Sashe 199
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
nan asibiti har wasu kwararun likito suka consultants aka dauko don shi suyi duba iya abinda zasu duba a kansa din magana dayace sun kasa gane ainihin abinda ke damunsa din. Exam din dana soma yasa sam banda lokaci ga yaya habu dasu mama sunyi min fada cewa na maida hankalina wajen exam din tunda akwai mutane a tare dashi. Amma matsala daya shine tunda ya fara dan budan idonsa din nan a ni kadai ake gane wani abin da yake bukata wani lokacin ko ban kusa zasu kirani in zo in duba masu shi din. A cikin hakan har exam dina yayi nisa sosai ga jinya ga kuma karatu wata rana ina zuwa mama ke sheda min cewa tana ganin za a bar asibitin nan don tayi masu bayanin cewa su gwada dagashi daga asibitin a gani kuma. Munyi hakan da ita kamar kwana biyu na dawo ina hanya maria take fada min cewa an bar asibitin da yaya an mayar dashi gida. Jin abin nayi wani iri sai kuma na barwa zuciyana komai nake tambayan yanzu yana ina ke nan tace yana gidanshi wajen matansa. Saidai ance a tsohon part dinsu da suka tashi aka ajeshi ba a kaishi ainihin part dinsa ba don kada a dameshi a nan din . Ajiyan zuciya na sauke ina fadin to yanzu yaya zanyi Yanda tace dani ya habu yace dole can zan koma nima mu kula dashi tare dasu saidai na dinga yi ina zagayen gidana. Sam banji dadin hakan ba a raina amma na bar zancen kamar yadda tace nayi sai idan sun nemini da maganan hakan na karaso gida a cikin bacin rai. Don kuka dai nayisa a yanzu har na daina saidai tunanen zuci kuma dana koma yi wanda yafi kuka wahala donshi yana cin jiki. Nashigo nayi wanka tare da alwala nafito ina kimtsawa yaya Habu yayi salma a gidan hakan yasa na fito daga dakina don ni kadaice yanzu a gidan Biba ta koma wajen uwarta tun faruwan al,amarin nan a can take yanzu saidai tana zuwa kwana bibiyu da yan uwanta su gyara muna gida suyi min wanki da sauran wasu aiyukan. Na fito muka gaisa na samu wuri na zauna yake fadin bayan ki dazun mun bar asibiti da jafar yana gida yanzu haka. Na dago kai na kalleshi yace ehh saboda mun yanke shawaran a mayar dashi gida acigaba da wanan na gargajiyan tunda duk munsan ciwonsa dai bana asibiti bane. Don haka zaman nasa a asibitin baida amfani banda zaman kashin kudin da akeyi kawai naso a kawo shi nan don zaifi jin dadi a nan din sai kuma nayi tunanen cewa mutane ba zasu gane hakan ba zasu dauka da wata manufa muka kawo shi nan din. So shiya dai na kaishi can aka bude masa part din mu a nan yake yanzu don haka nazo in fada maki dole kema din zaki koma can din a yanzu har muga abinda hali zaiyi. Idan ya kama din mu fita dashi wajene sai mu fita dashi din aje can a gwada sa,a kuma yanzu dai zuwa nayi na fada maki zuwa dare sai ki shirya zan dawo in daukeki nida maria mu kaiki can din . Hawaye na soma sakewa yake fadin kiyi hakkuri hakan jerabawan mune mu daku saidai shi dake kwance ya fimu shiga wani rayuwa. Don haka ki natsu banson kije ki biyewa Nusaiba kuna saida hali har mutane suyi Allah waddai da halin ku ki natsu kisa ido ga jinyar mijinki shine abinda zai kaiki gidan. Ya barni da zulumi ya tafi na rasa abin yi dole maria din na kira ta ban shawara na dauki dan abinda zanyi amfani dashi a can din tunda ba zaman dindindin zan tafi yi ba gidan. Hakan ya faru sunzo bayan sallah isha,i suka daukeni bayan yaya yayi gargadi ga maigadin mu na nan gidan sosai akan ya kula da gida kada ya bari kowa yazo gidan ya shiga idan bani bace na turoshi. Mun isa mun samu motoci biyu a gidan hakan na nufin akwai baki a ciki lokacin haka muka karasa ciki da sallama abokanshine suka zo daga abuja dubansa suka samu an sallamishi suka zo gidan. Suna zaune a falo dasu mama sai yaya ibrahim da zai zauna a na shima tare damu din suna bayani saiga ya habu don shine a gaba aka gaisa ya kara masu bayani halin da ake ciki nan suke fadin har idan za a fita dashi waje din ne don Allah su sani. Da zasu tafi suka kawo kudi mai yawa suka bayar Asmau suka mikawa akai masu godiya suka tafi. Sai bayan fitansune maman tudun wada ta juyo tana fadin kin iso yar nan sai kikaji shawara ya canza mun bar asibitin ? Ai nace habu ya kiraki ya sanar maki tun dazun din yace kina makaranta a lokacin idan kin dawo dai zai sameki. Ya habune ya shigo da kayana dan troler ne dana saka kayana a ciki sai sallaya da al,qura,n dina dana dauko yana shigowa ya nufi ainihin dakin da suka zauna da maria don gadon dakin da komai yana nan a dakin yadda suka barshi. Ya fito yake fadin dakin nan zaki zauna ke Rahama mama dubune tace a nan zata zauna ke nan kuma ? To me zata tsaya yi can mama tunda yana nan sai mama tudun wada ta karbe da fadin inba ita ba waya san yadda zaibi dashi haka yadda takeyi ai itace dai karfin jinyar nasa ko . Asmau ta miko kudin tana fadin habu ga kudin nan dasu Mansur suka bada ki bawa mama koda wani abinda za ayi nan koda yske mu gani nawane ya mika hannu ya karba daga hannunta. Dubu dari biyune yace ya juyo yana fadin ga dari da ashirin ku raba ku ukku sai wanan su mama kuma su raba ya mika mata sauran. Ina waje daya nida yar uwata a takure yake fadin tundazun barcin yakeyi ke nan mama tace ya bude idanunsa dazun kafin magariba nan dai ya zauna suna hira dasu mama din da iya data shigo . Saiba ce ta fara mikewa bayan ta sauke ajiyan zuciya tana fadin aina zata ko mu nan zamu iya jinyarsa ba sai wata tazo ba don me za a kawo Ramaah ace itace zatayi jinyarsa. Keko kikan fara abinki ke nan mama dubu ta fada tace a,a mama abinda ake muna a gidan nan yayi yawa ke nan dai mu bamu da amfani garshi yanzu sai Rahama ko ? Yanzu meye abin fada cikin zancen nan wanda ke fama da kansa a yanzu har kun ga wajen wani fitina a nan kuma ? Ba fitina bane mama akan so a raina muna wayaune wani lokaci aiba a gidan nan take dashi ba saita zauna gidanta tunda ba nan take ba. Don me za a mayar damu yan kallo ace wai itace tasan kan jinyar sa to ai sai mu barta dashi tundaan kawotane ita data iya ta kuka dashi. Umm,uhmm duk abinda zakuce saidai kuce amma ba inda yarinyar nan zata a yanzu tunda itama mijintane don haka wace bata hakkuri ga hanya nan mama ta fada.