← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 306

Sashe 138

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saiba kuma ya habu ya fada don ganin Saiba again tana kiran dan uwan nasa a lokacin ya fadi hakan yana mikawa yayan nasa wayan. Ya karba yana mannawa akunnesa yace hello Nusaiba wallahi J sai Allah ya isar muna mucuci kawai azzalumi don yarinyar nan kake kokarin nuna mu ba komai bane a yanzu wajenka ? Yau har yakai a na fada muna cewa wai mu din kayi doping din mu ka koma wajen wace ake ganin tafi mu wallahi kai azzalumine J sai ,,,,, Dakata Nusaiba wanan wani irin zancen banzane kika kirani kina min mara amfani ina kan hanyar tafiya neman kudina ko wani yace daku da Rahama nazo tafiyan nan ? Aiko da itace ba a mussun hakan don zaka iya yin hakan a yanzu tunda ka iya ware ta daga cikin mu ka nunawa duniya tafimu wallahi ka dawo ansan wace za ayi don ni ba zan yarda da hakan ba kaji na fada maka. Ok ai ba sai na dawo ba Nusaiba ko yanzu kije gidan ku ba matsala na sake ki wuf Habu ya karbe wayan daga hannunsa yana haba dai J zaka biyewa haukanta ku zama daya ? Duniya ta zageka a kuma zagi Rahama a banza da bataji ba bata gani ba irin wanan abubuwan naji maka tunda ka kawo zancen auren Rahama a wajena . Nasan dama sai kun kwasa da Saiban sosai akan haka don haka don Allah ka kara hakkuri ka daure ka fita zancen ta kawai kaba banza ajiyan ta don Allah . A zaria ihun da Nusaiba tayine ya tayar da Asmau dake barci a falo ga yara sunyi kaca kaca da falon nasu da shinkafan da sukaci sub watsar ko ina sun zubar da ruwa samab center carpet din duk kiriniyarsu a lokacin baisa ta tashi daga barcin da takeyi ba sai ihun da saiba tayine ya tayar da ita agigice. Lafiya take fada tun kan takai dakin Saiban tayi dirsha kasa tana salati tana shiga take fadin lafiya maman ikiram ? Ita inda ranta yakai shine mijinsu wani abu ya sameshi tunda shine ke hanya a lokacin don haka tasa shi wani abin ya sama dai. Yaya J ne ko me ta kara fada tana matsawa kusa da ita a hasale ta dago ta kalleta tana fadin don Allah ni kin cikani da tambaya shine din. Burin ku ya cika yau tunda ya furta min saki amma ku sani wallahi yadda na rabu da J kowanku sai ta rabu dashi rabuwa na har abada gidan nan. Ba daini akaiwa haka ba to wallahi ki rubuta ki aje na fada maki har bafilatan nan da yar uwarta saina fitar da ita gidan nan dukkan ku . Wai me kike fada hakane don Allah meke faruwane sai wani magana kikeyi kamar wace ta samu laluran kwakwalwa ? Ehh hauka nayi ki fita kawai ki ban waje don Allah Asmau banson gulma tunda kinji meya faru dani ko ? Fita tayi daga dakin kamar yadda tace saidai bata zauna ba part din iya ta nufa ta samu Saare take fadin kijefa ina ganin mutumiyarki ba lafiya tsakaninsu da yayanki Ita da yaya kuma shida bai gari koya dawone tace ina ganin kiransa tayi da cin mutunci dai amma ki daije kiji ko meye ta mike da sauri ta fita daga falon iya din. Asmau takai zaune wajen iya tana fadin Nusaiba bata ji saida na bata magana nace tabar zancen nan taki nasan ta kirashi a wayane sukai cin mutunci ya saketa. Shine wai gaba dayan mu har mariya sai mu bar gidan nan yadda aka saketa daga kawai naje ina bata magana ta dinga fadan hakan akaina. Nasan za akai ga hakan don yarinyar nan bata da kirki ko kadan badai kan dan zancen nan da Salima tayi bane ta hakeshi ta kirashi da cin mutunci. Shine kuwa nasan ma shine iya saiga mata ta fito daga daki take tambayan meke faruwa kuma nan suke mayar da abinda ya faru ta mike tana fadin saki kuma ? Sakifa shi jafar ina ya koyo sakin mace daga dan magana ko da gaske kansa ya burgene ban sani ba kan yarinyar nan ? Wani irin zancene haka ga dan cikin ki dubu hau kika gansa dashi ko me da zaki fadi hakan kan danki dubu akan wanan yarinyar da batayi maki ragowa har kike kokarin aibanta danki ? To iya saki fa shi haka yaga mahaifinsa yayi daga zancen fatan baki zai furta wa yarinyar nan saki dama bai shiryawa fitinan mata ba ya tarasu haka gidansa ? Ki dai gyara kalamin ki ina horon ki da hakan matsalansuce can kinsan irin cin mutunci da tayi masa har aka kaiga hakan ? Saiga Saare ta dawo tana fadin wallahi kuwa wai sakinta yayi ta cikin waya daga magana kawai ya furta wai ya saketa. Gata can zata wuce kaduna yanzu dole mama ta mike zuwa part din ta bata hakkuri akan ta zauna sai kukan da takeyi . Bayan mama ta fitone yarta ta bugo waya take fadin wai ta dawo gida zaman me zatayi tunda yace ya saketa din me zata zauna yi kuma ta dawo gida kawai. Wanan yasa ta fita ba tare da sanin kowa ba tabar gidan zuwa kaduna din itako mama tana ta neman layinsa bata samu ba saina habu ta samu yake fada mata ya sauke j din har sun tafi. Shima gashi ya kusa isowa gida in sha Allahu sai batayi mai magana komai ba ta bari sai ya iso gida din taji meya faru. Koda ya iso ko part dinshi bai shiga ba ta tareshi da zancen cikin mamaki yake fadin saki kuma ita saiba tace sakinta yayi bayan agabana sukai maganan . Zaginsa takeyi tana ja mashi Allah ya isa shi kuma yace taje gidansu ta huta iya abinda na sani ke nan ya faru tsakaninsu. Kunj ko mena fada maku ba yarinyar kirki bace shikan ya juya zuwa part dinsu ya batsu nan ana zancen saiba din a part dinshine Maria ke fada mai abinda ta fada game damu din yace hauka takeyi kila ? Zamfara garin gusau. Kiri,kiri baraka ta hawa Aliyu kudin nan tace ya bari mahaifinsu ya fara juya idan sun kara yawa sai a samu abinda aka bashi shima ya soma nasa sana,an. Tun daga lokacin bai kara magana ba kuma yakawo ido yasa abinda bata sani ba shine shi Aliyu yasan mai mahaifin nasu ke aikatawa don wata bazarawace a nan makwabtansu daya taba nema taci mashi kudi ta koma zurmi tayi aure itace ta fito yanzu kuma bai daddara ba ya koma nemanta gadan gadan . Shine Aliyun yaso su zauna da uwar nasa ya hanata bashi kudin amma taki saurarenshi lokacin take ganin kudin yaron ke son ta mika mashi duka. Shiko Aliyun yadda yaso shine su samu dan fili su saye da rabin kudin rabi kuma ansan yadda za ayi amma batab basira ya kamata ta dauki kudin duka ta mikawa mijin nata da sunan zai fara sana,an hatsi dasu yana shiga kauyuka yana soyowa ya kawo nan cikon zamfara din tayi na,am da hakan. Balle dataga haikam ya bazama kasuwa sai dadi ya kara kashe mata zuciya gashi in zai dawo da dan cafanen su na kauye daga ita har yaran sun canza sosai a yanzu gaskiya. Zamana da anty Salima da habiba ba laifi gaskiya saidai matsalan daya shine banda saurin sakewa sosai har yanzu dai halin nan nawa yana nan a yadda takan fada ita saliman . Idan naje school na dawo ina daki ina hutawa sai dare zan dan fito mu zauna a ci abinci a danyi hira kuma in koma dakin karatu. Wanan yasa take ganin wai banda saki a bakinta nake jin abinda ya faru wai saiba tana gidansu yaya ya saketa. Gabana ya fadi sosai da jin wanan labarin don na tabbatar za ace saboda nice hakan ya faru tsakaninsu niko harga Allah ban sani ba. Nasan dai kafin yayi tafiyanshi yana lagos lokacin zai kirani mu gaisa wani lokacin ma shike tashina daga barci da asuba ko kuma ya kira da safe yana tambayan ko nafita zuwa school ? Amma tunda yabar kasan sai gaisawa yayi wuya a tsakanin mu dashi matsala dayace ban yarda na nuna masu hakan ba don salima tana yawan tambayana shi nace yana lafiya ai. Ranan wreekend ban fita ba ranan ina daki kwance ina barci anty Nafisa tashigo muryansune suna hira falo yasa nafito don mu gaisa da ita. Tunda na fito ta kyala ido ta kalleni take fadin wai wai wai Rahama kece haka wai lalai aure Rahamane sunan naki yabi zancen kinga yadda kika koma wata buleliya dake haka ? Cikon dan kunya nakai zaune ina fadin anty Nafisa sheri zakiyi min kuma bamu haka dake fa tace wallahi Rahama kin canza min lokaci guda ? Anty Salima na nuna ina fadin gata nan itace ke ban dadi na koma hakan ai muka dara gaba dayan mu nakai zaune ina fadin wai anty Nafisa daga barin je in dawo ranan kikai tafiyan ki ? To ai gani na dawo Rahama fitan ne yanzu ban faye sonshi ba mutane sun faye gulma yanzu tin anayi a bayanka har an fara fadama zance kamar mutun shine zai nemo miji da kansa ? Allah shiyasa banson fita ko ina aiko gidan iya ni tun bukin ki ban kara taka gidan nan ba har yau nocking din kofan da akeyi ya katse mata zancen. Habiba ta mike ta fita don ganin waye sai gata ta juyo tana fadin matar Uncle ce da wasu kafin ma ta gama zancen sun fado dakin cikin gadara da wani irin kallo. Duk da gabana ya fadi don ganinsu a lokacin saidai ban nuna hakan a fili ba naji wata daga cikinsu tana fadin a,a lalai kan Abuja ? Tunda na mike ban tsaya mu gaisa ba kitchen na nufa na dauko ruwa da abinsha na kawo masu tare da cups na aje a gabansu naji dayan tace to aimu ba ruwa mukazo sha ba. Haba dai kusha ruwa mana na sake fada cikin danjin nauyisu sai naji saiban tace ainan ba gidan da zamu tsaya bakunta bane balle a kama bamu baki
Chapter 138 · 0% Book details