan din ina kallon abin kamar da dama sosai don dukka yaran nata biyu tana basu kulawa irin yadda ya dace uwata gari tayi din. Don ko shima ya Habu yana tsaye da dawainiya dasu sosai duk da kamar karfinsa baikai na jafar ba da akewa kallon maikudi a cikin dangi . Dan kowa ya tashi dai jafaru dai jafaru dai nazo a roka min jafaru abu kaza da yawa haka suke zuwa a cikin dangi wajen mahaifiyar nasa tunda Jafar din baida tsayayyar matar da yan uwa zasu buga gaba da ita. Zakiga abin mamaki a babban gida da abin haushi har dana takaici shi jafar dai ya kasance mutum mai ujula yanzune zaizo kuna magana sai kuma wani uzuri ya kamashi ya barka wajen. Ya Habu kuma akwai tsare gida gashi shiru shiru bai faye magana ba amma akwai tsayawa ya fadi gaskiya don hakane ma kowa yake shakunsa a gidan haka kuma na kula Mama Dubu tafi ba Habu din lokacin ta da daukan sha,aninsa da muhinmanci. Rayuwa tana ta tafiya a hakan dai inda azumin wanan shekaran ke muna bankwana akwai dadi kuma akwai wahala wajen aikin abin buda baki ga mata. Sallah saura sati daya suna zaine ranan dai duk iyalan mama dubu suna zaune a falo misalin karfe hudu bayan sunyi sallah azahar ina kitchen ina ta hada abin buda baki don yanzu ban tsayawa jira tunda jiran baida amfani karshe a kaina aikin yake karewa kowa dayasha ruwa zai nemi waje ya labe. Ka zamo mai zafin nama wani lokacin akan kwari mutum ga hakan kowa saiya sakama ido don amsan zaka iya din . Saida hakan bai damuna don da zuciya daya nake hakan, suma kuma sun sani, haka kuma wanan aikin yafi min aikin gidan baffan mu sauki sau dubu. Gidan baffa karfe hudu dole mu tashi mu fara surfe idan mun gama gari ya fara haske mu dauki jarkan diban ruwa muna gamawa da mun dawo zamu cika jallon mu da dan gudun kokon da zamusha wurin kiwo mu zamu daka amma kuma a hana muna. Shiyasa nake kallon wanan nagatane tunda ni zan dibarwa kaina iya cina don haka ai wanan ya zamo gata kuma ga hutun da nake samu nayi na tsawon lokacin. Rabon kayan sallah Jafar din da Abubakar sukeyi sai mama da iya da kannensu mata dake ta rubutu a takarda suna mannawa su kuma matan shi suma suna nade kayan. Mama nifa har yau banji ance ga kayan sallah Ramaah ba salimace ke fadin hakan wa mahaifiyarsu ta kureta da idanu ? Kamar ya ba,ace Ramaah ba ba yaya Habu zai mata ba ita da matarshi Saare ta riga uwar bada amsa . Habu kuma Saare don tana kanwar matar Habu za,ace shi jafar ba zai mata sutura ba kome ? Cak suka tsaya ga abinda sukeyi gaba dayansu suna kallon mama din da saratu au kece zaki tsara yadda abin zai kasance ashe ? Wai akan wa ake magana Jafar ya tambaya da sauri salima tace Rahama ranan full name dina ta fada kai tsaye. Ramaah ya juyo ya dan kalli dan uwan nasa yana fadin Rahaam bata da kayan sallah dama kuma baki fada min ba salima ?. Yaya na dauka ka sani ai shiyasa ban fada ba da wuri naga kowa kuma baiyi magana a kanta a yanzu ba yasa nayi magananta ai. Wai wa kuke zancene bai samu kayan sallah ba cikin mutuwam jiki da jin nauyi mama din tace wanan yarinyar wallahi . Ni abin gidan nan yana ban mamaki ta ya yarinyar dake dawainiya daku haka zaku dinga cewa kun manta da ita don Allah zama baice haka ba wallahi. Iya ta fadi hakan cikin hasala tana juyawa kafin mama din tace a,a Iya munyi da Jafar tun a waye yace kayan sallah nace na yaran nan su uku zai sayowa kinji yadda mukayi na dauka harda nata aka hado ai ? Wai dai wace yarinya ke Asmau dana kawo kaya mena fada maku da aka fitar dasu ? Nikan kace nasu Saare ko kace mu zaba mu basu saura kuma muka zabi namu muka basu nasu ta karasa a sanyayye tana dukar da kai. Toke salima waya baki kayan ki ta amsa da fadin Saarece tashigo min dasu takai dakin mu ko wani bibiyu ta zaba ta ban nawa shike nan. A,a ni ban gane ba Saratu ina na wanan yarinyar ya shiga don Allah J is enough idon kayane a barshi kawai ke salima kuje a sama mata kaya gobe shike nan . Ya zakace dani shike nan wancan karon ma haka sukayi aka raba abu a gidan nan suka hana mata har mama taga laifina gashi kuma again ankara yi don haka ina son ina kayan nan suka shiga ? Suna tsakanin makiran matarka mana ai kaji sunyi shiru ga baki dayan su sunsan yadda sukayi da kayan ke nan a tsakaninsu tunda suna bakin ciki da zaman boyar Allah nan gidan nan. Itako bata ko san sunayi ba don basu gabanta sun dauki kiyayyan duniya da kyashi sun dora akan matar kani banda tsiya harda kanwata zaku saka a kishi. Ita kanta matar Habu bata san kunayin haukan ku ba hakama yar uwar nata gashi dukkan mu nan gidan muna moran wanan yarinyar. Ko wanan aikin da take ga sharan nan ga girki yaci ace yarinyar nan ko albshi ake mata tayi kissa amma ina tunda suna da wankakken zuciya ba hakan a gareta duk iyace take fadin hakan garesu. No ba zancen da za ace a kyale bane wanan duk da ba zama nake a garin nan ba nasan irin kokarin da yarinyar nan takeyi gidan nan kullum. Ko a fito min da kayan ta inda suka shiga ko kowan ku ya kawo nasa nan yanzu ku har saratu din ban cireta ba ? Dama ai tunda koma meye da ita aka hada baki aka kulla hakan tasan komai tunda hanyar data zaba ke nan bakiji kunyan hakan da kukayi ba don Allah ? Ina yarinyar nan kamar yadda Iya ta fada duk gidan nan kowa yana cin moriyanta a yanzu ku duba zuwansu yadda yanzu gidan nan ya koma fes dashi don Allah ? To mama akan me zai sayo muna kaya iri daya da ita idan su Saare yan uwansane ita kuma meye nasa don kawai tana kanwar matan Habu ? A zabure ya tasowa Saiba din dake magana a lokacin, tayi saurin fita don ganin an taresa daga zuwa gareta ta fita tana maganganu masu zafi game dani. Hawaye naji sun zubo min don a yanzu kan ba fahinci zancen da sukeyi a kaina sai hukuncin ya Habu ya burgeni da yace to ai gaskiya ta fada kada kuga laifinta don Allah. Nine ya kamata in dauki nauyin matana dana yar uwarta dake zama da ita gidan nan ba J ba kowa yasan albatkacina sukazo gidan nan . Kai Habu ka bari a fanci inda zancen nan ya dosa dan uwan ya taresa da fadin hakan inda yaci gaba da fadin kowa dake wanan gidan har gidan kawu nauyin irin hakan akaina ya rataya don hadin kan mu da kowa namu don me zasu so zarta hukuncin dabani na tsarashi ba . Yau yarinyar nan kamar kowa take a wajena tunda zamaka takeyi zaman mu kuma a cikin gidan nan to ai yaya komai za a raba saidai na raba nawa biyun in bata haka akeyi kulum a gidan nan salima ta sake fada. Ke ina aka kai kayan yarinyar nan ya kallo Asmau yana tambayanta suna wajen mu ta fada kai tsaye ki daukosu yanzun nan ya fada. Kayan nan fa basu gidan nan nake gani Saare ta kara fada a bangareta sai iya dake kallon mamaki take tambayan . Nikan me yarinyar nan ta rageku dashine a gidan nan wai ? Bakin ciki mana Iya amma in aikin karfine kowansu ya iya zuwa nan yace don Allah Rahama kizo ki taimaka min da kaza amma ba a sonta da karuwa . To wallahi kuji ni ban raba kan yayana ba a gidan nan ba macen da zata shigo tace zata raba min kan gida haka yanzu wanan abin dame yayi kamane wai ? Rikici sosai sukayi a kan kayan ni kan ban kulasu ba na gama miya na dora shinkafa na shige dakin mu na kwanta don fada sosai ya J yayi ya kuma rantse idan basu fito dashi ba duk kansu ukkun zasuji mamakin shi wallahi. Bansan ya akayi ba sai ga kayan an fito dasu da yamma an kawo min mamace ta kirani ta ban na karba nayi godiya saidai a kasan zuciyana na nasa cewa ko zan tafi tsirara ba zan saka kayan ba don nima ta fulanin sun hau a lokacin. Duk da karfi bai kai ba amma zuciyan gado yana nan a jinina aiki kuma idan ba na cikin part din mu bane na dainashi daga wanan ranan . Har washegarin da aka ban kayan raina ba dadi da safe na gama shiryawa nace da salima zanje da kaina asibiti in duba yar uwata dama haka nake bayan kwana bibiyu nake zuwa yanzu tunda aka soma azumi din nan. Sam ban fadawa yar uwata komai